GURBIN IDO

GURBIN IDO 5

“Ko kadan…..kada ki saka sunan yuuma don Allah daada,ba ruwanta,batasan me akeyi ba tun wancan ranar data fita a dakinki”

“Ibrahim!” Ta kirayi cikakken sunansa,abunda ya sake tabbatar masa zata yanke tsatstsauran hukunci ne,kuma kowanne irin hukunci ne hakan zata fadeshi ne ba da wasa ba

“Daga yau…..idan ka sake ka sake zuwa inda maimunatu take Allah ya isa ban yafe maka ba,sannan koda bayan raina ka sake ka aureta ban yafe maka ba” qarasa zama dirshan yayi a qasa maimakon tsugunon da yayi,ba qaramin kaduwa da hukuncin nata yayi ba

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya dinga maimaitawa kansa a qasa,bai taba zato ko tsammanin hukuncin innar zaiyi tsaurin haka ba

“Don Allah inna ki sassauta kiyi haquri,maimunatu bata taba yi miki komai ba,banda…….” Tsawa ta dakeshi tana katseshi

“Banason na sake jin komai daga gareka,wannan shine hukuncina na qarshe,tashi ka fita!” Ta fada a zafafe tana nuna masa qofa,sai da ya dafa qasa sannan ya miqe

“Himu” ta kirashi sanda yakai qofa

“Na baka kwana hudu kacal,ka shirya fara zuwa wajen gaje kamar yadda na gaya maka,umarnine nake baka” bayajin xai iya cewa da ita komai,don haka kansa da yayi masa nauyi kamar ya dauki kaya ya gyada mata sannan ya fice daga dakin yana jin jikinsa kamar zazzabi na shirin rufeshi.

**********Sake juya rufaffen takalmin danqon hannunta tayi don ta tabbatar dabarar data yi masa zata kaita gida,ita kanta batasan adadin liqin data yi masa ba,wani gurin da garwashin wuta da leda,wani gurin kuma tana samun zaren lilo ta zarge inda yake shirin rabewa dashi.

A hankali ta duqa ta ajjiye takalmin a qasa ta zura qafafunta,tadan motsa qafar ta tabbatar yayi,sai ta sauke ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ya sake fiddata a yau dinma dai still,takalmin bai mata tutsu ba,batasan ya zata kasance mata duk randa hakan ta faru,itadai shi daya ta sani a matsayin takalmin da take dashi,wanda ita kanta batasan adadin kwanakin ko shekarunsa ba a duniya bare ta iya tantancewa.

Sake waiwayawa tayi hagunta da damanta,har yanzu bata debe tsammani da ganin himu ya bullo ba,duk da cewa lokacin zuwan nashi ya gota sosai,tana da tabbacin babban abune ya tsaidashi,saidai tana fatan koma meye ya kasance yana lafiya qalau.

Waiwaya tayi sashen wata saniya ke zaune,gefanta jaririn san data haifa ne a dazu jimawa kadan bayan isowarsu wajen,ta tabbatar inna batasan cikin ya isa haihuwa ba,da ba zata bar mata ita zuwa wajen kiwo ba,dole idan lokaci yayi himun baizo ba,haka zata hada da kula da sauran dabbobin,da ita wannan sabuwar haihuwar su wuce gida,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,ita kadai cikin wajen,cikin tsoro da fargaba saniyar tahaihu a wajenta,wanda ita kanta tasan babbar kasada tayi,saboda samuwar matsala ta mutuwar uwar ko abinda aka haifa,dai dai yake da samuwar matsala cikin tata rayuwar,ko daya innar batasan wata aba wai ita asara ba bare haquri da ita idan ta sameta,haka ta dinga kai kawo har haihuwar ta kammala.

Saman dan dutsen da himun ke zama ko yaushe idan yazo ta koma ta zauna,idanunta nakan abun hannunta na shirin duwatsu green da jaa,tasa yatsanta guda daya tana wasa dasu,ta warasu wani lokacin ta hadesu,tana tuna lokacin da innarta ta zura mata su,har yanzu lokacin yaqi bacewa cikin idanunta.

Ta jima zaune a nan,tana jin wata kewa da kadaici suna shigarta,lokaci lokaci tana daga kai ta dubi yanayin yadda dabbobin ke kai kawo sannan ta sake maida kanta.

Karo na qarshe data daga kanta ta tabbatar lokaci yayi da ya dace su koma gida,ta sauka daga kan dutsen a hankali,ta gyara zaman hularta sannan ta dauki sandanta ta fara ratsawa ta tsakaninsu tana hada kansu.

