HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

***Satin Mama daya cif a Katsina, ranar da zasu dawo ranar
Bashir ya iske su a chan da dalleliyar mota da sha tara ta arziki, murna wajen
Mama da Zeenat ba’a magana aka dinga turashi gida gida na dangi dan aga irin
mijin da zeenatun ta samo, aikuwa nan da nan magana ta karade ko ina cikin family
din Maman, anan wasu da yawa suka samu labarin bikin Zeenat din wanda aka saka
wata daya kachal bayan Bashir din ya tabbatar musu da zaiyi komai basa bukatar
komai hatta da kayan gida duk shi zai zuba, hakan ya sake fasawa Mama kai ta
dinga hura hanci a lallai zeenatun ta ta dallo miji na kere sa’a, tausayi da
farin cikin halin da ta tabbata Iman zata shiga idan har ta auri fakirin nan
take, gashi dai su kam Allah yayi musu gam da katar dan yadda aka dinga maganar
Bashir din a dangi kadai ya ishi Mama tutiya da alfahari.

   A motar ya kwaso su
Zeenat na gaba gida na tashi cikin taken soyayya Mama da Marwan na baya har
Kano, Zeenat ji take kamar tafi kowa sa’a a duniya dan da gaske take jin wani
irin son Bashir din na ratsa ta.

   Sanda suka isa gida
magriba tayi saboda basu taho da wuri ba yana faman zaga dangi, alwala aka kawo
masa ruwa yayi, ya zauna Zeenat din ta shiga ta fito suka dasa sabuwar hira
irin ta yaushe rabo. Cikin hirar ne yake fad’a mata lefe in sha Allah za’a kawo
cikin upper week, zai sanar mata da ranar sai ta fadawa Mama, hakan yayi mata
dadi har tana hasashen uban kayan da za’a kawo mata dan taga Bashir din me
bajin ta ne sosai.

  Ranta fes ta koma ciki
bayan ya tafi, ta labartawa Maman lokacin Matar Abba Musa ta shigo wajen Maman
yi mata sannu da zuwa.

 

“Haba ni nayi mamakin da aka ce manyan mutane ne suka zo
neman aure gidan nan na tabbata dama wajen Zeenat ne, yarinya kakarki ta yanke
saka wallahi.”

 

Tace tana dariya, murmushi mama tayi

 

” Kice manyan mutane ne suka zo? Bani labari Binta.”

 

” Ai Maman Habib baki gani ba, wallahi manyan mutane ne
kamar ma daga wata babbar masarauta, yadda naga mazan gidan nan sun rikice
kadai zaka gane ba kananun mutane bane, na zata ma na Iman ne ashe na Zeenatu
ne, Baban Walid be min bayanin da zan gane ba kinsan wajen lokaci daya suka zo
dukka.”

 

” Aikuwa sune, kai kice dai manyan mutane ne, masarauta fa?
Kai masha ALLAH abu yayi kyau wallahi.”

 

” Ai Maman Habib ba karamin dace Zeenat tayi ba wallahi,
Allah dai ya kaimu bikin nasan za’a ga lefe na ban mamaki.”

 

” Bari kawaii, sai muzo mu tanadi kyautar girma da zamu
fita kunya, na gode da kika sanar dani dan Dr ba lallai ya fad’a min ba muna
yar tsama dashi.”

 

” Ai haka suke, basa fadar cikin su wallahi, itama kuma
Gajin ba zaka ji daga bakin ta ba tunda komai suna fad’a mata ai.”

 

Tabe baki Mama tayi

 

” Ai ni baki sani ba, so akayi a yi min bakin ciki.”

 

Sai ta rage murya

 

” So akayi fa a hana Zeenat auren Bashir din nan, kuma ina
kyautata zaton akwai saka hannun Gajin a ciki, toh in ba haka ba yadda Dr ya
rikice akan maganar lokaci daya zaki gane zugashi akayi.”

 

Kama baki Matar Abba Musa tayi

 

” Allah? Tab ashe an so yi miki tsakiyar da ba ruwa.”

 

” Ke dai bari, shiyasa na tsaya kai da fata, kinsan mutane
basa son ka cigaba ko aga danka ya cigaba ko zai huta.”

