Uncategorized

TAKUN SAKA 36

 

*_Chapter Thirty Six_*………..(Kura ga tsoro ga ban tsoro) ya faɗa a ransa ganin yanda jikinta keta uban tsuma tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Kansa ya sake ɗaukewa tamkar baiga halin da take a cikin ba ya ƙaraso gareta bayan ya ajiye kayan. Kuka ta fashe masa da shi tana girgiza kai, dan a duniya bata taɓa shiga cikin tsananin kunya da firgici kamar na yau ba. Tayi matuƙar daburcewa, wajen ɓuya kawai take nema amma babu. 

         Hannusa mai lafiya yasa ya zame hannayenta duka da take faman rufe jiki, duk ƙoƙarinta na son ganin ta faɗa jikinsa ta ɓuya kuma yaƙi bata daman hakan, sai ma sake mannata da yay da bango ya tokare ta da hannunsa mai ciwo duk da zogin da yake masa har zuwa yanzun. Cikin tsareta da idanu babu ko kunya ya fara magana cikin izza da ƙasaitar fushin da yake ciki har zuwa yanzun, “Nuna tsoro anan gazawace ga wadda ta nunama duniya ta girma, tunda har kika iya ɗaukar wancan da kika ƙulla, wannan ma dole ki ɗauka. Lokaci yayi daya kamata nima naga little Master a duniya, kafin ki ɗanamin tarkon da bazan tsallake ba Hibbaty”.

       Duk da ba komai ta fahimta a maganganunsa ba saboda ruɗanin da take a ciki, kanta ta shiga girgiza masa. Cikin rawar harshe da son ɓoye kanta tace, “Dan……”

        “Shiiii!!.” Ya faɗa yana ɗaura yatsansa bisa leɓenta.

       “Karma ki roƙeni dan zugani kike. Barinki a haka gareni haɗarine, saboda wannan kan naki ba kowane yare yake ganewa a cikin baƙi. Kinfi buƙatar dalla-dalla. Gara na tabbatar da kaina a gareki, kafin lokaci ya ƙuremin na ajiye jini na a jikin ki, maybe ki fara nazari kafin kiyi abu” . 

    Baki ta buɗe zata sake yin magana ya rufe bakin da yatsunsa yanda har sai da azaba ta sakata cire hannuwanta da take kare jikinta da shi ta riƙe nasa hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta.

       A karon farko ya saki wani lalataccen murmushi mai bayyana ƙunar zuciya, “K tsoro ce mai ban tsoro Muhibbat. Da yaren tsoro kawai ake fahimtar da ke karatun duniya. Tunda haka kikafi buƙata kuwa, sai ki shirya zaman jira da rainon ƴata ko ɗana har na fito a gidan yari tunda a can kikafi buƙatar ganina”.  

       Yana gama faɗa ya ɗan lakaci hancinta da janye jikinsa a nata, tana son yin magana yay mata alamar gargaɗi, idanunsa tamkar zasuyo aman bala’in da ke a zuciyarsa. Bai sake ce mata uffan ba ya juya mata baya ya sakarma kansa ruwa tare da cire towel ɗin jikinsa kansa tsaye tamkar yama manta da ita a wajen. Da sauri ta zame tai ƙasa jikinta na matuƙar rawa ta ɓoye fuskarta. Jin kamar ya kashe ruwan ya sata sake rumtse ido da ƙarfi kamar zatai kuka. Dan ita duk tunaninta tsayawa yay kallonta, duk da tanajin motsin da yakeyi alamar yin wani abu. Kaɗan ta buɗe idanunta sai taga har yanzu yana a yanda ya juya mata bayan. Ta ja ɓoyayyar ajiyar zuciya da fara ɗauraye jikinta da sauri-sauri. Duk da yanajin yanda take facal-facal da ruwa har yana fallatso masa a jiki bai juyoba, sai da ya kammala abinda yake a wajen sannan.

      Juyowar tasa tayi dai-dai da fisgar towel ɗin daya ajiye ta ɗaura. Duk da bai gama rufe mata jikin ba dai taji ƴar nutsuwa fiye da ɗazun da take a sule. Ya ɗan bita da kallo ganin yanda ta nufi hanyar fita da sauri har tanayi kamar zata faɗi, ga santsin ruwa da tiles ga na rashin ƙarfin jiki. 

