NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 13-14

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

Mutane nata tambayar page 9-10,kuyi hakuri mistake nayi wurin numbering nayi page 7-8 sau biyu idan ku ka duba labarin ya tafi dai dai,sai page na ranar Thursday ya kamata ya zama 9-10 na saka mashi 7-8 kuma.Ayita hakuri kuskure ne nagode❤ 


TALLAH!!!

ƙungiyar brilliant writers na yiwa masu karatu abishir da sabon littafin ɗaya daga cikin haziƙar maruciyar da zai fito bada jimawa ba”RASHIB HAIHUWA(da ciwo)daga alƙalamin OUM FARHANA(habibah shehu)kada ku ku sake a baku labari

????13-14

    Shiru ne ya biyo baya ko wane da abunda yake tunani a cikin zuciyar si har suke isa babban gida ya yi horn mai gadi ya buɗe tare da mashi barka da zuwa.

Tunda suka aje mota ya taimaka mata ta fito,samarin dake haramar gidan suke mata Allah sanya albarka(da yake ya kira kowa a waya ya faɗa masu),sai dai ta murmusa domin tana da alkunya,shike washe baki yana amsa wa har suka wuce inda mutane suke saura ƙiris su isa sashin hajia lanti yace,darling barin ɗauke ki nasan kin gaji da yawa ko?.

Waro idanu tayi waje,don Allah ka rufa mun asiri ina da kunya..,oh ni ne mara kunya ko?,wai naga ko irin ɗan alkunyar nan babu sai washe baki ka ke kana amsa gaisuwa.

Ah zee ALLAH ya amshi addu’ar mu na tsawon shekaru goma ha biyar yau ya azurta mu da samun namu rabon,jinin mu babu sirki!,kinga kuwa ba zan zama butulu ba ko?.

Haka ne,Allah ya inganta mana yasa rabo ne. Yawwa matata amin thumma amine,dai dai ƙofar hajia ya tura da sallama hanun shi ɗauke da kayan zainab….,tana zaune a palon tare da matar umar da yaranta suna karin safe.

Wuri zainab ta nema a ƙasa”ina kwana hajia,ina kwana aunty balki?”,hajia bata amsa baa,ita balkin ce ta amsa a ciki bakinta cike da ƙosai ga kofin kunun gyaɗa gaban su,yaran kuwa shayi suke sha.
wanan ya zama ɗabi’an surukan hajia lanti banda zainab,kusan kullum zasu kwaso yaran su a gidan zaa karya,aci na rana har na dare idan mazajen sun shigo nan zasu ci sanan su kwashi matayensu a tafi gida. Idan lokacin makaranta ne iyayen na wurin aiki daga makaranta aka ɗauko yara gidan zaa zube su sai dare a dawo dasu

Gaisawa suka yi da muhammad  cikin girmamawa har da addua ALLAH raba lafiya balki tayi.

Hajia ta tsare gida  hankalinta kwance tana karyawa,har ta gama suna zaune mai aiki ta kwashe kayan…,sai lokaci ta ɗago ta kalle su da kyau idanunta kur akan cikin zainab daga bisani tace,”ina mamin?”,kallon juna suka shiga yi babu bakin magana domin hajia ta tsare su da ido,zainab ma kallon tuhuma take mashi!.

Cikin inda inda yace,ai na ɗauka tan nan wurin ki ….,da ka kawo ta yaushe?,”ta daka mashi tsawa!”,ayi hakuri dai hajia wallahi koda na koma gida mun duba sosai a mai gadi bata nan,inda nasan za’a same ta naje bata.

Ƙarya ne wallahi kun yi kaɗan!,daga matar ka ta samu ciki sai a iza mun jika saboda ba sonta ku ke yi baa?,miƙewa tayi,na baka awa ɗaya duk inda take ka nemo mun ita!,tana kai nan ta wuce ɗakin ta cikin tashin hankali…,zube wa tayi bisa gwiwar ta hanunta duka saman kanta,sosai ta riƙe shi domin yana juya mata!

Mami!,mami ina kika shige ne?,idan kika yi nisa dani asirina zai tonu,kece rufin asirina!,shekaru ashirin ke nan ina ɓoye da wanan sirri don ALLAH kada ki guje ni zan tozarta a idon duniya domin kece maganin matsalata,cikinn nan na jikin zainab ba ƙaramin barazana bane a gare ni!.