A gaba take sanyasu mafi yawancin lokuta,idan taga zasu canza hanya ko zasuyi wani abu ba dai dai ba takan tsawatar musu,suna ji kuma suna fahimta yawancin lokuta,yau dinma haka ne,hannunta na dauke da sabuwar haihuwar da daya daga cikin shanun tayi.

A hankali baqaqen lafiyayyun motocin guda biyu ke kutsowa cikin rugar,tana haura duk wani tudu da kwari da kuma kwazazzabo dake kan hanyar ba tare da mutanen dake ciki sunji komai wata jijjiga ko wahala ba da ire iren wadan nan hanyoyin ke dashi a duk sanda mota zata ratsasu ba,hakan ya faru ne sanadiyyar kyau da lafiyar motar,wanda hakan yake da nasaba da irin tsadar da kowacce mota guda daya ke da ita.

Motar farko mutum hudu ne a ciki,driver salmanu,sai wani zaune a gefansa hayatu,daga seat din baya kuwa dattijuwar macace,hakimce cikin shiga ta alfarma,kyakkyawar lallausar blueblack din atamfa ce wadda tayi matuqar haska farar fatarta,duk da akwai tsufa tattare da ita,amma yanayin da take ciki na hutu da kuma jin dadi ya hana bayyanuwar tarin shakarunta,daga shekara sittin da takwas,ya maidata zuwa ‘yar shekara hamsin,idan ka cika qwaqwafi kuma ka qara mata da uku,hankalinta na ga window din motar,tana duban hanyoyin da suke wucewa,wanda sukanyi gamo da mutane jifa jifa,duk mutumin da suka gifta sai ya bisu da kallo,saboda abune baqo a wajensu,zasu iya irga sau nawa suka samu labari ko sukaga shigowar mota rugar tasu,wasu sukan cika da fargabar su waye suka shigo musu?,wasu kuma kyau da motar ke dashi ne yake daukar hankalinsu har sai tayi nisa ta bacewa ganinsu.

Daga gefan dattijuwar kuwa kyakkyawar matashiyar budurwa ce wadda duka duka ba zata haura shekara ashirin ba a duniya,shigarta kadai zai gaya maka cewa ta fito daga gidan ilimi wayewa da kuma wadata,kacokam ta tattara hankalinta ga wani littafi dake da shafuka masu dan dama,da alama nazari takeyi.

“Salmanu……..saukemin gilashin nan…..naga alama wannan baqin abun da kuka lafta masa bazai bar idanuwa suyi kallo yadda ya kamata ba” ta fadi tana hade gira.

Karaf matashiyar ta daga kanta daga kan littafin

“Haba anni….me kuma za’a sauke miki kiji?,an kunna ac ne fa,ta yaya za’a sauke glass,kuma ta hakan ma ai ana ganin komai,tunda ba dare bane” harara ta juyo ta watsa mata

“Ke….kiyi ta kanki,ni ba dake nake ba,toke da wanne mataccen idon ma kike iya gani daga nan din?,idon da komai za’ayi saida gilashi?,salmau zaka saukemin ko kuwa?”

“Za’a sauke anni” yayi maganar yana sauke mata da hanzari kamar yadda ta buqata.

       Sai da aka sauke mata gilasan tas sannan ta sake matsawa jikin window din tana fara'a

“Yawwa,yanzu naji batu,amma daa an qunshe mu kamar ‘yan kidnapping,ni ba baqin hali gareni ba da kullum xan fita zance a rufeni cikin gilasai” sarai matashiyar ta fahimci da ita take,kuma idan da sabo ta saba ko kuma tace sun saba da halin anni,duk wanda ke zaune da itama ya riga da yasan halinta sarai,don haka sai ta maida mayafin da yake kafadarta zuwa saman kanta,ta kuma rufe littafin saboda hasken ya mata yawa,karatun bazai mata dadi ba ta maida jakarta,ta ciro wayarta a maimakon littafin ta soma qoqarin kunna data,saidai yanayin rashin network mai kyau ya hana wayar tata amfani,dole ta maidata itama jakar.

“Ma sha Allah,kai ma sha Allah,lallai na jima rabona da adamawa,wai” anni keta fadi,fuskarta na nuna alamun jin dadin tafiyar sosai.

A dan rude maimunatu ta maida hankalinta ga marabar hanyar da shanunta ke tsallakawa saboda jin wani sauti,hango motocin suna tahowa yayi matuqar daga mata hankali,na farko yadda zata tsaida dabbobin da sukayi nisa da tsallakawa ta bawa motocin dama su wuce,na biyu kuma motocin sunyi matuqar sanya mata fargaba da tsoro kamar yadda suka sanyawa mutanen da suka baro a baya,su waye a ciki?,me sukazo yi cikin rugar tasu?,wadanne irin motocine wadan nan da sam bata taba ganin koda me shigen kamarsu ba?.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button