DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

.[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 1-5

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Fit…fit…Motoci ne suke faman hucewa A bak’in titi sanadiyar ruwa da ak’eyi. Wata budurwar yarinya ce k’e faman zanbada sauri har takai bakin wane gate, Nan ta tura A hankali saka kafarta da zatayi zuwa cikin gidan sai kuwa ji tayi an dak’a mata tsawa wacce sai da littafin hannun ta suka fad’i….

    ” Kee yasmin??? Cewar matashin saurayin nan!
   
     ” cikin tsoro da kuka tace kayi hakuri yaaa…

      ” Idiot kawai kalli ki sai kace almajira uban ina kuma kika tsaya…

   “Cikin hawayen da batasan dashi ba tace kayi hakuri wallahi lesson na tsaya…ta kalli jikinta da gaba daya ruwa ya jik’ata….

    ” Wani mugun tsaki yajaaa sannan ya nunata da hannu ..Gashi yanzu na makara sai shigen son makarantar tsiya babu abunda kikasani to bari kiji a sannu sai kin daina makarantar sai dai kidinga wankau…

    ” fuskar ta cike da damuwa tana shiga tsakar gidan sai tayi karo da dr cikin hanzari tayi baya tana danAllah kayi Hakuri wallhi bansani ba shiyasa…

    ” Murmushi yayi yace yasmin sarkin tsoro,can kuma yace yaya akai ruwa ya zaneki???

    ” Shiru tayi hawaye na bin fuskarta babu ta yadda zatace masa su abida ne sukace bazata hau musu mota ba..

    ” Ki daina kuka kinji yasmin kinga kinfara zama ‘yan mata kada ayimiki dariya kije ki canja kaya kinji idan nadawo zanbiyo dak’in mama kinji?

    ” Har cikin ranta tanajin dadin kalaman dr Amma kuma k’annan sa basa sonta kwata kwata…

    ” Wayar sa ce ke faman ringing cikin k’idan my love! Cikin nutsuwa ya dauka tare da fad’in Assalamu alaiki!..

    ” Cikin wata lausassar muryar ta tace bak’asona dr sageer yau 3days baka kirani ba sai dai kullum na kirawo ka? Ta saka kuka..

   ” Haba Ramlat menene abin kuka to bayan kinfi kowa sanin ina mutukar sonki!..

    ” Amma kullum kake nunamin aikin ka yafini mahimmanci gaskiya ni gwara ayi auren a huta wannan soyayyar taka kada ta salwanta ni…

    ” Dariya yayi yace oyaa to kiyi dariya naji!..

    ” Dariya tasaka sannan tace bari naje hajiya na kirana mayi magana anjima..

   ” Badamuwa ramlat ki kula da kanki kinji?

   ” i love u my doctor!!!

” baby same..cikin fara’a ya katse wayar tare da shiga cikin motarsa yana ‘yar dariya..

   
  Juya wa yak’eyi akan laushashiyar kujerar sa cikin sanyin office ya K’alli halifa yace kasan me bro??

   ” inajinka?

” yasmin din mama ina bala’in son yarinyar nan naso aci ta isa aure da kawai sai dai nafara neman auren ta….

     ” Halifa ne ya ajiye wayar hannun sa yace Doctor sageer kenan ka fiye barkwanci wallahi!!! Hahaha in banda idonka ya rufe ina kai ina yasmin a jss 3 fa take kai kuma kana babban likita mai aji wanda duniya tasan da zaman sa…Kuma yaudarar barister ramlat zakayi ???

   ”  Kai Abokina nagartar mace ake dubawa ba kyau ba, addinin yasmin ko mu da muke manya iya abunda mukeyi kenan,ga nutsuwa kalmar hakuri ta aure bak’inta duk gidan nan private school sukeyi amma baffa dan bashida kudi babu wanda yace bari yasaka yasmin a irin makarantar yaransa sai a gawamnati ya sakata kuma bata taba damuwa ba… maganar ramlat kuwa ka ajiyeta gefe!!!