Kamar wacce aka tsikara ta miƙe zuwa palo…,daga naya suka jiyo muryar ta,ka tashi ya nemo mun jikata!,zan cigaba da riƙe matar ka a gidan nan har sai ka gano inda mami take!.

Cikin tashin hankali zainab ta kalle ta domin jin abun take kamar wasar kwaikwayo!,ba a ga mami baa?,itace zata zauna a gidan hajia har na tsawon wani lokaci?.

Yana miƙewa itama ta miƙe,ƙafata ƙafar ka wallahi ba zan zauna ba duk inda aka kai mun yarinya sai an fito da ita domin na lura kaf ahalin ka babu mai sona da cigaba,ana ɓakin ciki da farin cik na!

Daakata zainab!,”ya daka mata tsawa”,da wanne zan ji ne saboda Allah?,duk wanda ya fi muhimmanci!.

Lallai moha a gaban ka zainab take ci mun mutunci kada kallo?,kiyi hakuri hajia mu yi abunda zai fisshe mu,ya zama dole zainab ta zauna a gidan nan domin bata da lafiya,zan fita neman mami.

Wallahi ba zan zauna ba garin mu zan koma kuma tare da ƴata!,kada kije ko ina Allah zainab zan mumunar saɓa maki idan kika bar gidan nan!,ai ba yau ka fara saɓa mun ba.

Hanyar waje ya nufa ta bishi a baya…,bayan hanunan shi yasa ya bugeta!

Jiri ya kwasheta nan take ta dafe bango tare da yunƙurin sake bin shi…,
ai kuwa ƙafa ya saka ya shure ta a gefen ciki!

Ƙara ta saki tare da dafe wurin nan take ta fita hayyacin ta..,hajia na zaune zuciyarta fal farin ciki burinta zainab ta fice daga rayuwar ɗanta,domin ita ɗin barazana ce a gare su.

Balki dai tausayin zainab ya kamata domin a gaban hajia ne kawai take nuna mata ƙiyayya,cikin zuciyarta tana matuƙar sonta da tausayina gudun ɓacin ran hajia yasa bata nuna wa.

Mai aikin hajia mariya da yanzu driver ya sauke ta sun dawo daga kasuwa tunda suka shigo komi akan idonta ya faru har muhammad  ya shiga mota zai wuce…,ta isa wurin zainab tana mata sannu ta kamata zuwa sashin hajia mariya,lokacin hankalin hajia lanti na kan yaran balki da suka fara kuka ganin abunda ke faruwa(abunka da yaro).

Koda ta duba babu zainab a ƙofar ɗakin,a zabure ta tashi domin a leƙa…,bata nan kuma ba motar muhammad .

Idanu ta rinƙa zarewa kamar mahaukaciya,balki kinga babu zainab a wurin ko tare suka fita ne?,girgiza kai tayi,ban lura ba hajia.

Zirga ya shiga yi ina zainab ta shige nea?,wanan rana yazo mun da rashin sa’a babu zainab ba mami!?.

Waya ta ɗaga ta kira muhammad daya parker mota a gefen titi yana kukan nadamar abunda ya aikata wa zainab,bayan a gaban shi likita ya bada sharuɗan a kula da italy,ta ina ma zai fara neman mami?.

Wayar shi dake ruri ya maido dashi cikin hayyacin shi ya ɗaga”tafi ya kayi da matar ka ko?”,xuwa ina kuma hajia?,gidan ubanka lalatacce kawai,idan ba tafiya kayi da ita ba ina ta shiga?,ni ban sani ba domin nan na barta a gidan!,”yana kai nan ya kashe wayar gaba ɗaya”,ya shiga tashin hankali.

Balki na zaune cike a mamaki da tsoron hajia,domin sai sambatu take kamar mahaukaciya har ta fara zargib akwai wata a ɗasa!

Mai aikin hajia mariya na isa da zainab sashin,hajia ta taso cike da tsoro”me zan gani haka?”,hajia ban san meke faruwa ba kawai na ganta ne duƙe a ƙofar sashin hajiyar su shine na wuto da ita nan.

