NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 15-16

MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

????15-16

       Ruɗani ta shiga,wani sashi na zuciyar ta na gargaɗinta da bin umurnin shugabanta,yayin da wani sashin ke ƙarfafa mata gwiwa ta koma wurin iyayen ta har sai taga halin da suke ciki sanan ta wuce!,sai dai muddin ta bijire wa umurnin shugabanta rayuwarta zai shiga cikin hatsari wanda zai sanadin rashin cikar burinta.


Idan tayi nisa da iyayenta a wanan lokaci da suka fi buƙatar ta komi zai iya faruwa ciki har da rasa cikin dake jikin mummynta ko rayuwarta.

  Muhammad  da ɗan uwanshi suka garzayo gida bayan sun fi abunda ya kamata a cikin gari,koda suka iso gidan basu wuce ciki ba sashin Abban su nan suka nufa…,da sallama suka shiga cikin babban palon.

Dattijo ne  fari sol mai matsakaicin jiki,cike da natsuwa da kamala,yana sanye cikin yadi fari da wando ,hanun shi riƙe da babban littafi na addini da alama nazari yake yi

Wuri suka samu a ƙasa  gefe  suna jira ya kamalla.,sai daya kai aya sanan ya miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya suka gaisa,”ya iyalen ku?”,da sauƙi dai ABBA domin wani al’amari ne ya tunkaro mu a yau ɗin nan..

Ba dai rashin lafiyar zainab ɗin bane”ya tambaya?”,cikin jimami shafi’u(babban yayan su muhammad) ya furta,yanzu maganar da ake bamu san inda zainab ɗin take baa,domin dai muhammad  ya barta a nan gidan ya fita hajia ta kira shi a waya wai bata gidan!,gashi ita mamin tun da safe baa ganta ba ,inda ya kamata mun duba bata har wurin yan sanda mun kai rahoto.

Girgiza kai yayi cikin ƙosawa da hali irin na lanti!,kun tabbata ita zainab ɗin basu tare da mami?,A’a ABBA ni da kaina na kawo zainab gidan nan ita ɗaya.

Yanzu me ya kamata ayi?,sanin kan ku ne mahaifiyar ku zaman kanta take yi babu sauran igiyar aure a tsakanin mu,bani da wani iko a kanta yanzu!,tafi jin shawarar mu akan nawa.
Amma ABBA mun riga mun kira sauran yan uwan mu zamu yi zama na gaggawa tare da ita a gaban ka,lokaci yayi da fitar tsabgar muhammad da iyalan shi,iya gwargwado yarinyar nan tana mata biyayya,ranar data gaji fa ba zaa ji daɗinta baa!.

Haka ne shafi’u ALLAH maku albarka,sai ku sanar da ita ai.

Shafi’un ya wuce sashin hajiyar su….,har ɗaki ya same ta,tana ganin shi ta shiga faɗa zainab tayi mata rashin kunya!

Sai da ta kai ƙarshe yace,idan ba damuwa hajia mu haɗu sashin ABBA akwai shawara da zamu yi akan lamarin.

Jimmm ta ɗan yi,shi baban naku ya shirya ko kai?,hajia don Allah ki rinƙa ba ABBA darajar da ALLAH ya bashi ,ko ba komi akwai zuri’a a tsakanin ku an zama ɗaya bai kamata yadda kike ƙoƙarin tuzarta shi cikin jama’a wasu lokutan!

Dataka can wawan banza kawai,duka bunda yake mun bakwa gani ko?,kada ku wuce gona da iri,wallahi wallahi idan ku ka kai ni maƙura sai na bankaɗo wani ƙuli nashi wanda baku sani baa!,idan yaso kowa ma yabar ganin mutuncin shi domin shi da wanan makirar hajia mariya sune musababbin shiga na tashin hankali wanda har yau na kasa fidda kai na,ban san ranar da zai fita baa!.

Ya isa hajia,koma menene Allah yasan gaskiya koma yana bayan mai gaskiya!,kiyi hakuri mu tafi akan ɓatar mami ne dole mu zauna tare a nemi mafita ɗaya.
Mayafi ta ɗauko suka kama hanya zuwa sashin…,koda suka isa sauran yan uwan shi sun iso.

