NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 11-12

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

????11-12

      Kallon zainab yayi cikin kulawa”kiyi hakuri mana Darling har wani lokaci”,kamar zata yi kuka ta zame ƙasa daga saman kujera,yanzu ka mun adalci kenan?,wattani nawa rabona da iyaye na?,idan kai aka yiwa haka ya zaka ji?.


Wattani kika ce,akwai wacce zata share shekara bata ga iyayenta ba kuma suna a gari ɗaya bare ke da akwai taraza sosai a tsakani.

Cikin ɗaga murya ta fara magana, daɗin auren bai kai mun nan ba da zan man ta da iyaye na har tsawon wani lokaci ban waiwaye su ba,kamar yadda na faɗa maka idan kaga ban tafi tare da kuba zamu haɗu a can!

Ɗaki ta wuce abunta Mani nata kwasar dariya…,uhm mami taurin kai yayiwa mammyb ki yawa na rasa yadda zan shawo kanta. Kada ka damu daddy zan maka maganin ta yadda ko kara ka aje ba zata sake tsallake wa ba!.

A’a ban saki ba domin Ni al’amuran kima sun fara bani tsoro,wai meke damun kine?,dariya tayi kuma”kada ka tashi hankalin ka babu abinda zai faru da kai,sanin abinda ke damuna idan lokaci yayi zaka ji kuma ka gani sai da safe daddy!”.

Ɗakin ta kawai ta nufa yana wurin zaune cikin mamakin ta ..,daga bisani ya kashe kayan wutan tare da rufe ko ina ya wuce ɗaki.

Tana kwance hankalinta ba kan waya
kamar bata da wata matsala a rayuwa,zee tashi ki haɗa mun ruwan wanka, ɗan guntun tsaki taja,nifa bana son damuwa kawai baka da halin ganin mutum yana hutawa sai ka dame shi!.

Nike damun ki zee?,bayan kai akwai wani ne cikin ɗakin nan?,uhm Allah baki hakuri in shaa Allah zai haɗa ki da daidai ke  ya wuce Ban ɗaki….,gyara kwanciya tayi tare da cigaba da surutai ƙasa kasa.

Yana tsakiyar wanka ta kwala ihuuu!,babu shiri ya dauro towel sauran jikin shi da komfa…,saman gadon ya haye tare da riƙo ta”meke damun ki?”,zan mutu mara na ciwo kamar zai fashe!”,hanunta duka biyu riƙe kam a marar ta.

Innalillah wanan masifa dame yayi kama,da an fita wanan a shiga wanan?,ya Allah idan wani laifi na aika ka yafe ni!,yadda take ihu haɗe da nishi sama sama yasa ya ƙara fita hayyacin shi domin yana matuƙar son matar shi abubuwa ne suka zo masu wani iri.

Bai tsaya sauya mata kaya ba kawai ya ɗaura babban hijab saman kayan bacci dake jikinta,ya saka jallabiya tare da ɗaukar wallet da key mota tana rungume a jikin shi ya nufi hanyar fita….,kiciɓis suka yi da mami a palo”ina kaza kai ta daddy?”,ɗauko hijab ɗin ki asibiti zamu bata da lafia,ba zan barki ke ɗaya a gidan ba dare ne.

Ban zuwa ko iya,itama ai babu abunda ya same ta , ka rasa yadda zaka yi da ita ne sai nayi maka maganin taa!,kawai ka kuma ciki zuwa da safe zata warke sumul.

dakata!”ya daka mata tsawa”,na rantse da Allah idan wani abu ya faru da ita,zan manta da soyayyar da nake maki sai na dauka mummunar mataki a kanki tunda na lura ke hatsabibiyar yarinya ce!.

Ni ɗin daddy?
tsaki jaya tare da nufan hanyar fita domin cikin halin da zainab ke ciki baya tunanin ko hajiyar shi tazo zai iya ƙyale zee haka nan.
Sai daya saka zee a mota sanan ya rufe mami ta waje sanan yayiwa motar gear…,ydda ya rinƙa horn yasa mai gadi buɗe masa gate da wuri.

Ɗan leƙowa yayi,ka kula da mami ita ɗaya ce kada ka bari ta fita zamu asibiti da zainab ba lafiya.  In shaa ALLAH za a kula ALLAH bata lafiya.

Wani asibitin kuɗi dake kusa dasu ya nufa…,amsanta akayi kafin aka buɗe mata file a wurin.

