GURBIN IDO 27-30

Samun kansa yayi da zuba mata idanu,abinda ba al’adarsa bace,yana dubanta tare da son tuna inda ya santa,tsahon wasu daqiqu kwanyarsa ta dauko masa komai,bafullatanar yarinyar nan,daya jima yana tunawa bayan marin da ya dauke fuskarta dashi,ya jima yana murza hannunsa a lokacin cikin fushi da jin haushinta na yadda ta qarasa tunzura fusatacciyar zuciyarsa ya aikata mata abinda ba halayyarsa bane,fuskar da yakan tunata lokaci bayan lokaci saboda qarfin halinta da kuma yadda ta bashi haushi a sannan.
Ga mamakinsa sai yaji duk wani temper na zuciyarsa ya sauka daga kaso casa’in cikin dari,zuwa kaso arba’in ciki dari,ta yaya zai zauna da wannan yarinyar?,wadda gaba dayanta baifi ya haifeta ba inda ace auren qauye akayi masa?,ta yaya zai zauna da wannan bafulatanar rugar?,wadda ya tabbatar babu abinda ta sani,babu kuma abinda ta iya?,ya aureta yace ya auri me?,ta yaya ma duniya zata kalleta a matsayin matarsa?,wanne irin rigima ce wannan ta anni?, take kwanyaraa ta hasaso masa unaisa,yayi comparing nata da wannan,sam babu hadi,ko ita unaisar bata cika mizani da ma’auni ba,tayi masa girma da yawa,don shaheeda bata kai wadan nan shekarun ba har ta rasu,barema tun halittarsa shi mace bata taba burgeshi ba,shaheeda ce mace qwaya daya tallin tal da ya taba daga kai ya dubeta da wata ma’ana ta daban,itace macen data fara bude rayuwarsa,kuma sanda ta tashi tafiya…..yanajin ta hada da muqullin komai nashi tayi gaba dashi.
Cikin rai da zuciyarsa ya dinga jin yanzu zaiyi solving daya daga cikin matsalolin kamar yadda yake kallon maimuntu da unaisa a natsayin MATSALA kuma GURBIN IDANU ne kawai,wadanda baijin zasuyi ko suna da amfani ko wata rana ga mamallakinsu,wanda dasu da babu duk daya
“Relax” ya fada idanunsa a lumshe,yana zagaya lips dinsa da yatsun hannayensa
“Yamin shuru!” Ya sake fada a karo na biyu,ganin taci gaba da rera kukanta kamar ma bataji abinda yace ba,yadda ya buqata kuwa a wannan karon….sai ta fara hadiye kukan sannu sannu har ta samu nasarar tsaidashi.
Shuru ya sake ratsa dakin,tamkar bazaiyi magana ba,kafin daga bisani ya bude dukkanin idanunsa ya watsasu a kanta
“Kinsan menene aure?” Yayi tambayar with husky voice,wani irin abu ya ratsa mata tun daga saman kanta zuwa tafin qafafuwan maimunatu,saboda girma da nauyin da tambayar tayi mata,me zata ce masa?
“Kinsan me aure yake nufi?” Ba tare da tayi dogon nazari ba ta gyada kanta alamun eh,kasancewar ba mutum ce ita wadda ta iya qarya ba.
Wani miskilin qaramin murmushi ya sake
“Okay……yayi kyau,tell me menene aure?” Ya fada yana yin qasa da muyarsa,hadi da tsareta da idanunsa nasu nauyin kallo,duk da bashi take kallo ba amma sai da taji gaba daya ta rude ta kuma daburce
“Ehhnnnnn” ya fada da madaukakin sauti,sai ta shiga girgiza kai alamun a’ah,bata sani ba
“Qarya kike kenan da farko….. okay let me show you the real definition of marriage” ya fada with confidence,zuciyarsa na gaya masa that’s the only way da zai cimna gaci na abinda yakeson aiwatarwa,ba tare da yasan maimunatun was simple and peace maker ba,sai ya miqa hannu ya janyota cikin zafin nama daya sake tsoratata zuciyarsa na ingizashi,ya sanyata tsakiyar qirjinsa duk da yadda zuciyarsa ke qin hakan.
