GURBIN IDO

GURBIN IDO 27-30

Shi daya ne cikin motar sai driver kamar yadda jabir ya tsara hakan ba tare dashi ya sani ba,zaman da yayi cikin motar ya yishi ne yana jiran fitowar jabir da yace yayi mantuwa a inda suka zauna,duba daya zakayi masa kasan cewa ango ne shidin zammm,yayi wani irin kyau na musamman cikin wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta lashe maqudan kudade tun daga wajen siyota har ya zuwa dinkin da aka yi mata,aikin hannu me matuqar kyau tsari da kuma tsada,takalmin sauciki kalar dark blue sosai daketa daukar idanu saboda sabunta kyau da kuma tsafta yana aje gefe,qafafunsa babu komai sai sock,gefensa ya fidda babbar rigar ya ajjye,a samanta ya cire hularsa kalar dark dark blue da ratsin light mai wani irin walqiya da daukar idanu ya ajjiyr hade da babbar rigar,hatta da links din hannun rigar gold color ya cireshi,ya nade hannun rigar zuwa gwiwar hannunsa,gargasarsa dame kwance luf ta bayyana sosai.

Wata magazine data wallafa sunayen fitattu kuma manyan kamfanunuwan gine gine a satin yake dubawa,kamfaninsu shine yazo a jeri na biyu,duba bayanan yake,amma can tsakiyar qirjinsa wani irin nauyi ne dake cunkushe a cikinsa,ranar ta yau gaba daya tazo masa ne kamar cikin mafarkai,tunda ya auri shaheeda kuma mutuwa ta rabasu bai taba tsammanin akwai rana irin wannan da zata zo ba,dukka wannan abun yanata qoqarin yaqi da abinda yakeji cikin zuciyarsa ne,amma a yau din,babu wadda ke ziyartar zuciya da kuma tunaninsa sai shadeedan,yana tuna rana irin ta yau cikin rayuwarsu data kafa masa tarihin da bazai gogu ba har abada.

Haske ne kadan ya bayyana a motar bayan an bude murfin motar,yana shirin daga kansa ga zatonsa jabir ne,sai yaji muryar mata suna fadin

“Shiga da bismillah,Allah yasa kin tafi a sa’a” wani abu ya tsaya masa a wuya sanda take shigowa motar a hankali,tana gama zama kuma aka maida murfin motar aka rufe,sai yaji driver yaja ya soma tafiya.

    Shuru ne ha ziyarci motar,babu wani motsi ko kadan a cikinta illa motsin injina dake aikinsu can qasa,cikin jikinta take jin sauyin waje da yanayi tabbas ya fara daga wannan lokacin,duk da bata iya ganin komai clearly amma tasan tabbas ba ita kadai bace cikin motar.

   Hannunsa ya zura a aljihun rigarsa ya fiddo wayarsa yanata qoqarin hadiye bacin ransa,shi jabirun zai rainama wayo?,yana nufin shi da ita zasuyi tafiya har ta wadannan awannin a mota guda don ya rainama kansa hankali?, numbers dinsa ya nema ya kuma kirashi,bugu biyu ya daga

“Jabir” ya ambata da wani irin sound dake nuna zallar bacin rai,saidai kuma ba wani da qarfi yayi maganar ba

    Lumshe idanun

ta maimunatu dake qudundune cikin yalwataccen mayafin da aka rufa mata har ka
tayi,bugun zuciyarta dake qara bugu take qoqarin saitawa,sautin muryar ya doki kwanyarta,tamkar a cikin kunnuwanta aka furta sautin kalmar jabir din,saita hade jikinta waje daya sosai,tana jin takalminta ya zame daga qafarta,amma babu damar ta motsa bare ta maidashi,hakanan kawai takejin wani irin tsoro yana ratsata,tabbas wannan shine mutumin daya zama mijinta a yau.

       "Kada kace komai,don muna tare dasu abbi,ga motarmu nan tasowa,wataqil zamu tsaya a hanya mu kwana saboda nisan tafiyar,please i beg you, don't misbehave,ka dorar da farincikin dasu abbi suka samu a yau din" magiyar jabir ta yau ta tabashi,don haka baice komai ba,amma hakan bai hanashi jan tsaki ba bayan ya kashe wayar

“Stop the car solomon” ya fada da tattausar husky voice dinsa

“Okay sir” ya amsa masa cikin girmamawa,sannan ya gangara gefan hanya ya tsaya.

30

 Ko sau daya bacci ko gyangyadi basuyi nasarar fusgarta ba,hakanan ko qwaqwaran motsi batayi tsahon a wannin da suka dauka suna tafiya,hakazalika motar haka ta kasance shuru,ba zata ce ga ainihin abinda yake faruwa cikin motar ba,sai daga bisani ne tadan janye mayafin dake kanta kadan saboda ta samu damar kallon gefan hanyoyin da suke wucewa da mugun gudu.