Ma aikaciyar jinyar ta tambaye shi abunda ke damun taa?,faɗa mata yayi ta nufi ɗakin da aka aje taa,babban 
likita ya bada dama ayi mata alurar ciwon mara da ƙarin ruwa,idan ta farfaɗo a duba ta da kyau.

Sai sintiri yake domin ya rasa natsuwar shi gashi bai fito da waya ba saboda sauri,ɗakin ya nufa tare da zama gefen gado yana ƙare mata kallo..,da alama bacci take yi a wahalce ƙarin ruwan na shigarta.

Cikin baccin take mafarki wai tana riƙe da jariri a hannu tsamo tsamo cikin jini,zaki na biye da ita cikin dokar jeji sai gudu take yi kamar ranta zai fita…,idan ta waiga saitaga yayi daf ta ita,ta ƙara kai mi har suka isa bakin tafkeken rami mai girma da faɗi babu wata hanya sai nan,idan ta kowa maya kuma zakin nan zai haɗiyeta!,gashi nan tsaye ƙikam ya buɗe baki sai miyau ke dalala!.

Ƙara riƙe jaririn tayi sosai tana neman mafita…,wani dubara ya faɗo mata tayi kamar zata afka ramin,ya nufo wurin..,sai ta koma gefe saura ƙiris ya faɗa ya juyo a hasale tare da yin kanta cikin zafin zama ya janyo ƙafar jaririn dake hanunta!

AI kuwa ta riƙe sosai tare da zube wa ƙasa,tana ja yana tana kwance ƙasa ta kasa tashi duk jikinta ya ƙuƙuje!,amma bata saki ba hat ya samu nasarar fizge ƙafar jarinrin ya taune!

Ihuuu ta sake ganin abunda ya faru nan take ta sake rungume sauran jikin  jaririn ai kuwa ALLAH ya bata sa a ta rarumi wani dutse dake gefe da hannu ɗaya ta kwaɗa mai a baki…,ya saki wani irin gurnani saboda azaba,bakin ya tsage yana zubar jini!.

Ƙara zaburowa yayi zai far mata nan take ta farka tare da sakin ihu tana ƙoƙarin tuge ƙarin ruga dake hanunta sai faɗa take;jaririna a kawo mun ɗauki !

A zabure muhammad  ya danne ta tana ƙoƙarin ƙwace wa sai kuka take yi yana ƙoƙarin rarashin taa…,jin ihunta yasa maaikaciyar jinyar dake aikin dare ta shigo da zumar masu gargaɗi suna damun sauran marasa lafiya. 

Meke faruwa ne?,farka wa tayi tana ihu bansan abunda ya same ta baa.

sake ta kawai inaga zafin ciwo ne,gefe ya koma tsaye yana kallon yadda take zazzare idanu hannu riƙe da mara!,dafa kafaɗarta maaikaciyar tayi tana mata sannu…,nan ta lura ƙarin ruwan ya kwacce har wurin yayi kumburi.

Canza mata hanun zata yi sai taji ɗigan abu a ƙasa,koda ta duba jini near!,baiwar Allah dama kina da ciki ne ko al’ada kike yi ne?.

Cikin matukar tashin hankali ta dubi jikinta,shima ya nufo wurin hankali a tashe..!,girgiza kai ta shiga yi cike da tsoro”ban sani ba amma lokacin al’ada na ya wuce da sati biyu ma”,Allah sarki inaga ɓarin ciki kika yi amma ban tabbatar ba sai likita ya duba ki!

CIKI !?”suka haɗa baki”,ku kwantar da hankalin ku barin kira likita…,ta fice a ɗakin.

Kuka zainab ta cigaba da rerawa cikin zuciyarta tana addua ALLAH yasa ba mafarkin da tayi bane ya tabbata a kanta!,muhammad  addua yake Allah yasa cikin ne kuma bai samu matsala baa.

Tare da likita suka dawo tana riƙe da file ɗin zainab…,turo ƙofar da suka yi ya maido da hankalinsu wurin,kallon muhammad  yayi ka ɗan bamu wuri zan duba taa.

Bai furta komi ba ya fita a ɗakin yanata addua  a zuciyar shi.., sannu ko madam ?,likita yace da ita amma bata amsa baa.

