GURBIN IDO

GURBIN IDO 5

Yadda suke sake kusanto inda suke ya sanyata yunqurawa da hanzarinta ta fara bawa dabbobin nata umarni da dukka salon da tasan suna iya karbar umarni da hani daga gareta,tanayi tana kutsawa ta cikinsu tare da dan daga muryarta.

“Kai salmanu……dakata” anni ta fada da sauri,idanuwanta suna sauka akan maimunatu,sosai ta zuba mata idanu cike da mamakin yadda take iya bawa dabbobin umarni da baki take kuma iya sarrafasu ba tare da takai duka ma ko daya daga cikinsu ba,idanun anni ya sauka ga dan qaramin dabbar dake hannunta,fari qal dashi sabuwar haihuwa,abinda yaja hankalinta kenan zuwa ga garken dabbobin,ta dinga binsu da kallo daya bayan daya

“Ma sha Allah,wadan nan dabbobin gaskiya na qwarai ne,sun samu kiwo da kulawar data kamata”

“Abinda nake fada a raina kenam hajiya yanxu hajiya,babban abun mamakin yadda qaramar yarinya kamar wannan take iya kula dasu gaba dayansu” cewar hayatu shima idanunsa akan maimunatu

“Bari hayatu,kaga inda ake mata,ba irin ‘ya’yanmu ba cima zaune da komai suna zaune ake musu” anni tayi maganar tana tabe baki.

Dariya ce taso qwacewa matashiyar amma ta danneta,sai murmushi da ya fita a fuskarta,yayin da hayatu da kuma salmanu suka dan dara kadan,saboda sunsan da wadda take,a tsakaninsu suka dinga tattaunawa,har zuwa sanda maimunatu ta ratsa ta gaban motocin suka wuce da dukka dabbobin,tana dan duba da kuma waiwayen motar tana mamakin yadda suka dakata mata suka bata dama ta wuce.

Ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bayan data tabbatar sun tsallake lafiya,abinda ya taba faruwa da ita shekarun baya bai sake maimaita kansa ba,wanda ita daya tasan bala’i da masifar daga fuskanta a sannan,har yanzu tana iya tuna sanda motar ta taho a guje,bata kuma damu data tsaya ba ganin dabbobi suna qetarawa,tana hango sanda motar ta banke dan dalonta da take matuqar ji dashi,ya zube a qasa jini na fita ta hanci da bakinsa,ta bishi da gudu ta tsugunna a gabansa tana kuma saboda ta tabbatar bazai tashi ba,taji mugun cin birkin da motar tayi,da fadan da wata murya ke mata tsaye a saman kanta,fadan da yafi kama da a dakeka a hanaka kuka saboda cikin xafi da fadar maganganu marasa dadi ake yinsa,abinda ya sanyata daga kanta ta dubi.mai maganar.

Kalmomin da zata gaya masa masu zafi take nema amma ta rasa,saboda ita din ba gwanar rashin kunya bace,bata ma iyata ba sam,to dawa zatayi bayan dabbobin sune qawayenta?,abu na qarshe da take ganin xata iya shine watsa masa harara gami da tsaki mai nauyi,kafin ta sauke kuwa aka sauke mata wani zazzafan mari da ya sanya wuta ta dauke mata gaba daya,ta daina gane komai,bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wani lokaci.

Ko a yanzun data tuna sai data runtse idaunta,tana tuna zafin marin saman fuskarta,abinda ya biyo baya kuwa ta gefan inna azaba ce ta cita mai yawa,bata damu da yadda fuskarta ta tasa ba saboda marin data samu akan abinda ita ke da gaskiya,ta tattara laifin gaba daya a kanta,tare d adora alhakin mutuwar dan maraqin saniyar a wuyanta.

Ajiyar zuciya ta sauke sanda suka iso gida,kamar kowanne lokaci ta daga murya ta sanarwa innar ta dawo,bata ajjiye dan jaririn a hannunta ba sai data qaraso ta miqa mata shi,bakinta har kunne,kai kace jika aka haifa mata na dan mutum

“Dama kinsan ta kusa sauka amma baki garzayo kin kirani ba?” Innar ta fadi haka cikin tuhuma,bata amsa mata da komai ba,itadai tana duqe tana daure wasu akuyoyi,banda abu irin na dan adam,ta samu uwa da dan lafiya,bata damu da yi mata sannu na wahalar datayi da naggen ba har ta sauka lafiya,ta buge fa tuhumarta,wanda tayi imani cewa inda ta barta a can ta taho kiranta wani abu mummuna ya faru,lallai ba zata daga mata qafa ba.

Tunda taji maimunatun tayi shuru tasan ba zata tanka mata ba,ita kanta ta santa da wannan halin,a wasu lokutan idan tayi mata irin hakan,yaxo akan gabar da take cikin fushi ko takejin haushinta,kamata take ta nada yadda ranta yayi mata suga.

Daga yau free pages sun qare,paid pages zasu biyo baya in sha Allah,hanzarta biyan naki kudin koki bibiyemu ta shafukanmu dake arewabooks

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button