GURBIN IDO

GURBIN IDO 27-30

“Alhmadlh ya rabb” ta fada can qasan zuciyarta,sai ta dubi matar da suke tare

“Ki shiga ciki kice ina samra?,ta baki waje kici abinci,zan kiraki mintuna kadan” miqewa tayi tana godiya,sannan tabi hanyar da zata sadata da farfajiyar sassan haj aishatun da take kamae qaramin tsakar gida mai siffar garden da aka wadata da wasu fararen duwatsu na wuta.

     Ci gaba yayi da takowa cikin falon,yayin da amma wannan karon tayi qoqarin ajjiye kunyar dake tsakaninsu

“Maraba lale,ashe kuna gab da isowa?” Wani dan qaramin miskilin murmushi ya subuce masa,ya qaraso gabanta ya zube ya soma gaisheta,tana amsa masa itama cikin kulawa tare da karantar yanayinsa.

Baiyi wata qiba ba sam,saidai jikinsa a murje yake kadan,sai kuma fatarsa data sakw fresh da kuma haske,alamin weather din qasar data karbeshi,akwai maganganu masu tarin yawa dake ran amma,saidai a yanzun kamar yayi wuri tace komai,don haka ta barwa lokaci na gaba idan suka gama warwarewa daga gajiyar tafiya.

Yadda ja’afar ya zube mata haka jabir,don marabarsa da ja’afar din daukan cikinsa ne na tsahon wata tara ne kawai batayi ba.

Kusan shi ya fara fita yabar jabiru da amma,wanda dama koda a baya abun kusan haka yake,hirarsu da amman bata qarewa,zaka sauka jabir ya haifa ba ja’afar ba.

Yana fitowa sukayi kacibus da ammi,kana kallonta kasan an fara shiga hidima,daga boys quarters na gidan take,taje ta duba yadda aka gyara gami da tsara wajen saboda saukar baqi ‘yan biki.

“Oyoyo,saukar yaushe?,ina ta ciki ban jiku ba?” Murmushin gefan baki yayi,ya gaidata itama a girmame kamar yadda suka saba

“Me zakuci?,don gidan gaba daya a hargitse yake,banjin zaku samu kalar abincin da kuke so”

“Ki turo mana hisham kawai ammi” muryar jabir dake tahowa daga baya ta bata amsa,don yasan halim ja’afar din sarai,tsaf zai iya cewa

“We are okay” bayan shi magana ta gaskiya yunwa yakeji

“Banajin zaku samu hisham cikin gidan nan jabir,gidan yau kusan babu kowa sai baqi,yana can hidimar saukar nasu baqin”

“Ba damuwa zan kirashi” jabir ya fada suka soma gaisawa sannan shima yabi bayan ja’afar wanda ya wuce sassan anni,ammi tayi gaba tana tunanin abinda zata sa a samar musu me dan sauqi da zasu iya ci.

       Sanda ya sanya kai falon har yayi kamar zai koma saboda muryoyin baqi da yaji sai kuma yaci gaba da cusa kai,sai daya shiga din sannan ya fuskanci su waye a falon,anty maama ce,sai ummi badi'a matar uncle abbas.

     Qaramin tsaki yaja qasan ransa,su kadai amma sun cika falon da hayaniya kamar mutum dubu,dukkansu maraba suke masa banda anni da taja bakinta ta tsuke,ya qaraso ya zauna saman hannun kujera yana amsa marabarsu,kafin dukansu su biyun su miqe anty maama tana cewa

“Anni bari muje,nan da awa biyu idan bamu dawo ba don Allah hayatu ko muslimu suje su debomin yaran nan”

“Zan gaya musu,amma kada kuje ku zauna kuma”

“Muna samo abinda mukeso zamu dawo”

“Allah ya tsare” suka amsa suna ficewa,sai falon ya rage saura shi da annin.