Ki kwantar da hankalin ki zamu yi iya ƙoƙari wurin baki cikakken kulawa a nan. Shiru dai tana kallon shi..,bayan ya ɗan dudubata yace da nurse ɗin ta gyara mata jiki ta taimaka mata zuwa ɗakin ganawa da marasa lafiya na musamman zai ƙara duba taa.

Taimaka mata tayi zuwa ban ɗaki tayi tsarki tare da saka pad  sanan ta bata riga dogowa wanda marasa lafiya ke sawa ,ta riƙo hanunta suka fito…,ganin su muhammad  ya miƙe tsaye yana tambaya”lafiya dai?”,zaa dubata ne ,nurse din ta bashi amsa suka wuce..,abunka da asibitin kuɗi akwai ƙarancin mutane har suka isa basu haɗu da kowa baa.

Kwantar da ita akayi saman wani gado ya tambaye ta ko tana jin fitsari?,ta girgiza kai!,ruwan gora ya umurci nurse ta bata,ta shanye duba.  Haka ta shanye ya cigaba da rubuce rubucen shi har zuwa wani lokaci ya sake tambayar taa,ta amsa tana ji.

Umurni ya bata data kwanta zaa yi mata hoton mara(pelvic ultra sound scan), domin gano yanayin da take ciki,ba musu ta kwanta ya fara aikin ckin gwane wa …,ya ɗauki lokaci yana yi daga bisani yace ta tashi ta koma ɗakin da take kwance,da safe idan ta sake samun ƙwarin jiki zai magana da su duka amma a kira mashi mijin.

Muhammad  naji saƙon likita ya shiga da sauri…,wuri ya nuna mashi ya zauna tare da bashi wani takarda,wanan bill nku kenan idan ka biya zaa baka sauran magunguna.

Zan iya biya da credit card ɗina?,sosai ma inaga ba zan shigo da wuri ba gobe da safe saboda akwai marasa lafiya a zan duba a babban asibitin gwagwalada,amma zan yiwa nurse magana ta kula da ita idan na shigo bayan na ƙara dubata zan maku bayanin matsalara taa,yanzu dai bata cikin wani damuwa.

Godiya yayi sanan ya fice zuwa inda zai biya kuɗin likita ya haɗa kayan shi zai wuce..,sai daya biya aka bashi receipt da sauran magunguna ya kawo wa nurse ɗin.

Tana dai kwance shiru ya tsaya gefe yana kallonta cikin tausayawa har nurse din ta mai magana ya basu wuri..,fita yayi sai data gama komi ya dawo tare da zama gefen gadon hanun shi riƙe da nata,yana  kuma yana shafa kanta cikn tsigar rarashi..,kiyi hakuri zee duk abubuwan dake faruwa laifi na near,bana yadda da maganar ka,bana haƙuri dake abubwa suna faruwa dake a dalili na,kuma ba kowa bane sila sai mami!,amma nayi alƙawari zan yi maganin taa.
Rufe mashi baki tayi da hannu,ya isa nayi imani duk abunda ya aru dani daga Allah ne amma dai ya zama dole mu bincika lamarin mami.

Shike nan Allah baki lafiya.

Cikin ikon Allah ciwon marar ya tsagaita mata har ta samu bacci yana zaune,zuwa wani lokaci ya jingina shima sai bacci…,zuwa da asuba aka cire mta ƙarin ruwa nurse tace ya samo mata abunda zata ci mai zafi.

Masallaci ya nufa yayi sallah daga nan ya wuce gidan iyayen shi…,Gidan shiru baa tashi bacci ba ya nufi sashin hajiyar shi,nan ma sai day buga inna mardiyya ta buɗe suka gaisa,ya tambaya ko sun ɗaura abun karyawa?tace ta ɗaura ruwa dai.

Don ALLAH a hanzart idan yayi zafi a samun a babban flask,a soya ko dankali da kwai ne zainab na asibiti barin shiga wurin hajia yanzu zan fito.

Assha ashe jikin ya matsa haka?,Allah bata lafiya yanzu zaa haɗa kuwa..,ɗakin hajia ya shiga da sallama suka gaisa ,lafiya dai da safen nancy?,ya faɗa mata abunda ya faru,”ina mami?”,shine tambayar data fara jeho mashi!,mamai na gida na barta saboda cikin dare muka nufi asibitin..,yanzu kai moha don baka da lissafi zaka bar yarinya yar shekaru goma ita ɗaya a gida saboda ɗan ciwon mara na al’ada da ya kama matar ka,babu kunya ka kwashe zuwa asibiti?,banga laifin ka ba ta riga ta gama da kai moha,mace bata da amfanin komi amma ka liƙe mata haka?,Allah ba zan ƙyale ku ba idan wani abu ya faru da mami!.

