GURBIN IDO

GURBIN IDO 27-30

       Maganganu ne gajeru marasa dogon zango,saidai nauyinsu yafi qarfin wani ma'auni ya iya gwadasu,shigen shigen magana irin wannan bata taba hadashi da mahaifinsa ba sai a wannan karon,nauyin maganganun da har dr ta sallamesu basu bar dukan sassan jikinsa ba,har sun kusa fita ya sake kiransa

“Ka shirya daga yau zuwa gobe,kaje gidan minister ka gana da unaisa”

“Unisa?” Ya fada cikin ransa,yana jin he knew the owner of the name UNAISA,to amma a ina?, somewhere….. somewhere,for sure,indai gidan minister ne,bu he may not remember ainihin inda yasan ta din.

   Dukka wannan shi da zuciyarsa yake wannan tadin,wanda tuni ya riga yace da abbi "To" yabi kuma bayan jabir sun fice.

“Ya?,yau din zamu wuce?,don inason naje naga fatima gaskiya,i missed her badly” yana jin iya maganarsa ta yau ta qare,so saboda haka bashi da abinda zai cewa jabir din,saidai ya masa wani kallo,yana shirin yi gaba jabir din yasha gabanshi

“Shawara guda daya J.pls and pls,kayi qoqarin bin maganar abbi,indai har kai din masoyin shaheeda ne da gaske,na tabbatar da tana raye itace mutum ta farko da zata fara tursasaka kabi abinda dukka magabatanka suke so,for the first and last time may be da sukeso kayi musu wani abu cikin rayuwarka,we will see if you can do it” jabir yakai qarshen maganar yana duba yanayin ja’afar,duk da cewa ya bashi baya,kamar yadda ya zata din,baice masa komai ba sai gaba da yayi ya barshi a wajen.

Sassansu ya yanke ya koma kawai,saboda kansa gaba daya ya gama daukan zafi,tako.ina abbi ya gama daureshi,tun jabir baice komai ba dama ya riga daya yankema ransa dole ya tsaya ya fuskanci komai,zaiyi duk yadda abbi da anni keso for the sake of them.

Ya jima a haka kafin yayi qoqarin dai daita nutsuwarsa,ya daga waya ya turama hisham tex kan ya kawo masa amna,ba jimawa sai gashi da ita,ya dire masa ita ya juya.

Jaka guda ta kayan wasan daya jima yana siya ya tura mata,duk sanda ya fita yaga wani abun wasa saiya tuna da ita,sai kuma ya siya ya ajjiye,murna ta ishi amna,ta dauki wancan ta ajjiye,ta dauko wannan ta ajjiye,komai sai data nuna masa,kamar ba shi ya siyo ba.

A gaba ya sanyata yana kallo kawai,iya wannan farincikin nasa ya sauke kaso mai yawa daga cikin nashi bacin ran,abu na qarshe da yarinyar ta fada shi ya tashi zaman nasu,ya kuma dawo da mutuwar shaheeda da twin sister dinta amra danya a ransu duka su biyun,kewa da maraicin shaheedan ya kamasu

“Daddy…..mommy taqi dawowa,taqi kawomin amra muyi wasa,daddy yaushe zasu dawo?,zanyi fushi fa daddy” cikin jikinsa ya rungumeta,yana shafan gadon bayanta

“Kada kiyi fushi,kita musu addu’a kinji?,zamu hadu dasu in sha Allah sooner or later”ya fada yana qoqarin hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya.

      Ta jima a haka kwance a jikinsa,yana jin yanayin saukar numfashinta da yadda ta qara nauyi a jikinsa ya tabbatar tayi bacci,sai ya miqe sabe da ita,daya hannun nasa kuma yana riqe da jakar kayan wasanta yayi sassan ammansa da ita.

   Yana shiga tana shigowa itama falon daga ainihin qofar baya na sassan nata da zata sadaka da masaukin baqi na gidan,ita da masu aikinta su biyu,lili da laraba,suna dauke da jibga jibgan duvet da ana fiddosu yawanci a lokacin taro irin wannan musamman saboda baqin.

         Jikinta sanye da Egyptian hijab daya saukar mata har qasa,duk da dare ne amma akwai eye glasses tare da ita,wanda takanyi amfani dashi lokaci lokaci idan taji bata jin dadin idanuwanta.

       "Karbeta lili,ki kaimin ita dakina,idan kin shiga ki rage qarfin acn nan,don naji kaman mura nason kamata" a ladabce ta amsa,ta dauki amna da ja'afar ya shimfide mata saman kujera ta wuce ciki

“Manya” ta kirayeshi da sunan da takan kirashi dashi don ba kasafai zakaji ta kirayi sunan nasa kai tsaye ba

“Zauna muyi magana” kamar yadda ta umarceshi haka yayi,ya koma ya zauna din yana bata hankalinsa

“Kayimin wata alfarma man” sosai yake duban amman tasa,abinda yasa ta fahimci tambaya yakeson yi kan alfarmar data ambata

“Don Allah na roqeka,ka daure ka karba qaddararka a duk yadda tazo maka,kada kayi wani abu da kasan cewa ba dai dai bane,ka riqe amanar da aka baka bisa gaskiya da na sanka da ita,don Allah”

“Ku daina roqata hakanan amma,kunfi qarfin haka a wajena” ya amsa mata yana bata assurance din haka ta cikin qwayar idanunsa,ta san yana da qoqarin bin umarnin na sama dashi daman,saidai sanin halinsa yasanya mata shakku kadan,amma a yanzun hankalinta ya gama kwanciya gaba daya

“Allah yayi ma rayuwarku albarka,shikenan sai da safe”

A daren gaba daya ya gama lissafa yadda zai tafi da komai,yadda zaibi umarnin mahaifansa ta gefe guda ba tare da rayukansu sun baci ba,hakanan ba tare kuma da matan da aketa qoqarin liqa masa sun dameshi ba,don haka a washegari bayan ya shirya ya fito,ya nema ma’aikata daga cikin kamfaninsa,ya tsara musu abinda yakeso.