Riƙo ta tayi meke faruwa dake zainab?,muna farin ciki an samu ƙaruwa kuma!

Ashhaa zainab sannu!,lami kai ta ɗakina saman gado barin kira hafsa a waya tazo a duba taa(matar yaronta ma aikaciyar jinya ce).

Saman gado ta ajeta sai sannu take jero mata…, har lokacin hanunta riƙe da wurin da ya shure ta.

Hajiyata shigo tana yimata sannu har hafsa ta iso gidan daga wurin aiki..,a hanzarce ta shigo suka gaisa hajia na faɗa mata zainab nada shigar ciki ne kuma kamar tana fama da ciwon mara.

Kayan awon cik ta fito dashi tare da duba yanayin cikin,babu wata matsala ta fito da wani alurra kwalba uku ta haɗe wuri ɗaya tayi mata.

Zata yi bacci sosai kada a tashe ta har sai ta tashi don kanta in shaa ALLAH zai bari.

Albarka hajia mariya ta sanyawa surukar ta tare da fatan alheri.

Ba’a daɗe ba bacci ya ɗauke zainab,hajia ta jima tana kallon ta cike da tausayawa domin babu abunda bata sani ba kawai ƙyalewa takebab,amma tayi alƙawari ba zata ƙyale hajia lanti ba idan wani abu ya faru da cikin zainab domin kar ta san kar shi yasa basa shan inuwa ɗaya!.

Bata son kai ƙararta wurin mijin su saboda bashi da cikakken lafiya,nan take ne jinin shi ya hau.

palo ta koma tare da ɗauko wayarta ta shiga neman lambar hajia fatima(mahaifiyar zainab)…,daga ɗaya ɓangaren safiyyah ta ɗaga da sallama,bayan sun gaisa tace taba hajiyar su waya.

Tace ta kashe zaa kira anjima domin tana wurin wanka ne.

Kashewa suka yi safiyyah dai hankalinta ba kwance bp,saboda tun ranar da mami ta kirata akan zasu zo ,zainab ta amsa tace da maman su akwai matsala akan lamarin mami hankalin su ya kasa kwanciya har yau da safe da muhammad  ya kira yaba faɗa masu zainab na ɗauke da shigar ciki.  Sai dai tun lokacin suke kiran layinta baa ɗaga ba a ƙarshe ma wayar a kashe.

Hajiyar su na fitowa tayi saurin kiran hajia mariya..,bata ɗauki lokaci ba ta ɗaga wayar da sallama.

Suka gaisa cikin mutunta juna a matsayin su na manya,hajia mariya
tace hajia fatima magana nake so muyi na fahimta a matsayin mu na many,domin abunda babba ya hango yaro ko ya hau ribi ba zai hango baa.

Tace haka ne hajia mariya,yawwa akan maganar zainab ne,tsakani da Allah yarinyar nan tana cikin damuwa matuƙa,idan da hali ku ɗauke ta kawai ta dawo gaban ki,saboda wata rana fa sai dai a kira ku ɗaukar gawanta.

Subhanallah!,abu bai yi daɗi ba kuwa hajia,kin san sha’anain ɗan yau baka matsa mashi idanba shi  ya kawo maka magana baa,sai ka saka mai idanu lamarin mata da miji sai Allah.

Duk da haka hajia fatima ya kyautu ki jata a jiki,ɗan yau sai da rarashi musamman zainab ba mai yawan surutu bace akwai zurfin ciki.

Tau hajia wallahi babu abunda zan iya yi a kai domin mahaifin su nada tsauri sosai,ba zai goyi bayan a dawo da ita gida ba amma zan turo safiyyah idan ya amince ta ɗan zauna da ita har cikin yayi ƙwari.

Jikin hajia mariya yayi sanyi domin taso su duba lamarin dai da idon basira,rayuwar zainab da abunda ke cikintana cikn hatsari!,bata so aji komi a bakinta ne kada ace ta haddasa fitina.