Fara yamutsata yayi,abinda yayi matuqar dukan hankalin maimunatu ya kuma kadata sosai,abinda tunda take makamancinsa bai taba faruwa da ita ba,mugun gigicewa tayi cikin tsoro da razani,ta sake sakin kuka tana riqe masa hannayensa da yakeson fara yawo dasu cikin sassan jikinta,sai ya tsaya cak numfashinsa na wani irin gudu,yana duban yadda ta riqe dukka hannayensa biyu cikin siraran tafin hannunta,jikinta na wani irin rawa kamar an kada mata gangi
“Bai kamata ba,baka kyauta ba” yaji can tsakiyar kansa zuciyarsa na gaya masa,bai musa ba,take zuciyarsa ta gamsu da cewa bai kyauta din ba,saidai kuma wannan ce hanya guda daya da zaiwa tufkar hanci,tunda baisan irinta ba yarinyar,abu daya ya sani game da ita,tsiwarsa da har ta iya buda baki tace masa Allah ya isar mata a wancan lokacin,yana jin this the only way out da zai dorata kan duk abinda ya tsarama zuciyarsa.
Saidai kash,yana shirin sakinta anty maama ta turo qofar riqe da jakar kayanta,abinda ta gani ya sanyata fadin
“Subhanallah” da sauri tana komawa da baya,abinda yaja hankalinsa,yayi hanzarin sakinta ya kuma miqe a nutse,ya isa bakin qofar dakin ya sake bude mata ita sosai,sannan ya juya zuwa bandaki bacin rai yana cinsa kan yadda ta gansu,yayi yaqinin abinda zaizo ranta daban,abinda zata rayama ranta yasha banban da abinda yake faruwa,ya tura qofar toilet din ya shige.
Gaban madubi ya tsaya yana duban fuskarsa,hannunsa yasa yana yamutsa sumarsa zuwa bayan kansa,yadan riqeta da qarfi yana jin haushin kansa da kansa,ta yaya zai riqe yarinyar cikin jikinsa har kamar haka?,sai yaja wani irin tsaki kamar zai cire harshensa,yana jin tsantsamin jikinsa dama hannayensa,duk da cewa babu abinda ke fita a jikinta sai lallausan qamshin turaren firdaus.
Wayarsa ya ciro ya turawa jabir tex kan ya shigo masa da kayan sawarsa,sannan ya ajjiye wayar,ya soma fidda kayan jikinsa yana jefarwa,ya daidaita ruwa me dumi sosai daga shower ya shiga ciki yana sabe jikinsa kamar zai cire fatar wajen.
Da wani irin nutsuwa dakiya da kuma tsare gida ya dawo dakin,bayan ya shirya cikin wata lallausar jallabiyya da aka yiwa aiki d wani gold zare mai kauri,idanunsa suka sauka a kanta,tana lafe a wani lungu dake daura da gadon,sai ya sake jan tsaki can qasan ransa,yana jin takaici na sake kamashi,baisan me anni ma ta dauki aure totally ba data hadashi da wannan.
Bai tsawaita magana da ita ba,cikin taqaitattun mintuna ya gama tsara mata dukkan wasu qa’idoji da dokoki da yakeso tabi da kuma zauna akai,ya riga daya sani a yanzun bai isa yace ya rabu da daya daga cikinsu ba ko ta yaya kuwa sukazo masa indai bada wani qwaqwaran dalili ba,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya,yana jin yayi maganin rabin matsalarsa,ya tabbatar a yanzun bashi da wani sauran case da ita wannan yarinyar,saura dayar,ya fuskanci itakam waccar kanta yana rawa sosai,zai kuma shata mata layi tsakaninta da rayuwarsa.
Fita yayi ya barta a dakin,bai dawo ba sai da bacci suka kama idanunsa,duvet din ya yayima ya koma saman kujera yayi kwanciyarsa,bayan ya kashe hasken dakin,bai wani jima sosai ba bacci ya daukeshi,don tunani da damuwar dake kansa a yanzun ta ragu sosai.
Kasa sakewa tayi cikin dakin,motsi kadan saita tuna abinda yayi mata dazun,abinda ke sake bata tsoro kenan,duk da maganganun da yayi mata dazun sun sake nuni da girman tazarar dake tsakaninsu,wanda zuciyarta tafi raya mata cewa gargadine ya sanya ya aikata mata hakan,bawai don ta isa ko tana da wani abu ba,babban shinge da layin daya gindaya tsakaninsu kawai ya sake tabbatar mata da cewa da gasken gangancin aka aikata na hadata aure dashi kamar yadda ya gaya matan,ita kanta daga dazu zuwa yanzu da kuma sanin data yi masa a baya ta sake tabbatarwa kanta tako ina yafi qarfinta,ya kuma yi mata fintikau,tun tana takure har gajiya tasa gabbanta suka saki,ta kuma zame da jikinta a nan qasa daura gadon,bacci mai nauyi ya fara fusgarta,zuciyarta cike fal da tsoronsa daya dasa mata a wannan rana.