      Taraba suka wuce kai tsaye saboda su raba tsahon tafiyar,uwa uba kuma yammaci tayi lis,babu security ace sunyi tafiyar dare,don haka suka yanke sauka a wani hotel dake kan babbar hanyar da zata sadasu da gombe,kafin su iso ma tuni jabir yayi booking dakuna,don haka suna isa kowa key na dakinsu aka bashi.

      Itakam tana zaune cikin motar,har zuwa sanda anty maama ta qaraso ta fiddota,ran anty maaman cike da haushin ja'afar din,ta yaya sunsha wannan doguwar tafiyar xai fita yabar diyar mutane cikin mota?.

        Yana tsaye a tsakiyar dakin yana amsa waya sanda anty maama tayi knocking,ya qarasa bakin qofar ya murza handle din ya bude mata ba tare da ya tsaya tambayar waye ba,kana yaja da baya yana ci gaba da amsa wayar.

         Bakin madaidaicin gadon dake shimfide da farin lallausan bedsheet,tadan duqa kadan dai dai kunnuwan maimunatun,ta yadda ita kadai zataji abinda take gaya mata

“Ki saki jikinki da mijinki,ki samu kiyi wanka da brush kafin ki kwanta,zan ciro miki wasu kayayyaki cikin akwatinki za’a miqo miki,ki saki jiki kinji ko?” A hankali maimunatu da kanta yake a duqe ta gyada kan nata,tana jin zuciyarta na wani irin bugawa,a tsahon shekarunta na goma sha shida tunda take bata taba kebewa da wani d’a namiji ba a daki daya kamar haka,balle har ta kaisu da kwana kamar haka,yau gashi za’a fita a barta da wani,wanda yake amsa sunan miji a gareta.

     Juyawa anty maama tayi ga ja'afar wanda har yanzu bai gama wayar ba,sai ta kada kanta ta fice a dakin,qarar rufe qofar dakin ya sanyashi waiwayowa,don bai lura dawa suka shigo ba,ya zaci tazo wajenshi ne zasuyi wata maganar,kuma sai yaji ta fice ba tare da tace komai ba,abinda ya sanyashi juyowa kenan.

     Cikin mamaki idanuwansa suka sauka ga maimunatun,kawo masa ita sukayi kenan?,lallai dai sai sun qure haqurinsa da juriyar da yaketa azawa ransa?,sai ya dauke idanunsa yana sallama da wanda suke wayar dashi,ya yanke kiran yana neman number jabir.

      Bugu daya ya daga,muryarsa cike da wani irin nauyi yace

“Baku da wani extra dakin?”

“For who?” Ya tambayeshi kai tsaye,don dama yasan dole ko yaya sai ya nuna turjiya

“Ban sani ba,am asking you ne,it’s simple question,just answer me bawai ka tsaya tuhuma na ba”

“Oh…oh sorry, let me ask abbi first,but dakin kadan ya muku ne?” Ya tambaya cikin zolaya izgili da neman fada,haushi da takaici ya sanya ja’afar jan dogon tsaki kana ya tsinke kiran,wai dole sai jabir ya sanyashi dogon magana ne?,baisan abinda yakeji bane?. Sai ya cilla wayar saman madubu,sannan ya jawo kujerar gaban mudubi ya zauna a kai.

     A hankali ya duqa yana zare takalmin qafarsa,idanunsa suka kan farar qafarta dake dauke da dogayen yatsu da suka sha jan lalle wanda ya sake qawata qafan,ya kuma zame mata ado sosai,sai ya janye idanuwansa,qafafun are tiny,abinda yake alamta masa tana da qarancin shekaru kenan?,haka kawai sai yaji zuciyarsa na darsa masa son ganinta da tantance wacece ita?,ta yaya zasu dubi kamarsa suce zasu aura masa yarinya kamar haka?,sakanni qalilan zuciyarsa ta kacame da wasuwasin yarinyar ce ko kuma hasashe ne irin nasa?.

     Miqewa yayi yana sake jan tsaki duk a qoqarinsa nason mantawa da wannan wasuwasin da yake azalzalarsa a rai,ya taka zuwa qofar bandaki bayan ya kalli agogo yaga lokacin sallar magrib yadan gota kadan,ya daura alwala,ya sake fitowa yana sauke hannun rigarsa daya nannade kafin fara alwalar,yana son ce mata taje tayi alwala suyi sallah amma kuma ya rasa ta yadda zai gaya mata,bawai kuma baisan yadda zaice mata bane,a'ah,kawai qyashin maganar yakeji,har ya fidda abun sallah ya shinfida tana zaune,sai daya sake jan tsakin nan nasa dai,wanda ya kuma sanya maimunatu faduwar gaba ta kuma rintse idanunta kamar kowanne lokaci idan yayi tsakin,don tana jin tsakin ne har tsakiyar kwanyarta,faduwar gabanta kuma nada nasaba da muryar dake mata kama da wata firgitacciyar murya data taba ji shekarun baya da suka wuce

“Kiyi alwala kizo” ya fadi mata yana jona qaraman kettle dake a gefansa.