       "Barka da warhaka" ya fada cikin rusunawa

“Barkan ka” ta bashi amsa a taqaice tana bata fuska,saidai a yau din baiji bata fuskarta ya dameshi ba kamar yadda suke da ita a baya,yana jin a wannan bigiren shi yafi cancanta ya bata fuska akan kowa

“Ina wuni?”
“Daban wuni ba zaka ganni?,ai da zamanka kayi a sassanka,ni yafi cancanta nazo na gaisheka ai,tunda yanzu ka zama uban kowa,sai abinda kakeso ka tsara zamu dinga bi,tunda kaika haifi kanka” kyawawan idanunsa ya lumshe kana ya budesu,ita tsohuwar batasan abinda yakeji bane?,batasan irin qunci da ciwon data haddasa masa ba haka siddan yana zaman zamansa yana lallaba rayuwarsa?

      Muryoyin sallamarsu ta katse anni daga ruwan tijarar data debo ta shirya sauke masa su tas yau a kansa,duka 'yammatan gidan ne suka shigo,wansa dawowarsu kenan daga gyaran gashi.

    Da hayaniya suka shigo saboda yadda sabgogin bikin suka fara musu dadi,amma suna hada idanu kowacce sai tayi turus,ta kuma saita bakinta,kudin goro ya yiwa gaisuwarsu ya amsa su gaba daya,babu wadda tayi gigin zama dukka suka juya suna barin sashen,daidai lokacin da amna wadda aka yiwa kanta gyara na musamman take rugowa cikin falon riqe da leda a hannunta cike da kayan qwalam tana qwalawa anni kira gami da cewa tazo suci.

     Cak ta tsaya sanda tayi idanu hudu da mahaifin nata,sai kuma ta watsar da ledar hannun nata,ta take da gudu tayo wajensa tana kiran 

“Dadddyyyyy….” Qasa ya sauko ya tanqwashe qafafunsa,ya kuma bude mata hannayensa gaba daya,yana jin wata irin qauna da qarfin jini dake tsakanin uba da diyarsa yana fusgarsa,ta kuwa iso ta fada jikinsa,ya sanya hannayensa gaba daya ya rungumeta cikin jikinsa yana sauke ajiyar zuciyaSosai ta qanqameshi itama kamar zata koma jikinsa

“Daddy” ta sake kira tana sauke ajiyar zuciya bayan shuru da tayi na wasu sakanni,dukka gaba dayansu shida annin sai tausayinta ya lullubesu,ya dagata sosai ya sake tallafarta yana dubanta

“Amnee” ya kirata da sunan da shaheeda kadai take kiranta da shi

“Daddy….kaima shine ka tafi ka barni?,mommy ta tafi,amra ta tafi,kaima haka?” Kai ya girgiza yana shafa sumarta da tasha gyara tana ta qyalli

“Am sorry my little angel……daddy yana neman afuwa,bazai sake tafiya ya barki ba” fuskarta ta washe sosai,da alama taji dadin maganarsa,sai kuma ta sake cune fuska

“Adda maimoon ma ta tafi,har yanzu bata dawo ba,daddy zaka je ka dauko min ita?” Anni ya kalla da alama yana da buqatar qarin bayanin sanin wacece ita,kamar kuma ya jijji sunan a bakin annin da ammansa,ganin anni bata bashi wani hint da zai gane wacece ba sai ya gyada kai kawai

“Zan dauko miki ita lil princess” qanqameshi tayi tana murna

“I love you daddy”

“Love you more amne na” sai ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya dake nuni da samun cikakkiyar nutsuwa.

    Karamin tsaki anni ta sake

“Kalli…..wannan daukar hakkin har ina?,Allah ya kyauta wannan banzar zuciyar taka data kasa daukan kalar tata qaddarar” bai tankawa annin ba,don yasan jiqaqqiya ce tsakaninsa da annin,kuma ba zata qyaleshi ba tabbas sai ta maida masa kai tsaye ko kuma a fakaice.

    Koda ya tashi tafiya qin yarda amna tayi ta sauka daga jikinsa,tana maqale dashi,da ita yatafi sassansa,ya samu.jabir har ya fito a wanka,yanata fama da wayoyin al'umma.

