GURBIN IDO

GURBIN IDO 31-35

“Yanzu har a miki aure cikin hutun nan amma koni ki kasa gayamin moon?,ashe yadda na daukeki daban yadda kika daukeni daban,na gode,na gode sosai” ta fadi tana miqewa daga gadon bayan ta ajjiye mata katinta.

     Da hanzari ta kamota tana dubanta

“Ni ba cikin hutun aka dauramin aure ba,da aurena na shigo school din nan” amsar tata ta bawa afra mamaki matuqa,ta kuma taimaka wajen sauke fushinta,mamaki ya maye gurbin hakan.

        Janta tayi suka zauna tare,sannan ta dubi afran

“Sai da nayi watanni da aure sannan na fara zuwa nan” a nutse ta warware ma afrah komai,babu wani abu data boye mata,don itama tana jinta da gasken gaske har cikin zuciyarta,asali ita bamai yawan magana da dogon surutu bane,kuma tun zamansu tare suka fuskanci ba kasafai hirar samari data aure take burgeta ba yasa basu fiya irin wannan hirar ba muddin tana cikinsu,hakan yasa babu wani abu da ya tado maganar bare su sani.

       "Captain ja'afar marwan akko?,shi na gani a rubuce,da gaske shine mijinki?" Afra ta fada wani murmushi na fita saman fuskarta,kai maimunatu ta jinjina mata

“Dama ance yayi aure,mata biyu,ashe harda aminiyata ta gobe a ciki, congratulations…..congratulations once again sister,kin ciri tuta,ke dashi kun tsinci dami a kala” ta qarashe maganar tana duban idanun maimunatu,fuskarta fal da murmushi,maganar ta bawa maimunatun mamaki,ta waro idanu tana duba afrah ba tare da tace komai ba,ita kuwa batayi qasa a gwiwa ba ta dora da

“Duk yadda zan fasalta miki kyanki haduwarki da kuma nutsuwarki ba zaki fahimta ba maimunatu,tunda a kanki ake magana,kina da dukkan wani qualities da nake da tabbacin babu namijin da zaisan kina dasu ya iya dauke kansa a gareki ki wucess,infact…….ba namiji ba,koni macen na gama yiwa brother na kamu,ashe J ya riga dsya qwamshe wannan rabon” takai qarshen maganar murmushinta na sake yawa zuwa dariya dariya,dole kuma ta dora murmushi kan fuskar maimunatun,tasan halin afrah sarai,duk da cews ba wai yaune ranar farko da ta fara ko suka fara kodata ba ita dasu ayman

“Well……abinda yasa nace ke kuma kin tsinci dami a kala?…..hmmmm….. captain ja’afar…….matashin da yake sanya razani da yawa a zukatan ‘yammata,matashin da ya sanya idanuwan ‘yammata da yawa zubda qwalla,matashin da ya sanya zukata da yawa cikin bege da qauna mai tarin yawa,ciki harda cousins dina su biyu,wanda har yau basu debe tsammani a kansa ba” ta qarashe tana sakin dariya,tare da tuna irin dambarwar da suka sha,tana cikin masu yi musu dariya kafin ta fahimci girman jarrabawar da suka fada,kafin ta fahimci waje ja’afar data fara yin hankali ta fara tausaya musu.

       Dubanta maimunatu takeyi kwanyarta na tafiya cikin nazari da tunani afran ta dora,saidai wannan karon cikin seriousness take maganar

“Qawa,kada kiyi wasa da damarki…..kada kuma ku tsaya kallon ruwa kwado yayi miki qafa,kina da dukkan komai da zakiyi wining a kansa da zuciyarsa,karki barwa kishiyarki waje ko fili ko kadan,kada kuma ki sake wadan nan alamomin rainin daga wajenta suci gaba da fitowa a kanki,ta yaya zaki sakar mata rayuwarki tayi yadda taga dama?,mijinki rayuwarki ne ko yaya kika gai ga qinsa,wannan zaiyi amfani ne kafin ki amsa sunan matarsa,duniya ta fara kallonki da sunan,amma bayan kin amsa din kuwa,baki da wani zabi daya wuce ki gyara komai,indai bakiyi hakan ba….baki kyautawa anni ba,sannan bata cancanci wannan tukuicin daga gareki ba” maganganun afra sun ma maimunatu nauyi a ka,ta saqa abubuwa masu yawa a zuciyar maimunatu wanda suka dinga yi mata kai kawo aka,saidai tana duba abin,tana duba yadda lamarin zai kasance,ba zasu fahimta bane cewa yadda suke kallon lamarin dashi kansa mutumin ba haka abun yake ba?.