 

” Zahiri, toh Allah ya kyauta, ban yi zaton hakan daga
gareta ba.”

 

” Ai ba laifin ta bane, itama yadda aka dora ta haka zata
tafi akai.”

 

” Eh kuma gaskiya, tunda kinga ai bata cika saka ido akan
al’amuran mu ba.”

 

” Shine, koma waye kansa yayi wa, aure kam babu
fashi.”

 

” Assalamu alaikum.”

 

 Iman tayi sallama ta
shigo, gimtse fuska Maman tayi,ta gaishe su matar Abba musa ta amsa a sake tana
tsokanar ta da amarya amarya, murmushin yake kawai tayi tana satar kallon
yanayin fsukar Maman, zuwa tayi ta fad’a mata anjima zata tafi wajen dangin
Mamanta amma ganin Matar Abba Musa ya saka ta fasa ta wuce kawai daki ta karasa
hade koman ta waje daya.

  Bayan tafiyar Matar Abba
Musa ne ta fito ta samu Maman a kitchen tana rarrabe kayan da tazo dasu dangin
su kuka kubewa da daddawa waje daya

 

“Mama dama yau zan tafi gidan su Mamana.”

 

Tsayawa da abinda tayi, tayi ta kalle ta a mamakance tace

 

“Yau? Yaushe aka yanke 
maganar tafiyar taki ban sani?”

 

“Dama tun ranar da na dawo daga gidan Ya Maryam Abba yayi
min maganar.”

 

“Toh! Shi zai kaiki kenan? Ko turowa za’a yi kije? Ko da
yake mutanen da basu damu dake ba yaushe zasu turo? Wannan din ma nasan dan Dr
yayi magana ne.”

 

“A ah tare da Abban zamu je.”

 

“Kutmar Uba!” Da sauri Iman din ta ja baya dan yadda
ta ga Maman ta birkice lokaci daya

 

” Ni za’a yiwa munafurci? Wato yace zai ganki saboda yaga
tsohuwar matar sa ko? Dan an raina min wayo an maida ni wata sakarai. “

 

” Dama… “

 

” Dallah rufe min baki, wato gani shashasha an dauko raino
an bani shine yanzu za’a nuna min bariki ko? Toh wallahi ba zata sabu ba
wallahi kinji na rantse, ko ya barki ki tafi ke kadai ko ya hada ki da wani
cikin yan uwansa ko Hafiz ne ma. “

 

Shiru Iman tayi kamar ruwa ya cinye ta, tana jin sababin da
Maman take kanta na kasa ita dai bata ce komai ba,me zata ce ma?

 

” Bari yazo naji abinda yasa zai munafurce ni wallahi,
bayan duk kokaarin da nayi wajen rik’e ki amma sam yanzu baya gani, dan kawai
yar matsala ta ratsa tsakanin mu shikenan sai ya rufe ni. “

 

” Uwata zo ki wuce, kije waje kina da bako. ” Abba da
yazo a lokacin yace yana kallon Maman, sum sum Iman ta fice kafin Abban ya dubi
Maman cikin bacin rai yace

 

” Kin bani mamaki Hajara, ban zaci haka daga gareki
ba.”

 

” Dama ai haka ne, duk abinda mutum yayi ba gani za’a yi ba
musamman aka ce da ba naka bane, amma ai Allah ya gani. “

 

” Bakya tsoron Allah kuwa in dai haka ne, har kece zaki ce
Allah yana gani? Kina tsoron haduwar ku kuwa? Bayan wahalar da kika bawa
yarinyar nan har kina da bakin magana? “

 

” Wahala? Ita tace maka na bata wahala kenan ? Oh shine ka
shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda
nayi baka gani ba. “

 

” Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa
Ummi, kinci amanata kin ha’ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba
sani ba.”

 

” Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar
ko, ko nace tsohuwar karu… “

 

 A wani irin bacin rai ya
daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik’e  hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin
mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta
bata mishi rai.

 

“Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya
san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida,
shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?”

 

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman
ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik’e
masa riga ta baya

 

“Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda
ba.”

 

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge
rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata
ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .

  Shashen Gaji ya wuce da
ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga
Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.

  Tana shiga Mama dake
tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad’an ta fadi amma ta tsaya akan
kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button