Tunda ta shigo sashin idanun shi fes a kanta domin suna gida ɗaya,sai ya shafe wata mai ganta baa. Duk da haka kullum cikin begenta yake saboda  tana da asalin ɓoyayyen kyau da ba kowa ke gane wa ba kasancewarta baƙa,shekarunta sun ɓoye domin mace ce mai tsafta da kula da kanta,wanan dalili yasa yake matuƙar sonta duk da auren haɗi ne.

Gaisuwar da take amsawa na ɗiyanta ya maido da hankalin shi wurin su,saman kujera mai zaman mutum ɗaya ta zauna ko kallo bai isheta baa.

Shafi’u ya gabatar da addu’a daga bisani ya ɗora;makasu din taruwar mu a nan shine dalilin ɓace war mami da ita kanta zainab a yanzu,mun yanke shawarar taruwa a nan ne domin neman mafita daga iyayen mu.

Allah albarkace ku da zuri’ar ku,”amin ABBA  suka amsa”,ina baku haƙuri akan abubuwan da suke faruwa,duk da banda masaniya akan wasu abubuwan dukan ku kun fi kusanshi da mahaifiyar ku,banda laifin da na maku ba?,koma dai menene ku gafarce ni,abunda na sani yarinya kamar mami bata isa barin garin nan ba!,tana cikin garin nan amma a ina?,shine muka kasa gane wa….

Kamar yadda zainab ma tana cikin gidan nan wurin makirar matar ka,kuma dole kayi mata magana ta fito da ita ko wallahi sai na datse igiyar auren su kamar yadda hajia mariyata saka ka datse namu!.

Murmushi yayi irin nasu na manya domin yasan halin lanti sosai tana da matukar kishi mai zafi,musamman akan hajia mariya.

Wanan ba hurumi na bane lanti,ai kin saba yanke hukunci kai tsaye,yanzu ma zaki iya samun ta da maganar.

Huci ta shiga yi,yaran su kan shiga cikin duhu a duk lokacin da iyayen nasu ke irin wanan hatsaniya,kan su na ɗaure wa domin suna hganin kamar akwai  wata ɓoyayyen sirri da basu sani baa!.

Tunda haka ne ku tafi zan ɗauki matakin da ya dace akan ɓatan mami kuma zata dawo…,amma kin san dawo warta a wanan lokaci zai zo da abubuwa na ban al’ajabi?,zai iya kawo tarwatsewar zuri’ar mu!.

Hakan yafi komi mun daɗi dama ni aka bari cikin tashin hankali ku hankalin ku kwance!, gwara asiri ya tono kowa ma ya huta.

Shiru yayi yana jimami,yaran duk an barsu a duhu dai!,haka taron ya tashi babu wani gamsasshiyar mafita.

Tashi tayi  ta nufi sashin hajia mariya har ɗakin baccinta…,lokacin tana ban ɗaki.

Daidai hajia lanti na ƙoƙarin fizgo zainab daga saman gadon,hajia mariya ta fito,”kada ki soma wallahi domin zaa yi kare jini,biri jini!”,juyowa tayi suka haɗa ido ko wacce na huci!

Sai me ai ba yau muka fara baa!”cewar hajia lanti”,ci goro cikon benci tabarmar kaɗa caca!,sanin kanki ne baki taɓa cin riba a kai na baa!,sai nawa muka kara kina cin ƙasa?

HAJIA mariya kenan!,a baya kenan da  nake ɗaukar darasi a wurin ki,amma yanzu na wuce sanin ki,nayi nisan da kara kaf ɗin ku babu wanda ya isa ya dakatar dani!,ba wanan cikin kike tattali ba saboda tsabar sharri?,burin ki a haife shi in wulaƙanta a idon duniya?,wallahi sai na zubar dashi sanan in lalata mahaifar yadda ko a mafarki ba zata taɓa ɗaukar ciki baa,sanan in dawo da mami ta tona asirin ku daga baya ayi walƙiya ɓoyayyen sirin ko wanne a cikin ku ya bayyana!.

