GURBIN IDO

GURBIN IDO 12

    Yuuman na fita ta aiki laulo a sirrance yayi mata kiran daada,bata bata lokaci ba kuwa tazo,ta kuma rattaba mata dukan bayani,kishi ne sosai ya kama daadan,me yasa bata nema safiya ko zubaida ba?,indai ko haka ne bata ga dalilin da zata aika gaje ba su da sukafi kusa da daadan suna zaune,gwara maimunatun taje,ko da zata samu kudi daga gareta ai dai ba zata samu jin dadi da daular dake gidan anni ba

“Ya zakiyi ragon azanci irin haka furera?”

“Kaman yaya innar himu?”

“Ta yaya zaki tura gaaje?,tafiyar maimunatu ai shine dai dai,zata je fa samowa gaje kudin aurenta da wanda zaki mata kayan daki da sauransu,don na tabbatar miki himu gini yake na kere sa’a,kinga kina buqatar kudin da zaki mata duk wata hidima,na tabbar jauro zaiyi iya abinda yaga zai iya ne,abu na biyu idan maimunatu ta tafi dole ne himu ya sake haqura da ita,ya kuma tattara hankalinsa ga gaje,saboda maimunatu tayi masa nisan da yasan bazai ganta ko ya sameta ba,kinga komai zai tafi mana dai dai babu wata matsala,sannan ke kanki yarinyar nan alaqaqai ce a wuyanki,har mamaki nake yadda kika ci gaba da riqon diyar mai miki kiwo,kinga yanzun kuwa salamun salamun” sosai inna furera ta gamsu da shawarar daada,tabbas ita din masoyiya ce,kuma maganganunta na bisa hanya,maimunatu zata zame mata tamkar wani jari,hankalinta kwance zata zama wata me arziqi tana daga kwance,da wannan gamsuwar ta taka da kanta har gidan bappa labaran,ta kuma tabbatarwa da anni cewa ta amince.

     "Nawa ne kudin da za'a dinga biyanki na aikinta?" Anni ta tambayi furaira da kanta tana kallonta,tsanarta na shiga ran annin,murmusawa tayi sannan tace

“Ina ganin a duk wata ki bada dubu biyar” inna furera ta fada tana fatan anni ta amince da kudin data yanka din.

“Na ninka miki sau hudu,zan dinga aiko miki da dubu ashirin da kuma ladan kiwo” mamaki ne ya cika furera qwarai,har ma ta rasa abinda zata fada,bata taba tsammatar samun haka daga anni ba,ashe maimunatu alkhairi ce tare da ita,ashe ita shatu ta haifawa.

     Cikin tsananin murna da farinciki ta koma gida,ta samu maimunatu ta gama da wanki ta kuma dora sanwar abinci,bayanta kamar zai karye saboda duqen da tasha,sanda fureran ta kirata ta shiga fargaba da tsoro

“Zauna nan,ki kuma saurara da kyau kiji abinda zan gaya miki” qas tayi da kanta,zuciyarta na tsananta bugu,tana ayyano masifu kala kala a ranta,ko waccece ta sameta a yau din?.

“Dattijuwar da tazo gidan nan kwana uku da suka wuce,ta ganki kuma tayi sha’awar tafiya dake domin ki taimaketa da aikace aikace,na kuma amsa mata,don haka ki zama cikin shiri,daga gobe zuwa kowanne lokaci zata daukeki ta tafi dake can garinsu” da fari maganar ta razanata,ta kuma rude sosai,ta lumshe idanunta tana kiran

“Ya Allahu,ya Allahu” a hankali sai taji zuciyarta ta fara dai daita data tuna daga inda matar ta fito,daga bangaren yuuma,yummar da zata iya cewa kaf fadin rugar ita kadai ce masoyiyarta,ta tabbatar yuuma ba zata bari abunda zai cuceta ya rabeta.

     Ta sake maida tunaninta ga matar,akwai cikakkiyar suffar kamala dattijantaka tattare da ita,ta tuna yadda take dubanta fuskarta dauke da fara'a da kuma tarin kulawa,tabbas akwai kyakkyawan zato a kanta.

“Bakiji bane!” Kakkausar muryar inna furera ta saukar mata cikin kunnuwa,sai ta bude idanunta tana gyada kanta

“Kina jina ko?,wallahi wallahi kikaje kika aikata wani mugun hali,ko kikaje kika gwada musu halin maitarki kikayi sanadin da kika dawo gidan nan,na rantse da sarkin da raina yake hannunsa saikin gwammace mutuwa da rayuwa,duk da bansan matar ba a zahiri,amma na tabbatar gida ne na wadata,basu damu da abun duniya ba,duk wani abu me amfani da kikaga sunyi wasarere dashi ki dauka ki adana min,ni ina da buqatarsa,kome zakici maimunatu idan zai ajjiyu baki ajjiyemin ba Allah ya isa” maganganun data dinga yi sun yiwa maimunatun nauyi qwarai,sai tayi qas da kanta tana saurarenta har sai data gama ta sallameta.

   Yini tayi cikin taraddadi da kuma fargaba,duk da tana samun relief duk sanda zuciyarta ta gaya mata cewa yuuma ce,masoyiya guda daya da take da,ta bangarenta ne wannan lamarin,sai tayi qoqarin saisaita qwaqwalwarta tare da addu'ar kome meye ya zame mata sauqine na rayuwarta.
Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button