A hankali ta miqe,ta kuma dan ja mayafin nata baya kadan,sannan ta wuce zuwa bandakin.

Gaban madubi ta tsaya bayan ta yaye lullubin kanta gaba daya,tana sakin wata ajiyar zuciya me nauyi gami da kallon fuskarta,wadda lallausan gashinta me azabar santsi da yasha gyara daga wajen yakumbo saratu ya fito kadan ta gaban dankwalin nata,saita debe ruwan dake zuba daga famfo ta fara alwalar,tana yi tana kallon fuskarta a madubi,zuciyarta nata mata saqa abubuwa masu yawa harta gama,ta maida dankwalinta da mayafinta ta fito,ta kuma tsaya a inda ya mata nuni suka tada sallar.

Yadda yake sallar cike da nutsuwa yayi matuqar burgeta,ko banza alamune dake nuni da sanin addininsa.

A hankali ya sallame,idanunsa suka sake sauka akan dogayen hannayenta suma da suka jiqu da jan lallae cikin ado me ban sha’awa,hakanan ya samu kansa da juyowa gaba daya yana fuskantarta,idanunsa suka sauka gaba daya a kanta,ta tanqwashe qafafunta sosai tana zaune,sai ya ganta ‘yar qarama a gabansa,tazarar dake tsakaninsu ba mai yawa bace

Shuru ne ya baquncin dakin,numfashin kowannensu yana fita tare sa tulin tunanin dake zuciyar kowannensu,yaci gaba da zama a haka yana fuskantarta tare da wassafa me zayace da ita?,duk sanda yadan dubi sashen da take zaune sai yaji wani abu ya tokare masa wuya,yanzun haka bayan ita akwai wata daban dake gombe tana jiransa?,for god sake anni zatayi masa haka ne wai?.

Kamar wadanda aka umarta daga shi har ita kowanne ya daga kanshi zuwa ga dan uwansa,take fuskarsu ta hade waje daya kamar yadda idanuwansu suka cudanya da juna,fari qal din idanuwan nan nata da baqaqen qwayar idanunta masu digon zaiba jiki,kyakkyawan idanunwansa dake da wani irin shape,tare da wani irin maganadisu dake cike da zallar kwarjini.

Kusan lokaci daya wani abu ya daki zuciyar kowannensu,wanda ta bangaren maimunatu ba komai bane face wani irin tsoro razani da kuma firgici da ya kusa tafiya da numfashinta,cak ta tsaya da zuqar iska zuwa huhunta na wucin gadi,hatta da ja’afar din ya karanci hakan,yayin da shi kuma zallar mamakin qananun shekarun da take dashi hadi da kamanni da tayi masa da wata suka ratsashi.

Cikin jarumta ta zuqi wani dogon numfashi ta kaiwa hunhunta cikin wasu sakanni masu mugun sauri,abinda ya tallafa mata numfashinta ya dawo da aiki,saita lumshe idanunta da kyau tana shaqar numfashin da qyar,tana kuma jin yadda zuciyarta ke mugun bugawa da sauri kamar zata tsinke daga inda take ta fito.

“Hey” ya fadi cikin mamakin yadda take wasu abubuwa kamar wadda taga giftawar mutuwarta a gabanta,maimakon maganar tasa ta taimaka wajen bude idanuwanta ko samun nutsuwarta……a’ah,sai ta sake razana,saboda muryar ta sake tabbatar mata da shi dinne dai,shine dai wannan mutumin,take jikinta ya dauki rawa,zuciyarta taci gaba da kadawa a tsakanin qirjinta,sai tayi wuf zata tashi jikinta na kakkarwa kamar wadda azababben zazzabi ya rufe.

Caraf ya damqi tsintsiyar hannunsa cike da haushinta da mamakin firgitar da tayi,riqon da yayi mata ya sanyata sakin kuka babu shiri tana dubansa,mamaki ya cikashi qwarai,sai ya janyota ta koma ta zauna a inda ta tashi.

Sosai hankalinta ya kuma tashi,ta hade jikinta waje daya hawaye naci gaba da bin kuncinta,ta yaya zata manta da wannan fuskar?,yaya zata manta dashi,mutumin da ya kusan sanadin cirewar qwayar idanunta saboda marin da ya zabga mata duka akan dabbobinta?,mutumin da ya mata barazana da kakkausar murya,wanda tun daga ranar bata sake ganinsa ba,saidai duk sanda taga mota,ko taga wani abu da yayi kama da mari saita tunda da abinda yayi mata,sau tari takan shafa kuncinta idan ta tuna da wancan lokacin,mutumin da razanata matuqa,ta tsani taba,ta kuma tsani me shanta,sai gashi ya fesar da hayaqinta saman fuskarta,abinda ya kusan haddasa mata daukewar numfashi,wanda ya aikata mata wannan duka shine zaune yanzu a gabanta,shine kuma mijinta?.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button