Daga baya kenan lanti!,kada ki manta nice nasa aka auro ki gidan nan domin cikar burin mu,yanzu da burin mu ya cika baki da wata amfani zaman me kike yi?,ince dai da mamin kike taƙama wai zata maye maki gurbin ƴa mace da baki samu ba kamar yadda aka buƙata a haihuwar muhammad ?,yanzu ina take?,taje neman nata burin,tayi maki nisan da ba zaki taɓa iya kamota baa!

NICE nan SHUGABA mariya na tura mami inda tya kamata domin cikar burinta!,domin tarwatsewar naki burin,mu zuba sai na ga bakin ki wallahi lanti!.

Jin wannan hayaniya kamar a cikin bacci yasa zainab ta tashi a razane domin ta gasgata maganganun  da taji daga bakin surukanta!

Yunkuri hajia lanti tayi ta dunkule hannunta na dama gam,ta cije lebenta na ƙasa!,nan take zainab ta fara salati domin mararta ke matukar murɗa mata kamar hanjinta zasu fita.

Ashe hajia lanti abunda ke cikin zainab ta riƙe kam cikin hanunta tana ƙoƙarin ganin bayan shi!,ganin haka hajia mariya ta  yi wani irin gurnani nan take wani haske ya fito daga idanunta kamar wuta ya soki hanun hajia lanti!,

zubewa ƙasa tayi tana gurnani nan a take hanun ya sale kamar wuta ya cinye!

Cikin zafin nama ta sake miƙewa,ba zan taɓa kyale abunda ke cikin zainab yazo duniya ba sai dai yau asirin kowa ya tonu a gidan nan!.

Barin taɓa bari burin ki ya cika ba koda zan rasa raina sai an haifi cikin nan domin shi zai kawo ƙarshen duk wani tashin hankali da rashin jituwa a gidan nan.

Barin kashe ki in kashe zainab ɗin idan yaso zan kashe kai na,wanda ya zamo toshin haddasa komi zai warware.,tsohon ki dake ƙaa shine babban anoba wanda ya ƙirƙiro duk wani mugun abu domin neman suna a duniya,gashi ya mutu ya bar maki gadon mugun abu har ɗiya da jikoki haka zai ta zagaya zur’ar ki!

Cacar baki ya kaure a tsakanin su ko wacce idnunta ya rufe..,a hankali zainab ta sulale daga saman gadon tana dafe da marar ta ta sulale zata bar ɗakin!,hajia lanti ta zabura tare da yin wani irin surkulle wani haske ya bayyana ta watsa shi a cikin zainab!,nan wurin ta zube tana ganin bishi bishi jini mai dubi ya fara bin ƙafafunta a guje kamar an buɗe famfo!

lokaci ɗaya taja dogon numfashi tare da ɗauke wuta.,hajia mariya tayi wani irin yunkuri tare da tattaru duk wani irin bajinta nata da niyyar tunkarar hajia lanti!,a zabure ta buga bangon ɗakin!,hajia mariya ta  hango mami ɗaure saman tsauni a galaɓaice ta fita hayyacinta ai kuwa ta zube a ƙasa cikin mutuwar jiki domin wanan faɗar yafi ƙarfinta.

Dariya mai rikitar wa hajia lanti ta kece dashing!,na faɗa maki wanan ba lantin da kika sani bane?
!,nayi ƙarfin da har abada ba zaki taɓa iya cin galaɓa a kai na baa!

IDAN kika fita a tsabgata zan kyale mami ta tafi inda  take so,amma zainab rayuwarta na cikin hatsari,abunda ke cikinta dai na gama dashi ta hanyar zuba dafi na musamman a jikinta!,kalli nan”bango ta buga wani hoton ya bayyana”,zainab ce kwance gefe tana kakarin mutuwa,yayin da zaki na gefe ina cin wani jariri saura kaɗan ya kai ga kaiser…,hajia mariya ta zabura tare da hura iska  wurin wani irin tsawa ya tsarwatsa bangon bat komi ya shafe!.

Daria ta sake yi sosai tana kallon hajia mariya,aikin gama ya gama ai mami na ƙarƙashin iko na sai yadda nayi da rayuwar taal,zainab kuwa awwani ƙalilan uka rage mata a ɗauki gawanta a sashin ki!,kinga alhakin mutuwar ta na kanki ta sake fashe wa da dariya!!!!

AYI HAKURI DA WANAN

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button