    ” Tabbas hakane daman ai ka guji wanda kayiwa alheri…

    ” Let talk later ina da cs yanzu…

    ” To Dr see u later…

Yasmin yasmin yasmin bakyajina ne??

   ” Baffa sallah nakeyi…

” yauwa yarinyar kirki inafatan mahaifiyar ki tagaya miki sak’ona???

     ” A’a bata gayamin ba..

  ” To yasmin ke yarinya ce mai tarbiya kinga kuma bani da wata d’iya sama dake yar uwarki tayi nisa tana aure a benin kullum tunani na akan naga kinyi karatu ne…

    ” Cikin murmushi tace baffa kadaina damuwa dani wallahi banda wata matsala kai dai kacigaba da yimin addua…

    ” Yasmin inason zan kaiki boarding nasamu kudi Akallah wanda har kigama zan iya biya zuwa litinin sai ki shirya d’an Alhaji sule da yaranshi zaku tafi…

    ” Toh baffa Allah yakara budi nagode zanyi yadda kace…

     ” Dak’in mama tashiga ta rungumeta tana kuka dagota tayi tace daina kuka auta babu yadda banyi da mahaifinki ya kyali k’i agida ba,…

    ” Mama banason nabarki, ke daya duk gidannan basason mu kar susaka miki damuwa…

    ” Dariya tasaka tace haba auta babu mai samin damuwa kikwantar da hankalin ki kinji…

    ” Tohm bari naji gurin Anty zulai…

     ” Tunda tafito maryam ke faman hararar ta har tazo hucewa …

     ” Sannu da gida maryam ya makaranta…

    ” bansaniba ‘yar talakawa kudin makaranta ma ubanki yakasa biya miki haka zaku kari ai sai dai talauci ya kashe ku…

    ” Adaidai lokacin dr sageer yayi parking motarsa maganar data duk’i kunnan sa shine baban ki ma sai mun sa an koreshi a gadi…

     ” Yasmin ce tace Ai shi arzuki bako ne wanda baizo masa ba shine bai san saba wanda kuwa yazo masa to yasan zai kari, kuma duk iskancin ki kada ki kara saka iyayena tunda naga ke islamiyar taki bata amfana miki da komai ba, banza mara hankali kawai…

    ” wani dadi yaji ashe yasmin ta iya fada lallai…

    ” Maryam ce ta wanka mata mari wanda sai da dr yajiyo…

  ” Sai da ya kifa mata mari har guda 3 sannan yace baki da kunya ke?? to nakara ganin kin zagi yasmin Allah sai nayi miki illah shige kibani guri nonsense kawai…

     ” Kuka tasaka ta shige tana wallahi sai na gayawa mamee…

     ” Hannun yasmin dr ya riko yace yi hakuri ‘yar kanwata sannan yasa hannun sa ya goge mata hawayen fuskarta sannan yace muji nasiyo miki laptop saboda naga kina kokari a makaranta…

   ” A’a ni kabarshi nagode sannan ta shige gurinsu…

   ” yajima yana kallonta sannan ya tafi ….

  
  Kasancewa yau litinin yasmin ta shirya domin tafiya boarding sai kuka takeyi har suka tafi itada baffa mama sai addua takeyi mata…

   ” yau da daddare dr sageer yace mama ina auta ne??

   ” Auta tayi makaranta kwana ai..

  Boarding??? Why aka kaita haba mama..

    ” kayi hankali kada baffa yaji…

   ” Fita yayi cike da damuwa zuciyarsa sai zugi takeyi masa gashi ko zai mutu baffa ba zai kaishi makarantar ba…!!!yanzu yaya zanyi da kaunar yasmin???

ASALIN SU…

Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…
  
  Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…

    i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS

   GOD BLESS YOU OLL….

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 5-10

DOCTOR
SAGEER

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button