HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

“Yaya, wani labari naji fa, dangin mijinki na hirar basu
san Ina wajen ba, naji suna cewa Iman tayi goshi ta samo jinin sarauta, ana ma
tunanin dan sarki ne duk da Basu tabbatar ba ana boye zancen ne amma kamar
hakan ne.”

 

Wata irin dariya Maman ta saka, har da hawaye

 

” Kinji ki Fatima da wani zance, su fa basu san kan zancen
ba, maganar Zeenat ake ba Iman ba, na ji wannan zancen tun bayan zu ba ai,
kawai na kyale mutane ne yadda abun zai kada su, ba dai anjima kadan zasu iso
ba? Zamu gani ai.”

 

” Allah yaya? Kin Kuma tabbatar da hakan ne?”

 

” Zaki gani ai.”

 

Tayi gaba tana murmushin mugunta, ba karamar kunya tasan za’a
sha ba a lefen Iman din ba.

 

 

Hmmm

 

 

 

 

 

 

***Assalamu alaikum sisters fatan alkhairi ga kowa da kowa. In
Sha Allah hutun mu zai kama asabar da lahadi, domin kowa ya samu damar aiwatar
da wani abu me muhimmanci a rayuwar sa, sannan mu kula da gidajen mu da iyalan
mu dukka, mu bawa yaranmu da mazajenmu lokacin da suke bukata daga garemu. In
Sha Allah Monday to Friday za’a samu posting in sha Allah, sai dai wani uzurin
ya gifta. Sannan masu korafin ba’a basu page biyu ko uku a rana, wani page
dayan yayi wasu pages din guda biyu, so idan hakan ne gwara dayan me tsawo mu
tafi a hankali har Allah ya bamu ikon kammalawa.

  Zafafa biyar na godiya
da zabin su da kuke a kowanne lokaci, dan Allah mu cigaba da yi ma juna uzuri
kuma mu kyautata lafazi a tsakanin mu domin magana me kyau ma sadaka ce.

 

 

Masu sharing novels group group una weldone kunji? Dan Allah ku
daina babu kyau, ka sowa dan uwan ka abinda kake sowa kanka hakan na cikin
cikar imanin mumini.

 

Rano

1/18/22, 19:58 – Buhainat: Halin Girma

    14

 

 

_*Zafafa biyar na kuÉ—i ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki
karanta. Muna haÉ—aki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan
cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar
zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

 

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

 

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

 

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

 

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

_________________________

 

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*

 

*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki
mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

 

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma
nagartattu irin namu na gida da suka sami haÉ—i na musamman da babu cutarwa a
ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

 

*_Muna da haÉ—in_*

 

_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

 

_Muna Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

 

_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_

 

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

 

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

 

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi
da rahusa. Ga mai buÆ™ata sai ya nememu tanan 👇ðŸ
¼_*

 

_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE
d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

 

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN
KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_

 

•••••••••�

 

 

 

*****

Azahar sosai ya tashi, ya mike yana salati, daga curtains din
dakin yayi yana mamakin tsawon lokacin da ya dauka yana baccin, wayar sa dake
saman gadon ya dawo ya dauka ya bud’e ta, misscalls ya gani ya duba sannan ya
ajiye ya fito zuwa falo in da yatar da abincin sa a jere cikin manyan warmers
sai kuma wani dan basket da aka rufe shi da jan kyalle me kyau dake dauke da
hoton heart, matsawa yayi gabansa yana kallo,

 

“Menene wannan?” Yayi maganar yana rik’e kugun sa da
sauri wani bafade ya shigo, ya rissina yace

 

“Sako ne daga shashen Kilishi, inji gimbiya Laila.”

 

“Laila?” Ya furta cike da mamaki

 

“Yaushe ta zo?”

 

“Tun da safe, lokacin baka nan.”

 

“Dauke shi a kai sashen Ammi, ace ta ajiye.”

 

Sake dukawa yayi cikin girmamawa yace

 

“An gama ranka ya dade.”

 

Juyawa yayi ya koma ciki, yayi wanka sannan ya shirya yana
tunanin dawowar Laila a irin wannan lokacin da yasan suna tsakiyar karatu ne.
Fitowa yayi ya tsattsakuri abincin ya fita wajen ammi dan be samu ganin ta da
safe ba.

 

A gabanta ya tarar da sakon nasa, ta bishi da kallo sannan ta
kalli kwandon da yake na Kaba. Sai da ya zauna ya gaishe ta sannan ya saka aka
miko masa basket din

 

“Ammi kinga ko? Menene ma’anar haka?”

 

“Ni kaina nayi mamaki, amma kuma kasan dama hakan zata faru
idan har ta samu labarin auren ka.”

 

” Bana son wata matsala gaskiya, zan aika da sako wajen
Kilishin dan ba zan dauki rainin hankali ba.”

 

” Ka rabu dasu, karka yarda su bata maka rai har kayi
tunanin biye musu, ka cigaba da addu’a nima kuma ina tayaka mahaifin ka ma,.ba
zasu taba samun nasarar abinda suke so ba.”

 

” Shikenan Ammi, dan Allah aje a kona basket din nan dan
bana son ko ganin sa.”

 

” Shikenan, ka cigaba da walwalar ka karka yarda makiyinka
ya gane weakness dinka.”

 

” In Sha Allah Ammi.”

 

” Allah yayi maka albarka.”

 

” Amin.” Ya amsa yana jin tamkar dawowar Laila akwai
wani babban dalili

 

” Yawwa na kira Fatima akan lefen ka, zata hada komai in
sha Allah, idan yaso sai su tafi ita da kai da wata dai cikin su, Takawa ma yace
shi zaiyi komai, amma duk da haka Fulani tace yayi nasa itama zatayi nata mu ma
nan sai muyi namu.”

 

“Wayyo ni dan gata.” Yace yana murmushi

 

“Ammi gatan kar yayi min yawa ai.”

 

“Ba zai ba, Allah yasa ayi damu kawai, amma dole sirikata
taga gata.”

 

“Uhm.. Allah sa idan tazo karta kwace min wajena.”

 

” Dole ne ai, kasan dai yadda nake son ya mace ko?”

 

” Shikenan sunana sorry wallahi.”

 

Dariya Ammi ta saka

 

” Aikam ka shirya tun yanzu.”

 

” Shikenan, Muhammad kana ji? Kayi hakuri da duk abinda
zaka gani.”

 

Ya fad’a cikin yanayin kalar tausayi, dariya sosai ya bawa Ammi
tayi sosai, kallon ta ya dinga yi cikin tsantsar son ta, yana son Ammi da duk
wasu halayenta, babu abinda yake so irin yaga tana farin ciki sosai, hakan yake
sashi jin zai iya komai dan ganin ya faranta mata, ya dawwamar da farin ciki a
kan fsukar ta, hakan kuma ba zai yiwu ba sai dole yaki karbar muradin Bubu,
dole ya hakura da mulkin ko da yana so, saboda farin cikin Ammin Sa!

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button