      To sai da tayi mugun da gaske sannan ta yakice tunani me qarfi da ya kamata daga ranta,ta koma karatunta ka'in da na'in,itama afrah bata sake ce mata komai ba,saidai a fakaice take mata karatun yadda soyayya take,sau tari a gabanta take wayoyinta yanzu,ta daina kebewa kamar yadda takeyi a baya,wani lokaci saidai ta tashi ta bata waje,idan taga dama ta qyaleta,idan kuma bata so ba ta biyota nan ma ta addabeta.

*Tsararriyan books shelve,wadda ke dauke da tarin litattafai a jere cikin tsari da tsafta da kuma sanin makamar aiki,tsaye yake a gabanta,daya daga cikin qofofinta a bude,da alama wani littafi yake nema,hannunsa daya dauke da wani littafi daya nutsu qwarai yana dubashi shafi bayan shafi,yayin da daya hannun nasa kuma ke riqe da cup dauke da matsatsen ruwan tuffa da inibi,sanye yake da wasuSlim fit suit Korean design royal blue color,shigar da a duk sanda ya yita take masifan karbarsa,kamar dama anyi suits da blazers saboda shi ne,kallo daya zaka yiwa kwantacciyar fatarsa kasan cewa hutu da jin dadi sun ratsashi,duk da cewa babu cikakken hutun ba ma’ana a ruhinsa,saboda uban tulin tarin ayyuka da kullum yake jibgama kansa,duk don yayi keeping kansa busy,ya raba kansa kuma da dukka wani tunani da kuma damuwa.

       Fuskarsa nan mai cika da haiba da kwarjini tana nan a yadda take,babu faraa ko walwala sam kamar bashi daya bane a cikin qawataccen office din nasa ba,sumar kansa zuwa ta fuskarsa nata sheqi tare da fidda qamshin hair mist mai kwanatar da zuciya.

     Taku daya yayi zuwa baya kadan da qafafunsa dake sanye cikin wasu lafiyayyun baqaqen takalma,wanda zaka rantse da Allah ba'a fita waje dasu saboda yadda suke sheqi,babu alamun saukar qura a kansu,ya dan jingina da teburinsa yana furzar da iska daga bakinsa bayan yakai shafin qarshe,yana tuna sanda shaheeda ta bashi gift na littafin,sai ya dan rufe littafin kadan yana kulle idanuwansa na wasu sakanni,kullum kwanan duniya yana jin cewa ya rasa babban bango kuma majingina a rayuwarsa,tunda ya rasata kullunm rayuwarsa sake jigata takeyi,babu wani sassauci tako ina.

    Idanunsa ya buda a hankali sanda akayi yaji ana scanning key din office din nasa,qofar kuma ta bada qara alamun an budeta kenan,bai wani motsa ko kuma ya damu ba,saboda yasan duk duniya mutum daya ya bawa wannan damar wato jabir,shi dinne kuwa,ya sako kai cikin office din bakinsa dauke da sallama,hannunsa dauke da file yayin da idanunsa suke kan fuskar ja'afar,yayi kyau shima cikin tashi suit din da take kamanceceniya data ja'afar,ya qara haske da kuma qiba yayi fresh,alamun duk yadda yakeso haka take samuwa a gareshi.

     Bakinsa ya motsa yana amsa sallamar tasa,kana ya miqe tsaye sosai saman qafafunsa,ya sanya hannu a nutse ya maida littafin inda ya daukoshi,ya rufe sannan yafara takawa zuwa kujerarsa,jabir din na biye dashi da idanuwa,yana kuma karantarsa,ransa da zuciyarsa na masa rashin dadi,don ko kowa baice komai dashi ba,yasan akwai abinda ya motsa zuciyar ja'afar din.