       Ya ɗan girgiza kansa da sakar ma kansa ruwan shower tausayinta na ratsashi. Tabbas yasan abinda ya faru a yau ɗin rubutaccene da ga alƙalamin ƙaddarar Sa. Ko babu ita sai hakan ta faru, tana da laifi yanada laifi. yasanma yafi yawa fiye da natan, sai dai yanda ya santa inhar ya nuna mata sassauci sake birkice masa zatayi, a yanzu kuma rayuwarta tafi ta kowa haɗari dan ita kowa kema kallon lagonsa. Haka dai ya kammala wankan cikin dabara da tunane-tunane. Bathrobe ya saka maimakon towel ɗin da ya shigo da shi tunda ta ɗauke. dan ya fahimci gaba ɗaya tsurewa take idan ta gansa babu rigan. Koda ya fito kwance ya sameta a kan gado ta kudindine da bargo. Komai baice mataba ya ƙarasa ga mirror yana ɗan duban kansa zuwa real face nasa na Isma’il da ya fito da shi. Jakar kaya daya gani ajiye a gefe ya sashi fahimtar su Habib sun dawo kenan. Koda ya buɗe kayansa ne a ciki da dukkan abin buƙatarsa na yau da kullum irinsu mai, turare da makamantansu. Ya ciri abinda zai buƙata ya ajiye gefe da wanda itama zata buƙata ɗin. Harya gama kintsawa Hibbah na cikuykuye abinta a bargo duk da tana jin motsinsa. Amma tsananin kunya da zazzaɓi sun hanata ƙwaƙwaran motsi. 

        Shima duk da yasan idonta biyu komai baice mata ba, sai ma salla da ya tayar ta azhar. Sai da ya idar ya miƙe ya saka sabon mask sannan ya karasa saitin inda take a gadon. Hanunsa dafe da kansa dake sara masa ya kai zaune. Batare da yace komaiba ya yaye bargon da ɗaura hanunsa saman goshinta. Sosai jikin ya ƙara zafi, dan haka ya ɗan tsura mata jajayen idanunsa da ke sake tabbatarma mai kallonsa baida lafiya. “Ki tashi kiyi salla, sai ki sha magani ki kwanta”. Yay maganar har yanzu muryarsa bata fita da ƙyau.

         Sarai Hibbah tajisa. sai dai ta kasa koda motsawa harya tashi. Sai da taji ya fita a ɗakin gaba ɗaya sannan taja numfashi tare da miƙewa zaune tana share hawayen da ke ziraro mata wanda ba komai ya kawosu ba sai tsananin kunya da nadamar abinda ya faru. Ga kewa da ƙulafucin son ganin ƴan uwanta da Umminta da ke cike da zuciyarta.

    ★★

   

      Sosai su Habib sukaji daɗin ganin yay wanka ya sauya kaya. Sai dai tsananin tausayinsa na nan shimfiɗe akan fuskokinsu. Dan a kallo ɗaya da zaka masa zaka iya fahimtar rashin jin daɗin jiki dana zuciya dake tattare da shi. Kawai dai ƙarfin hali ne da juriya irin tasa.

       Sannu da tambayar yaya jikinsa suka shiga jera masa. Batare da ya iya buɗe bakin yayi magana ba ya shiga ɗaga musu kai kawai alamar amsawa. Basu damu ba, dan su kansu idan yana cikin irin wannan yanayin sunajin tsananin shakkarsa. Yanayine da yake a cikin fushi da zafin zuciya. Ƙiris yake jira wani ya shiga gonarsa ya tabbatar da fushin a kansa.

         “Ga magani ko a kawo tea sai ka sha?”.

    Musbahu ya faɗa cikin girmamawa. Master da ke kallonsu na tabbatar da suna a cikin ƙoshin lafiya ya jinjina kansa kawai yana rufe idanu. Sai kuma ya motsa laɓɓansa a hankali ya ce. “Kunyi salla?”.

       “Eh”

  Suka faɗa kusan a tare.

Komai bai sake cewa ba da ga hakan sai da Adam ya gabatar masa da magungunan da suka shigo da shi. Khalid kuma yay saurin nufar kitchen ya ɗakko ruwa tare da tea da ya haɗo masa. Batare da yayi magana ba ya ɗauka tea ɗin yasha kusan rabin cup. Shima maganin yasha. 

        Fahimtar ya kammala ya saka Habib fara masa bayani a nutse game da aikin daya turasu. “Alhmdllh Master anyi bani gishiri in baka manda. A yanzu haka dukkanin iyalansu suna a hannumu”.

       Kansa ya jinjina fuskarsa har tana nuna alamun jin daɗin yanda sukai aikin cikin sauƙi da sauri babu wani mishkila. Musbahu ya dire jakkar da suka shigo da ita shima yana faɗin. “Wannan wayoyinsu ne duka anan. Duk da mun yanke network ɗin gidan gaba ɗaya saboda tsaro dai sai muka taho da su. Kayi haƙuri munyi abinda baka saka mu ba. A cikin yaran akwai wani mai taurin kai ya nema mana gardama muka bibbigesa, dan mun nunama mamansa ta tsawatar masa amma taƙi”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button