Hajia kiyi hakuri ciwon ne yaci ƙarfinta kuma dai bata taɓa yin irin shi baa,kinga ma nurse ɗin tace tana tsammanin shigar ciki ne ya fara samun matsala amaa ynzu da sauƙi.

Shigar cikin gidan kurt!,ka taba jitter/ganin inda aka ɗaure wa mace bakin mahaifa sanan ta samu ciki?,inace ta inda ƙwan haihuwar zai shiga aka rufe?,shashasha kawai wanda bai san inda ke mai ciwo baa,ka tsaya lelen ta har ka rasa wacce Allah ya baka tunda ita ba so take ba ko an rasa bata da hasara boko ya fice mata haihuwar.


Ganin faɗan ba zai ƙare ba ya mata sallama zai koma asibitin..,kai zaman asibiti ya kama babu wani nawa da zai biyo kurt,sanan ka tabbatar ka ɗauko mun yarinya a zauna a nan har ku gama shirmen zaman asibitin idan kun shirya kua da ita sai ta koma.

Wuce wa dai yayi zuwa kitchen ruwan ya tausa an zuba a flask da kofuna an soya ƙwai dankali ya rage baa kwace ba…,zama yyi ya jira lokacin har gari ya fara haske hankalin shi na asibiti wurin zainab,ya yiwa inna mardiyya godiya ya tafi.

A hanya ya saya madara,sugar,milo da  bread ya isa tana zaune saman gado shiro ba kowa a ɗakin….,ya jiki naki?,da sauki ta amsa ina mami?,
ba gida na tfi ba wurinsu hajia tana maki ya jiki. Ina amsawa tace duk da tasan ya dai faɗa ne kawai.
Ya shiga haɗa mata shayin da komi yadda take so ya dawo bakin gadon,a hankali take sha har ta ƙoshi shima ya ɗan ci domin hankalin shi ya koma gida wurin mami gashi bai fito da waya baa.

Akwai abunda kike so ne?”ya tambaya cikin kulawa”,eh ka tafi gida ku zo da mami,sanan ka ɗauko mun kayan da zan sauya da wayata.

Shike nan sai na dawo!,tana kallo ya fice.

Koda ya isa gida mai gadi ya buɗe mai suka gaisa sanan ya wuce ciki..,yadda ya rufe ƙofar haka ya same shi alamar baa taɓa baa.  Buɗe wa yayi ya shiga shiru bbu kowa a palo ya higa ƙwalawa mami kira shiru…,har ɗakinta ya shiga wayam kuma babu kowa a toilet har ƙasan gado da closet ya duba ba kowa!,kuma ba alama an fita ta window.

Ya nufi ɗakin baccin su…,yadda suka bashi haka yake!,ko ina ya duba a gidan har can baya harabar babu kowa nan hankalin shi ya fara tashi!,ciki ya koma ya ɗauki riga doguwackier,zani da hijab na zainab sai wayoyin su ya nufi wurin mai gadi…,wayar shi na kunne yana kiran hajiyar su.

Ya iso wurin kenan ta ɗaga”am nace ko kin aiko driver ya ɗauki mami ne?”,saboda me zan aiko driver?,bayan mun gama magana nace ka kawo mun ita da kanka ko amsa ni kayi?.

innalillah ya furta!,me ya faru near?,ba komi dama na dawo gida ne ban ganta baa!

Baka me baa?,wallahi ƙarya ne duk inda jikata take a cikin garin abuja sai kun fito mun da ita!,ta kashe waya.

Tashin hankali wanda baa sa mashi rana,bai san lokacin daya jingina da jikin ɗakin maigadi ba!,ranka ya daɗe meke faruwa?,kai zan tambaya tunda kai ka kwana a gidan!.

Wallahi ran ka ya daɗe jiya ban yi bacci ba a gidan domin wasu abubuwa na ban al’ajabi ya faru,wasu koke koke kamar na dabbobi ko jinnu dai gashi nan har asuba ,nayi nayi in shiga ciki in dubi halin da yarinyar nan ke ciki wuri a rufe wayar ka dana uwargida bai shiga!.

