Uncategorized

MATAR UBA 26

????????????????????????????????     *MATAR UBA*

????????????????????????????????

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*????MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION????????️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

 “`NOT EDITED

CHAPTER 26“`

“Aunty you’re like an angel to me, I just want to see you”

Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi awa d’aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.

Ba Asiyah kad’ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.

????????????????????????????????

………. “Are you ready?”

Ammar ke wa Asiya wannan tambayar Murmushi tayi ta d’aga Masa Kai alamun eh, Shima Murmushin yayi ya kalli Hashim yace “She likes laughing”

Murmushi kawaii ya Masa.

A hankali ya Fara cire bandage d’in Diyya da Hashim duk hankalin su na kanta , sai da ya rage bandage d’aya Ammar ya ummurci Diyya da ta tsaya a gaban Asiyah hakan kuwa akayi, bayan ya cire idanun ta a rufe yace “Open your eyes slowly and carefully”

A hankali take Bud’e idanun ta tana ganin wuri bashi bashi ba idanunta na wassakewa ta sauke su akan wata kyakkyawar halitta fara, ba doguwar bace sannan ba gajera bace Murmushi tayi Mata ita ma Maida Mata “Aunty Diyya kece?”

“Eh nice” idanun ta ya cika faal da hawaye mikewa Asiya tayi ta rungume ta kyam a jikin ta cikin kuka take Mata godiya.

Gyaran murya Hashim yayi “Wato ni ba a damu dani ba ko? kin ma manta Dani?” Yadda yadda maganar ne ya sanya ta dariya Yana magana Kamar d’an shekara biyar harda langwab’ar da Kai, Kare Masa kallo tayi ganin yanda ya canza ya Kara haske ya Kara kyau.

Karasowa yayai gaf da ita Diyya ganin zai iya ture ta, ta matsa ta basu wuri, kallon kallo sukeyiwa juna, wani irin wutar son junnan su ne ke tafarfasa a cikin zukatan su, hannu ta ya riko yace “Nayi matukar murna da idanun ki suka dawo Baki ji yanda nake ji ba ba yau”

“Hmm nago….. ” Saurin rufe Mata Baki yayi da lausassan hannun sa ya gyad’a Mata Kai had’e da fad’in “Ban bukatar kalmar godiya daga gare ki, Nayi wannan ne a matsayin ki na wacce na fiso, wannan kad’an ne, sannan kofa a Bud’e take idan kina bukatar wani abu just tell me”

“Ko wacce irin bukatar da Zama maka dashi zaka min?”

“Eh insha Allah just name it”

Diyya har ta Isa kofa zata fita Asiyah Tace “Aunty Dan Allah kizo”

Ba musu ta karasa inda suke, kallon sa tayi Tace “Inaso ka had’a ni da Aunty Diyya ma’ana ka aure mu”

Zaro Ido yayi yace “Amma wasa kike ko?”

“Dagaske nake”

Iska ya hura Mai zafi yace “Na amince” ya Maida kallon sa ga Diyya “Da fatan zaki amince da hakan My Diyya?”

Saurin ‘dago kanta tayi tana kallon sa cike da mamaki sakin hannun Asiyah ya nufi inda ta tsaya Murmushi yayi yace “Kina mamaki ne?”

Kai kawaii ta d’aga Masa Murmushi yayi yace “Maganar aure ne ya baki mamaki ko Kuma Kiran ki da nayi da My Diyya?”

Kai a kasa murya chan ciki Tace “Duka biyu”

“To ki daina mamaki kinji”

Kai ta d’aga Masa idanun ta hawayene ,d’aga habarta yayi yace “Kuka? Please ki daina” ai kuwa kamar ce mata yayi ta kara, ganin kukan yayi yawa ya rungume ta, a tare suka sauke wani ajiyar zuciya.

Asiyah sai Murmushi take (Ni ko nace Asiya Murmushi Kuma ko Yar kishin Nan babu) Diyya da Hashim sun Lula wata duniyar,dama gogan naku Yana so Yana kaiwa kasuwane a kunne ya rad’a Mata “I miss you Bae”

“I miss you too” Kara kankame ta yayi a jikin sa kamar zai Maida ta cikin cikin sa.

Gyaran muryar da ammar yayi ne suka tuna Basu kad’ai bane yayi saurin sakinta kamar wani Mara gaskiya.

Dariya Ammar yayi yace “Congratulations Asiyah”

“Thank you Dr”

Hashim yace “Is there anything left?”

“No I have already discharge her”

“Good in that case we are going back to Nija tommorow”

” What so soon?”

“Yeah what will we wait for?”