      Sai da ya zauna sosai sannan ya tura file din gaban 

“An gama hada komai,na gama nawa signing din,saura naka,zaka duba inda yake da gyara sai kayi,ka saka hannu mu miqa musu takardun, withing one to two weeks ya kamata a gama” ya qarshe maganar yana maida dubansa ga wayarsa daya zarota daga aljihu,saboda qarar shigowar text,murmushi ya subuce masa ya buda text din yana dubawa,yayin da hankalinsa kacokam ya koma kan wayar tasa,abinda yaja hankalin ja’afar,ya tsaya ya zuba masa ido,kana yadan bugi table din dake tsakaninsu.

      Daga kai jabir din yayi yana dubansa,har yanzu murmushi bai bar kan fuskarsa ba

“Ina jinka”

“Baka tare dani” ya amsa masa kai tsaye da tsayayyar muryar nan tasa

“Yes…..gaskiya ne,hankalina bai wajen magana ta gaskiya,yanzu me ya rage?,inason naje gida lunch ana jirana” zube masa idanunsa yayi sosai kafin ya janyesu,kana yace masa

“Kana iya tafiya” da wani irin low tune da ya sanya tausayinsa sauka a zuciyar jabir,yafi kowa sanin yadda shaheeda tayi tattalinsa a lokacin rayuwarsa harma fiye da haka,amma a yanzu duka yayi loosing wannan caring din,dole abubuwan su dinga tabashi,duk da cewa shi yaqi bada wannan damar,yana da hope akan maimunatu shima kamar yadda yaji anni tana fada,ya sake samun gamsuwa akan yarinyar tun ranar da suka zauna sukayi magana ne tsaho a kanta da anni amma ya tattarata ya kaita makarantar kwana,annin kuma ta hana kowa masa magana,tace su xuba masa idanu suga iya nasa gudun ruwan.

         A dan shurun da ya ratsa ta tsakaninsu ne tex ya shigo tasa wayar shima,sai ya jawota yana dubawa,qaramin tsaki yaja

“this is nonsense” furucin ya fita can qasan maqoshinsa,idan ba kunne kasa sosai ba ba zaka ji me yake fada ba,kira yayi ya aje wayar saman table bayan ya sakata a loud speaker,bugu biyu ya daga

“Me kake cewa ne?,ace duk gidan a rasa me daukota?” Yace da hisham kai tsaye,lumshe idanunsa hisham yayi daga wancan bangaren kafin ya amsa shi

“Babu yaaya,drivers din duka sun fita tare da abba,yana da baqin da suke zirga zirga dasu,ni kuma nan da minti goma akwai wanda zanwa surgery,kuma emergency ne har mutum biyu,kafin na gama kuma an ja lokaci” katse kiran kawai yayi,ya fara laluban number anty maama.

     Itama bugu biyu ta daga suka gaisa

“Driver dinki yana kusa ki bani aronshi?”

“Wai…..ai kuwa yau tun sassafe ya debi yara abbansu yasa ya kaisu qauye”

“Ok” yace a gaggauce

“Akwai wani abu ne?”

“No,ki gaida yaran, thanks “

“Okay” itama ta bishi dashi,tasan halin kayanta fes,bama fadar zaiyi ba

“Waye ya bawa drivers na gidan nan hutu ne gaba dayansu?” Ya jefawa jabir dake nanuqe da wayarsa yana maidawa fatimansa reply na dinta tambayar,sai a sannan ya daga kai ya dubeshi,duk nema neman drivers da yakeyi yana jinsa,ya kuma san dalilin hakan,don kusan da goyon bayansa anni tayi wannan hukuncin

“Hey man,kai ne mana?,ka manta kenan ka zauna ka sani a gaba zaka fara tuhuma?” Tsaki ya sake ja yana tattare files din da suke gabansa

“Bari na fito maka a mutum,duk wannan goce gocen da kake bazai maka bafa,ka tashi kaje dauko yarinyar mutane kawai,three months bata nan amma don zaka bata just thirty to fourty minutes ka daukota a school sai ya gagara saboda adalci irin naka?” Wani kallo ya masa,tunda yaji amsar daya bayar yasan da issue din kenan,sai ya dakata daga hada takardun

“Idan kaji haushi me zai hana kaje kai” dariya ya sake sosai

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button