Shike nan nawa ya ƙare domin bata cikin gidan babu inda ban duba ba wallahi ba kowa!,A’a ran ka ya daɗe a sake duba wa dairy…,ya nufi cikjn gidan yana ƙara duddubawa.

Ya ɗauki lokaci sanan ya dawo cike da tashin hankali domin bai ga kowa baa!,muhammad  yace zama bai ganshi ba bari ya duba maƙwabta duk da estate ne babu wanda ke damuwa da wani,haka ya rimƙa yawo cikin anguwan har cikin gari gidajen yan uwa ace bata zo baa.

Koda ya isa likita ya shigo tafiya na gaugawa ya kamashi zai shiga garin minna saboda su ya shigo,kuma har ya zauna da zainab a office ɗin shi muhammad  ya dawo.

Ya shiga ɗakin babu kowa ya tambayi nurse ta nuna mai office ɗin da ake jiran shi…,da sallama ya shiga suka gaisa ya nuna mashi wurin zama.

Bayan ya kalle su na wani lokaci ya fara magana;kun taba amfani da wata hanya na tsarin iyali ne?,daga sama tambayar yazo masu.

Eh likita a farkon auren mu nayi tubal ligation wanda zaɓin mijina near,a cewar shi sai mun mori rayuwar auren mu zamu fara tara iyali,na goyi bayan shi duk da an faɗa mana illar dake ciki saboda ina da burin komawa makaranta.

Jijina maganar yayi,amma haihuwar ki nawa?,ɗaya!.

Kuma baki samu wata matsala ba tun daga rainon ciki har haihuwa?,gaskiya na wahala matuƙa wanda da kyar na haihu da kai na.

Maganar gaskiya kun tafka babban kuskure domin shi tsarin iyali irin wanda kuka yi bako wace irin mace ake yiwa baa,hasali ma sai wacce tatara iyali sosai kuma ta tabbatar bata buƙatar wani haihuwa har karshen rayuwarta, ko wacce rainon ciki da haihuwa ke zuwa mata a wahalce har wurin haihuwar ta kanyi yunkurin rasa ranta sai an mata aiki,sune irin matan da ya dace su ɗauki wanan tsarin iyali na ɗaure bakin mahaifa(tubal ligation).

Domin idan aka yiwa mace irin ki wanan tsari gaskiya da wuya ta isa ɗaukar wani cikin,saboda an ɗaure bakin mahaifa babu ta yadda maniyyi zai shga ciki,illa ya taruwa ne a saman mahaifa zuwa wani lokaci yabi jikin ɗan adam ko ya fita a lokacin jinin al’ada.

Illolin shi nada matuƙar yawa da hatsari,ciki akwa;
yana ɓata inda fitsari  ke taruwa a jikin mace(bladder),da magudanan jini(blood vessels).

Ciwon mara mai tsanani har ƙarshen rayuwar mace

Idan kuma ALLAH ya nufa kin samu ciki zai rayu ne a wajen mahaifa(ectopic pregnancy ),wanda zai zo da matuƙar wahala tare da barazanar tafiya da rayuwar kibbutz,idan ya kai ma lokacin haihuwa sai anyi aiki ko a rasa ki ko abunda ke cikin ki.

wanan ne yasa cikin ki na farko kija wahala sosai Allah ya taimaka kin rayu da abunda ke cikn ki.

Yanzu dai a takaice kina ɗauke da cikina sati shida a wajen mahaifa(ectopic pregnancy ),ciwon mara da kika yi fama dashi yana daga illar tsarin iyali da kika yi shine har yake barazanar lalata cikin!,Allah ya taimaka duk da ya fara zuba mun dakatar dashi ta hanyar wani allura wanda kuka saya dubu talatin da biyar.

Yanzu cikn na lafiya zamu bata hutu na wata biyar(bedrest)idan anan kuke so ko a gida,abunda ake bukata dai ko spoon kada ta ɗauka da hanunta har cikin ya shiga wata shida kenan.

Saboda tsabar farin ciki kuka ta shiga yi na farin ciki,shi kuwa baki ya kasa rufuwa.

Yace da likita a basu sallama zai koma gida da ita zaa kula da ita sosai.

Shawawari ya ƙara basu da magungunada zata yi amfani dashi sai sallama.

Sun fito ne take tambayar shi ina mamin?,ya tsinci bakin shi da cewa tana wurin hajia can zamu yanzu haka!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button