HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

 

1/11/22, 15:42 – Buhainat: Halin Girma

    11

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

_(Palace of exotic scent and more)💯❤️_

 

_MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi
kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers ‘yan yyi dominku da
yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da kayan
decors,plated gold,da turaruka kala-

kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga
kamfanin naseem hr suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria.
Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka
wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da wasu kasashen ketare
ngd_

 

***

A wani yanayi Maman ta dago, gabanta ya fadi ganin Abba a tsaye
a kofar Zeenat na rakube a gefe kamar munafuka

 

“Dr, Sannu da zuwa.”

 

“Kinsan daga ina yarinyar nan take?”

 

Ya nuna Zeenat yana jin kamar ya rufe ta da duka.

 

“Aiken ta ne nan baya gidan Amarya me koko.” Tace
bayan tasan ba hakan bane. Kwafa yayi cikin kada Kai yace

 

“Yaron da nace babu ita babu shi take zuwa suna haduwa a
bayan layi, na fad’a miki na kuma bana son yaron domin ba yaron kirki bane,
amma a bayan kunnenku.”

 

“Idan har ta dage ba zata ji magana ta ba, zata dinga fita
suna haduwa a wani wajen ba da izini na ba ko na yan uwana, zan sallama masa
sai tace ya turo,amma…”

 

Ya nuna ta da yatsa

 

“Idan har wani abu ya je ya dawo, kar ku  kuka da kowa, ta kuka da kanku!”

 

Shiru Maman tayi taki cewa komai, haka Zeenat din da ya zaci
zata bashi hakuri sai yaji tayi shiru

 

” Kin amince da Bashir din, kin yarda zaki aure shi?”

 

Daga kanta tayi da sauri babu kunya ba tsoron Allah, wani irin
faduwa gaban Abban yayi, yaji tamkar zai fadi saboda wani jiri da ya nemi zubar
dashi, be zaci haka daga gareta ba, sam ba tarbiyyar da yayi wa yaransa bace,
sake maimaitawa yayi cikin danne abinda yake ji yace

 

” Kinji kin gani, kin Amince?”

 

” Dr ka bar maganar nan idan muka shiga ciki sai
mu…” Dakatar da ita yayi da hannu, ya dakawa Zeenat din tsawa

 

” Ki bani amsa!”

 

” Eh Abba.” Tace tana nokewa idon ta fes tamkar an
soye gyada

 

” Shikenan, shikenan.” Ya maimaita

 

” Kice dashi ya turo magabatansa, suzo wajen Yaya.”

 

Sai ya juya wajen Iman da tayi kamar ta bud’e kasa ta shige
saboda kunyar abinda Zeenat din tayi yace

 

” Kema ki ce masa ya turo dan ba zan bata lokaci ba.”

 

Daga kanta tayi da sauri, ya wuce su yana jin wani irin tashin
hankalin abinda Zeenat din tayi, tabbas laifin Hajara ne, ita ce bata
tankwarata ba, bata nuna mata daidai da akasin haka ba, abinda ma ya lura Itace
take son abin, ba zai yarda wani abu ya faru ba a dalilin hana ta auren Bashir
din, dan yaran yanzu zasu iya komai akan soyayya, shiyasa kawai ya yanke
shawarar aura mata shi din idan har ta kafe, da azo ana wallahi tallahi.

   Abban na barin wajen
itama Iman tayi saurin ficewa dan tasan sarai Mama zata huce akanta, tana juyo
fad’an da take wa Zeenat din sama-sama, ta kara sauri ta zagaya ta baya ta
shiga ta kitchen ta wuce dakin su kawai.

   Tsawon kwanakin Abba
bashi da walwala sam, ita kanta Mama ta kasa gane kansa, da ya shigo zai wuce
dakin sa kawai sai kuma gobe, a da tayi tunanin fushin ba zai nisa ba, sai taga
abin yana neman zarcewa, takanas ta same shi da maganar da ban hakuri amma sai
ya share ta yama yi ficewar sa ya barta, haushin hakan ya sakata share shi
itama ta san dole zai gama fushin sa ya dawo ko da Anyi auren yaji su kalou zai
ajiye komai ya dawo, tasan ta fishi gaskiya shiyasa taki goyon bayan sa, dan
tasan zugashi akayi dan an ga Zeenat din zata huta.