Cikin gidaje hudu da yake dasu ya zaba daya,wanda yake dan nesa kadan da nasu gidan,yasa aka hau aikinsa baji babu gani,don dama gidan kusan an gama komai nasa,fenti da saka qwayaye da sauran kayan qawata gidanne kadai ya rage,abinda yasa yayi saurin yin hakan,don bayason abbi ko anni wani yace su zauna a ainihin gidansa dakegovernment house road,don yafi kusa da nan gidan nasu,gidane iya gida,wanda ya amsa sunansa,kuma ya ginashi ne musamman a sannan saboda shaheeda,a sanda ta haifa masa twins,ya zuba musu komai da komai,sanda zasu tashi zuwa gidan suturar jikinsu kawai suka dauka,kuma ko bayan rasuwar shaheedan babu abinda ya bari aka taba cikin gidan,hatta da suturarta,da anyi maganan kwasan wani abun sai a rasa kansa,sai aka yanke shawarar a jinkirta ko yana kan tsinin zafin mutuwar ne,saidai har kwanan gobe komai yana nan a muhallinsa,a baya cikin gidan yake rayuwarsa,saidai yadda yake dada komawa yasa anni ta yanke shawarar ya tattaro ya dawo gida cikin jama’a,a kulle wancan gidan ko za’a samu sauqin wasu al’amuran,an dan samu din,saidai babu abinda ya canza shaheeda daga zuciyarsa har kwanan gobe ita da amransa *SO BAYAN RAI*

Gidan daya zaba din gida ne sama dake da babbar haraba da zata iya daukan motoci goma,akwai balcony da zaka shiga wanda yake dauke da babban falo,hagu da dama na bangon falon qofofi ne guda biyu,kowacce qofa akwai babban falo hade da bedroom a cikinsa, kitchen daya ne wanda yake falon,saidai babba ne,babu wanda zai takura wani,hakanan side biyu gareshi,a falon akwai stairs da aka qawata da wasu irin makarai masu kyau,marbles ne zube har zuwa saman,inda zai sadaka shima da falo babba ne dakuna guda uku ne a saman kowanne manne da toilets dinsa,sai wani balcony din daga sama wanda zai baka daman ganin ainihin harabar gidan fetal,a qasan akwai spare din daki guda daya,sai dakunan baqi maza da na me gadi daga can wajen gidan.

Gidan yana da girma,don kowanne daki da falo babbane qwarai,hakanan yadda aka tsara ginin ya bada sha:awa ainun,saidai jabir da ya gani yaga gazawar ja:afar din,a matsayin da Allah ya bashi,duba da gidan da zai dauko unaisa

“Idan gidan bai mata ba saita fasa dani ta zaba wani fine,iya abinda zan iya kenan” ya gayawa jabir,kamar shine unaisan.

Duka kudin anty maama na lefe ya tura mata abinta ba tare daya sake wani musu ba,hakanan dukka wata zirga zirga ta samarwa da baqinsu masauki tare dashi aka yita,saidai sau tari har suje su dawo ba zakaji yace kanzil ba,lokutta mafi yawa wayarsa na a hannunsa ne,cikin abokansu guda biyun da suketa zirga zirgan tare babu wanda ya kawo komai ransa,saboda sunsan wayeshi,captain j din haka nan dabi’arsa take sun sani tun ba yau ba,magana ko surutu shine assignment mai wahalar cinyewa da zaka hadashi dashi.

Sai daya qara kwana biyu sannan ya samu ya sukunin saka time na zuwanshi gidansu unaisa kamar yadda abbi yayi masa umarni,ganin yadda yake shiga cikin sabgogin yasa abbi bai tanka masa,don yana ganin sauyi muraran da kuma qoqarin bin umarni daga wajen ja’afar din.

A ranar yayi zamanshi a sassansu kamar bashi da plan na zuwa ko ina,tab ce saman cinyarsa yana duba wasu abubuwa,sanaye yake da bawin boxer wanda ya fidda ainihin qirar tsayayyun qafafunsa dake cike da tarin gargasa,jabir ya turo qofar dakin ya shigo,a shirye tsaf cikin shadda,sai yaja turus ya tsaya

“Me zan gani?,J baka duba agogo ne?”

“What happened?” Ya tambayeshi a nutse abinsa,kamar ma baisan meke faruwa ba

“You are very stubborn manya,me yasa kakeso ayita maimaita magana daya?,just simple instruction amma ka kasa bi” idanu ya watsa masa bayan ya kashe tab din

“Yaushe na gaya maka fasa zuwa na?”

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button