HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

“Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato
kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na
gama cin wahalar ki.”

 

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga
sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman
magana,

 

” Lafiya Mama? Me tayi?”

 

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.

   Abinda Abba ya guda sai
da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace
bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya
dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana
kallo ta cigaba da haukanta.

 

 

 

***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin,
karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya
kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a
k’asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi
risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji
labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya
gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya
so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun
relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin
gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope,
sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake
jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai
sauran lokaci.

   Tunawa da tayi da
envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud’e, murmushi tayi
ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart
a k’asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai.

   Cigaba da rikewa tayi a
hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana
jin wani irin feeling, she’s nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba.
Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.

 

“Mun sauka.” Taji yace sai kuma yave

 

“Owk tura min number shi.”

 

Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message
ya ciro ta ya kira ya fad’a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa

 

“Ummi muje gashi chan ma.”

 

Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda
yake nufo su.

 

“Welcome Sir.”

 

 Yace cikin girmamawa, ba
bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a
daidai aljihun.

 

“Thank you.”

 

Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban
motar ya zauna ita kuma Iman ya bud’e mata baya sannan ya jasu suka fita daga
airport din.  A daidai wani hotel suka
tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace

 

“Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina
bukatar wani abu ki kirani.”

 

“In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe.”

 

“Allah ya kaimu.” Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga
gefe yana kallo suka bar wajen.

 

   Ta cikin dark tinted
glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da
dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.

    A wani babban gida
cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din
ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin
ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka
nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button