  

***Bayan tafiyar Muhammad basu yi magana da ita ba, sau biyu
tana kiran number sa bata samun sa, hakan ya saka ta damu sosai, gashi tasan
Abba zai sake mata magana akan abinda yace ta fad’a masan, gashi bata sameshi
ba, tsoron ta daya Allah yasa ba guduwa yayi ba, dan har ga Allah zuciyar ta,
ta yarda dashi. Har tana jin son sa na shigar ta, koman sa daban ne hatta
maganar sa, ta kasa gane komai akansa musamman a fagen da zata ajiye shi,
yanayin sa da koman sa yasha banban da shigar sa, tana bukatar sanin sa sosai
kila ko bayan sunzo da iyayen sa an daidaita, a lokacin zata bijiro masa da
tambaya akan sa, ko da ba komai ba, a kalla ya bata labarin wani abu da ya
shafe shi.

   Fitowa tayi falo ta
zauna bayan ta gyarawa Gaji daki, maman su Maryam ce ta shigo, ta gaishe ta
tana tashi ta kira mata Gaji, tare suka dawo da Gajin ta gaishe ta sannan suka
soma hira akan abubuwa da dama. Ita dai Iman na zaune tana jin su tana duba
wayar ta. Maganar Maryam suka shiga ya sakata d’agowa tace

 

“Umma Ya Maryam din ce bata da lafiya?”

 

“Wallahi Iman, wai har kwananta uku a asibiti amma basu
fadawa kowa ba, bari tayi an sallameta dazu amma, shine nake tunanin wanda zai
je mata ya dan taimaka mata ko na sati daya ne.”

 

“Allah sarki, Allah ya kara sauki.”

 

” Ko ke zaki je ne takwara?”

 

“Toh…” Tace har cikin ranta bata so ba

 

” Iman bata son mutane ai, zata iya zuwa kuwa? Maman su
Maryam din tace tana murmushi

 

“Idan ta kamata ya zatayi?” Gaji tace

 

“Wai kar a takura ta dama.”

 

“Haba kinji wani zance, yar uwarta ce fa? Idan batayi mata
ba wa zatayi wa?”

 

“Haka ne.”

 

“Zance Umma, ba komai ai.”

 

“Toh shikenan, anjima sai wani cikin samarin ya mik’a
ki.”

 

“Ai ba sai anjima ba, yanzu zata shirya sai su wuce, ki
shiga sai ki sanar da Maman tasu, idan yaso sai ta fadawa Ibrahim din duk da
nasan babu abinda zaice.”

 

“Toh shikenan bari na shiga wajen nasu.” Ta tashi ta
fita,ita kuma Iman ta wuce ciki ta dauko charger ta tazo ta fita.

 

   A zaune ta tarar da
Umman suna maganar da Mama, tana shiga tace

 

“Ki shirya zaki je gidan Maryam kiyi kwana biyu, Allah ya
kara sauki.”

 

“Toh.” Tace ta wuce ciki, ta dauki wata karamar
Jakarta, ta saka kayanta kala biyu sai undies da hisnul muslim, da dan abinda
tasan zata bukata ta fito, bata ga su Maman a falo ba, sai ta nufi dakin ta
rataye da jakar a kafadarta, ta kwankwasa kafin ta shiga

 

“Mama na fito.” Tace daga kofa, jakar ta dake kan gado
ta dauko ta ciro dubu daya ta mik’a mata

 

“Sai kin dawo.”

 

Hannu biyu tasa ta karba mamaki na kamata, tayi godiya ta fito
still tana jin kamar mafarki, magana me dadi daga Mama har da bata kudi? Akan
me? Sam sai taji hankalin ta be kwanta ba, taji kamar ta koma ta tambaye ta
dalilin action dinta amma babu hali.

  Ita kadai ta dinga juya
dubun har suka isa gidan Maryam din, ta fito rik’e da jakar ta shiga gidan. A
falo ta tarar da ita da mijinta sai sister dinshi wata babba haka. Wani farin
ciki ne ta gani a fuskar maryam din, ta tashi zaune tana mata sannu da zuwa.

  Gaishe su ta fara yi
suka amsa dukka sannan ta nufi wajen Maryam din tana mata ya jiki,

 

“D-D bari naje na kai Yaya gida tunda ga Maryam tazo.”

 

“Ok tam.” Tace

 

“Nagode sosai Anty Saliha, ku gaida gida.”

 

“Gida zaiji Maryam, Allah ya kara sauki ki kula da kanki
sosai kinji? Ki dinga cin abinci sosai saboda kiyi saurin dawowa dai, Allah ya
kawo wani rabo me albarka.”

 

” In Sha Allah zanci, nagode.” Tace a kunyace, sukayi
sallama suka fita

 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button