28

  Wani kallo ja'afar ya watsa masa,da alama gayyar al'umma yayo musu,wanda shi baisan da hakan ba,bai kuma shiryama tarbar kowa ba,dakinsa ya wuce ya sauke amna saman gadonsa,tana ta faman zuba masa surutu,labarai iri iri,a lokacin idan kaganshi kai baka ce miskilin ja'afar din nan bane,mai yawan dakiya tsare gida da kuma shan qamshi,duk yabi ya cika fuskarsa da fara'a,hakanan duk tambayar da amna tayi masa sai ya bata amsa,saidai da yake halin a jininsa yake,ba jimawa yaji kansa ya fara cakewa da surutun amnan

“Amnee…..pls be quiet for a while,ki huta kada maqogoronki yayi ciwo,zanyi wanka,idan na fito then sai muci gaba” kai ta gyada masa,sai dai tun bai gama fidda kayan jikinsa ba taci gaba daga inda ta tsaya.

    Yana daga toilet din ma yana saurarenta,murmushi kawai ya saki ya girgiza kai

“Surutun waye tayi haka?,shaheeda?,nooo….shaheeda nada hira,amma bata da surutu me yawa,salma?,laila?,hafsah?,maybe ya amsawa kansa da kansa yana tabe baki.

   Sanda ya fito ya taddata da jabir,da yake shi din sarkin yara ne ya biye mata sosai sunata sabgarsu,sai ya juya ya buda walking wardrobe dinsa ya shiga yana duba kayan da zai saka,kafin ya futo sun fita,sai ya fasa shirin fitar da yayi niyya,ya saka boxer dinsa kawai ba tare daya nema ko singlet ba,turarukansa ya fesa,sannan ya shafe lallausan baqin gashin dake cike aqirjinsa wani irin azababben oil perfume,yabi lafiyar gadonsa ya kwanta,bayan ya ragewa dakin haske ta hanyar sauke duka labulayen dakin,ya kuma kashe duka fitilun dakin.

      Bacci yayi sosai mai wani irin nauyi da dadi wanda ya jima baiyi irinsa ba,knocking da ya dinga ji sama sama cikin barcinsa ya sanyashi bude kyawawan idanunsa da suka qara girma saboda bacci,yadan mutstsukasu kadan,sannan ya ture lallausan duvet din daya rufe jikinsa dashi,ya zuro qafafunsa qasa yana miqewa,ya isa qofar ya bude.

    Jabir ne dauke da amna,kwalliyar jikinsa ta bambanta data dazun

“Wanne irin bacci kake?,ko a masallaci ban ganka ba”

“What?” Ya fada calmly,ya aza idanunsa ga agogo,sai yaga har bakwai tayi,a hanzarce ya saki handle din qofar ya shige toilet don ya daura alwala.

     "Na shirya zan fita mukaci karo da abbi yana dawowa,yace na gaya maka yanason ganinmu after isha prayer" kai kawai ya gyada masa,yana budewa amna hannunsa,ta taho da hanzari tana ci gaba da zuba masa surutunta,tare da bashi labarin inda sukaje dazun,sai jabir ya miqe ya fita ya basu waje.

     Yana shirin fita sallar isha din hisham ya shigo,cikin girmamawa ya gaidashi,ya amsa masa yana sanya qaramar hular tashi ka fiya naci saman sumarsa

“Ina kaje duka yau?” Kansa yadan shafa

“Ina da patient ne yau a asibiti da yawa da zan gani,so bayan kuma na gama dasu na wuce wajen gidan yaa jabir,na sallami companyn da suka zuba home decor na gidan” kansa ya gyada kawai,hisham din ya daukar masa abun sallah suka fito zuwa masallacin suna taba hira kadan kadan.

     Sai daya sake komawa ya duba ammansa,sannan ya wuce sassan anni,ya nema abinci wajen baba tabawa,wadda dama tun da can gurinta ko wajen ammansa yake cin abinci duk gidan,to sassan amman nasa yaga ya soma cinkoso,bazai iya tsayawa karbar komai na sassan ba,don bashi da tabbacin amman itace ta girka duk abinda za'a bashin.

     Yana ankare da yadda annin keta faman cin magani,sai shima ya basar kamar bai gani ba,ya zauna sosai hankali kwance yana cin abincinsa,cokali daya bakinsa,cokali daya bakin amna hira,duk tabi ta cikashi da zancen adda maimoon,kome yayi mata sai tace 'haka adda maimoon takemin'.