“you’re right, but Amma gonna miss you guys”

“Same here bro, you’ll attend our wedding right? Cos you’ll be our guest of honor”

“Insha Allah, ill be there.”

A motar sa ya Maida su har masukin su, sannan yace zai dawo da yamma su fita cin dinner, Hakan kuwa akayi karfe takwas ya dawo ya d’auke su suka fita,tare da matar sa suka zo, Sunci sun Sha har sai karfe goma saura ya dawo da su, sannan ya musu alkwarin Kai su airport.

Baccin su suka Sha Mai dad’i Amma Banda Asiyah tana ta tunanin abinda zata tarar indan ta koma gida sai kusan karfe uku amba dare ya barci ya sace ta,karfe biyar saura ya kwankwasa musu kofa, tashi sukayi sukayi sallah sannan suka shirya, karfe biyar da Rabi Amma ya kirasu cewar Yana waje, already sun so jakar su kawaii suka d’auka suka fita, Hashim na ganin jakar hannayen su yasa hannu ya karb’a.

Hira suke Sha duk su ukun har suka karasa inda motar Ammar yake,ban kwana suka Masa,shi kuwa yace Yana Nan Yana zaman jiran IV.

Suna shiga jirgin ko wannen su ya duba sit d’insa wannan karon shi ya zauna a tsakiyar su, kallon shi sukayi sai ya d’aga musu gira kallon juna Asiyah da Diyya sukayi suka tuntsire da dariya, Zama sukayi Sabida Ana sanarwa jirgin zai tashi,Hira suke sama Asiyah ce ta Fara bacci, ba a d’au lokaci Mai tsawo ba Diyya ma bacci ya d’auke ta sai zuba surutu yake Jin ba mai bashi amsa ya Dubai yaga duk sunyi bacci,ganin yanayin baccin nasu zai iya sanya musu ciwon wuya ya rungume Diyya da hannu d’aya kana ya kwantar da Asiyah a cinyar sa, daga bisani Shima baccin ya d’auke sa.

Diyya ce ta Fara farkawa, Murmushi kawaii tayi ta sake komawa baccin ta, basu farka ba har sai da jirgin su ya sauka Nija, a hankali Suma fara Bud’e idanun su. Idanun shi ya sauke Akan Diyya dake ta kallon sa gira ya d’aga mata Yana Mata kallon lafiya, Murmushi tayi Masa ya sa hannu ya shafa fuskar ta, Asiyah kuwa Mika ta shiga yi “Wayyo bayana”

Dariya sukayi yace “Allah ya bani hakuri Ni da kuka danne Ni”

Asiya Tace “hakkin Kane kula da mu,ko ba haka bane aunty?”

” Hakane Kanwata”

“Au had’e min Kai zakuyi lallai sai nayi da gaske”

Dariya kawaii sukayi,suna fita suka Tarar da Faysal na jiran su,Gidan su Diyya suka wuce yace “Zan zo Hira anjima” sukayi wucewar su.

Umma tayi matukar farin cikin ganin su musamman da yanzu Asiyah tana gani “Haba Badiyya tunda Kuka tafi ba Kira shiru haka gashi Ni ko na kira ba samun ki nake ba”

“Yi hakuri Ummu wallahi tunda mukaje muke ta fama da zuwa asibiti ban zauna ba shiyasa”

“Tunda an Samu abunda aka je nema ai Shikenan”

“Yanzu Asiyah ya ake ciki da maganar Baraka take da suna ko?”

“Eh umma Baraka,ban San yanda ake ciki ba,Amma insha Allah gobe zanje Ni gidan maman Yesmin naji yanda ake ciki”

“Har sai mun jira gobe? Ai ki tashi mu tafi kawaii yanzu,baza ki gane yanda na damu da aka Mata ba”

“Aunty daga dawowar mu sai mu fita ga gajiya ko hutawa ba muyi ba,ki Bari sai gobe kawai”

“Gaskiya Asiyah take fad’a ku bari sai gobe kuje d’in” umma ke wannan maganar.

“To” kawai Diyya tace don taso su je a yau d’in nan.

Mummy tayi mutukar farin ciki duk da Bata San dalilin sa na tafiyar ba, kwata kwata kwanaki biyar yayi baya gidan Amma ji take kamar ya fi wata,bayan ya huta ne ta zaunar da ita duk abubuwan dake tafiya, Kama daga kan Maganar Shirin auren da yayi na karya da Safiyya, har izuwa ‘batan da Asiyah tayi da samun lafiyarta da Kuma Shirin da suke na kama Baraka, har izuwa alkawarin auren da yayi wa Asiyah da Diyya

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button