Iyaye muji tsoron Allah ku sani yaran nan da Allah ya baku amana ce a gare kurt,akwai hisabi a tsakanin  ku,kuja su a jiki domin sanin damuwar su,ku fi kowa kusance dasu ta hakane kawai zasu sake daku sosai,duk da yawancin mata da suke fuskantar ƙalubale a gidajen auren su gudun ɓacin ran iyayen su yasa suke ɓoye wa,iyayen basa yiwa yaran adalci idan magana ya fito baa taɓa tsayawa a jita bakin mace sai a ɗaura mata laifin gaba ɗaya,kafin ka sani anyi rayuwar ta mummunar illa,Allah yasa mu dace.

Ɗakin ta sake leƙawa,zainab na bacci cikin kwanciyar hankali..,kitchen ta nufa ta bada umurnin abunda zaa dafa wa zainab mai ruwa ruwa.

Duk data manyanta sosai mace ce mai kazar kazar da motsa jiki shi yasa ba kasafai ake gano ainihin shekarun ta baa.

Muhammad gajiya yayi da yawo ya nufi office ɗin babban yayan shi..,bai ɓata lokaci ba ya zayyane mashi komi,shawara suka yanke kawai zasu kai report wurin yan sanda,gidajen radio da talabijin sanan  su sanar da mahaifin su domin idan yaji daga sama ba zasu ji daɗin halin da zai shiga baa.

Haka ko sukayi,sai da suka nufi duk inda ya kamata akayi sanarwa sanan suka nuka sanar da sauran yan uwan su a haɗu a gida akwai taro na gaugawa.

Mami ce duƙe gaban wata mata a wani katafaren gida,sai dai matar ta juya baya baa ganin fuskarta.

shiru ya ratsa wurin daga bisani matar ta furta,ya zama dole ki nisanta  dasu domin cikar burin ki,lokaci da muka ɗiba maki yayi da zaki nisanta kanki da kowa naki mami!

Godiya nake kuma ban manta da alƙawarina a gare ku baa,amma ina neman alfarma a ƙara mun lokaci rayuwar mummyna yana barazanar tarwatse wa,ya zama dole in bata kariya daga azzaluman dake ƙoƙarin ganin bayanta!

Dakata maami!,har sau nawa zaa rinƙa baki dama mahaifiyar ki na wasa da damar ki?,in ce taurin kai ne da ita ko an hanata aikata abu sai tayi?,shike wahalar da rayuwarta ai,abunda baki sani ba kawai suna amfani dake ne wurin tarwasa farin cikin iyayen ki,idan baki nisanta kanki dasu ba sai kin zama ajalin iyayen ki!.

Duk na gare komi fin ƙarfi na akayi,ki sani har yanzu banyi ƙarfin da zan iya bawa iyaye na wani kariya na musamman baa,idan ban bi abunda suke buƙata ba zan rasa iyayena ne!

Zaki rasa mahaifiyar ki ne kawai idan har ta cigaba da yin taurin kai,mudin ta nufi hanyar kazaure sai gawan ta!,yanzun ma da take a cikin gidan nan rayuwarta da abunda ke cikinta na cikin hatsari babba,zama ɗakin mijinta shine babban kariya a gareta ko baki faɗa mata bane?”cikin tsawa ta tambaya”,na faɗa mata amma ta kasa fahimta,duk yadda naso hanata fita sai ta bijire,ina neman alfarma a bani dama in kula da ita har ta haifi abunda ke cikin taa,daga nan zan nesanta kai na dasu yadda ko labari na ba rasa taɓa jiba.

Ba zai yiwo ba mami!,ke ɗin yar aiki ke kuma kin isar da saƙon ki a tsakanin su,kin wanzar da farin ciki a zukatan su,lokaci yayi da zaki bar su har abada!,ko kin manta burin ki na son zama shugabar yan
ƘUNGIYAR ASIRI NE? ban mata ba ya shugaba na!,shine kike ƙoƙarin wasa da damar ki?,mutane nawa ke neman wanan dama a duniyar
ƘUNGIYAR ASIRI? ,amma basu samu baa?.

Lokaci yayi da zaki koma akure wurin mai girma father john domin samun horo na musamman akan wanan buri naki!.

Ina ƙara neman alfarma dai a barni na gana da ahali na kafin tafiya taa!

NA GAMA MAGANATA!,”matar ta faɗa tare da ɓace wa ɓat kamr walƙiya!.

https://youtu.be/ixxq7FYwJ-o

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button