       Yana gamawa cikin sa'a yaji shigowa abbi,don haka ya miqe yana dauke da amna

“Kaje ka dawo,kazo muyi lissafin kudin kayan lefen da maama ta ranta maka ka zube mata abunta”

“lefe?,lefen wa?”

“Au da tattabaru kayi zaton za’a aura maka?,ko kuma babyn roba na wasan yara?,’ya’ya ne kamar kowa masu gata,ehe” anni ta maida masa amsa sannan ta fuske,sai kawai ya juya baice da ita komai ba ya fice,yana jin haushi yana sake cika masa zuciya.

     Da sallama ya shiga katafaren falon dr marwan khalid akko,can ya hangesu saman dining shi da jabiru,da alama zamansu kenan,yayi masa izinin ya qaraso,yana jawo kujerar sake daura dashi hadi da nuna amna yace ta zauna,tayi daraf kuwa fa haye ta fara masa surutun nata,har sai da ja'afar yace cikin lallausan muryarsa,very calm

“Amnee,pls….keep quiet” narai narai tayi da idanunta,don bata gama bawa daddy dr kamar yadda take kiran abbi ba labarin da take bashi,to amma ita kanta duba daya uban nata yake mata take laushi,dole tayi shuru,ta fara saka yatsanta tana dangwalan romon pepper soup din kifi da aka yiwa abbi.

       A sannan ya samu suka gaisa da abbi din,ya musu maraba,sannan ya tura masa warmers din yace ya diba abinci yaci

“Am full abbi,yanzu na gama ci wajen anni”

“Yayi kyau” yace yana ci gaba da cin abincinsa,sai dinning din yayi shuru,kasancewar dabi’ar abbi din,ba kasafai yake cin abinci kuma yana magana ba,har sai ya kammala,shurun da ya sanya ja’afar ciro wayarsa,yanajin abbin da jabir suna magana jefi jefi,wanda kusan duka kan tsare tsaren bikinsu ne.

    "Bismillahi" abbi ya fada yana zama saman kujerun falon,yayin da jabir da kuma ja'afar kowanne yayi matsugunni a qasa

“Kai jabir alhmdlh,mun gama duka maganar da zamuyi dakai…..am ja’afar,abinda yasa na kiraka” abbi ya fadi yana gyara zamansa sosai,gami da cire hularsa ya aje gefe

“Inason in tambayeka……wacece ta haifeni?” Girma maganar ta yiwa ja’afar sosai,har sai daya dago suka hada ido da abbi,kana ya maida idanunsa qasa

“Anni ce abbi”

“Ma sha Allah,to ban sani ba,ko ka manta ne,dani da umar da sagir da abbas da usman…..dukkaninmu anni ce ta haifemu,kuma qarqashin ikonta muke damu da dukka abinda muka mallaka,ba zanyi magana me tsaho ba,saboda nasan kasan matsayinta a wajenmu,hatta da mahaifiyarka zabin anni ce idan baki sani ba,shi yasa ta zamto ta musamman a wajena,na kuma yi dacen da maza dubu basuyi ba,dukka hukuncin da anni ta yanke a kanka yatabbata,kuma ba komai bane ya janyo hakan ba ina da.imanin qauna ce da kuma damuwa da halin da kake ciki,Allah yayi maka wata iriyar zuciya data banbamta data kowa,amma ka sani,jajircewa da karbar al’amura a yadda sukazo suna iya kawo sauyi,hakanan lokaci yana iya warkar da kowanne irin ciwo komai girmansa,duk wani abu da zakayi a yanzu akan aurenka shizai nuna dai dai matsayin anni a wajeka,idan ka wulaqantata ko ka watsa mata qasa a idanu to ni ubanka marwan ka yiwa haka,idan ka karba abun da kima da mutunci,ka kuma riqeshi da daraja to ni ubanka marwanu ka mutunta,saboda haka zabi ya rage naka,dan halak dai shike rama halacci,anni kuwa halacci tayi maka ba butulci ba,zanga dame zaka sakawa mahaifiyata”.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button