HALIN GIRMA 11-15

” Sa mana key din a kofar.”
Tace wa Maryam din tana
gyara zaman ta. Key din Maryam ta saka musu ta dawo ta zauna kusa da ita
“Ashe ke zaki zo, naji dadi da ba’a turo wata cikin yaran
chan ba wallahi.”
“Wallahi, ya jikin naki? Naga kinyi fari sosai.”
” Toh ba dole ba, kin ga uban wahalar da nasha kuwa? Kai
Iman aure- aure akwai wahala wallahi.”
” Sannu, Allah ya kara sauki.”
” Amin ya Allah.”
” Ya gida yasu Mama, Gaji da kowa da kowa?”
” Kowa lafiya lou, duk suna gaishe shi.”
” Ina amsawa, amma zasu zo su dubani ai ko?”
” Eh toh nasan zasu zo, dan baki ga ma fad’an da Umman tayi
ba, kwana uku a asibiti baku fad’a ba.”
” Ina na sane, hankali na baya jikina, laifin D-D ne, shi
ne be fad’a ba wallah. Anty Saliha ma baki ga fad’an da tayi ba.”
” Ai dole, wani abun kana bukatar Babba kusa da kai.”
“Aikuwa.”
” Allah ya kara sauki ya kiyaye gaba.”
” Amin addu’ar kenan.”
” Sai naji labari kuma, Ashe su Abba sun fara maganar ku,
Umma tace min ma ke kamar su abba sun gama bincike akan shi har ma sun tabbatar
da shi din zasu bawa, Umma tace bata taba ganin Abba ya damu da wani a cikin
masu zuwa neman yayan gidan ba kamar yadda ya damu da wannan din, ko dai wani
Babban kika samo mana ko wani basarake?”
Tace cikin zolaya
” Kai Ya Maryam, bafa kowa bane hasalima dai ba wani me
kudi bane kawai dai inaga ko Abba ya gamsu da halayen sa ne.”
” Eh toh haka ma Umma tace, nima tsokanar ki nake, ke yanzu
ka samu miji na gari me son ka me son farin cikin ka shine, ba yalwar arziki
ba, da wani arzikin gwara rufin asiri.”
” Haka ne.”
” Allah ya kaimu lokavin, musha biki.”
Dariya tayi kawai dan ita jikinta a sanyaye yake da rashin jin
sa har tsawon kwanaki hudu, ta damu sosai sosai har ta kan zauna tayi ta tuna
moments din da sukayi tare, wani lokacin tayi murmushi ita kadai wani lokacin
kuma ta ji kunya ta kamata.
_”I love you.”_ Kalmar da yadda ya fade ta take ta
tunawa, har yadda lips dinsa suka hade waje daya yayin da yake furtawa, cikin
muryar da take yawan yi mata amsa kuwwa a cikin kunnenta
“Dan Allah dafa min danwake, shi kawai nake sha’awa baki na
babu dadi wallahi.”
Maryam ta katse mata tunanin da take, ajiye wayar ta tayi a
gefen Maryam din, ta tashi zuwa kitchen din, minti kad’an ta leko
“Toh ai bansan Ina kayan naki suke ba.”
Tasowa Maryam din tayi, tazo ta dauko nata komai ta nuna mata
sauran sannan ta dawo falon ta jona wa Iman din wayar ta a charge kusa da ita
ta kunna tv ta koma ta zauna tana kalla, jefi jefi tana yiwa Iman din hira daga
nan.
Wayar Iman din ce tai
kara, alamar shigowar kira, tana daga kitchen din amma sai da ta ji gabanta ya
fadi, saboda tsabar jiran kiransa har ringing tone ta chanja masa nashi shi
kadai saboda da ya kira yadda zata fi saurin ganewa,
“Ana kiran ki Iman.” Maryam tace tana jawo wayar ta
kalli screen din
“M ne yake kira, M M M waye Ma? Sirikin nawa?”
Tace tana murmushi, maimakon Iman din ta fito ta karba sai kawai
ta cigaba da aikinta tana jin Maryam din na mata sababin zata katse, kamar ba
kiran da take jira bane, amma kuma a kalla yanzu hankalin ta ya kwanta, tasan
cewa da gaske be manta da ita ba. Sake kira akayi karo na biyu,
“Bana son wulakanci Iman, bari na daga kizo ki karba.”
Dagawa tayi ta saka a kunne
“Sweetheart.”
Ya furta cikin rada yana sauke ajiyar zuciya, da sauri Maryam
tayi gyara murya tana cire wayar kafin ta mayar tace
“Yayarta ce maryam, tana kitchen ne.”
“Anty Maryam, Ina wuni?”
“Lafiya lou wallahi, ya aiki?”
“Alhamdulillah.”
“Dama tana kitchen ne, amma yanzu zata zo zata kira.”
“Owk nagode sosai.”
“Nima Nagode.” Ta katse kiran tana tashi, zuwa tayi
kitchen din da daddage da d’aka mata duka a baya
“Dan wulakanci kina ji yana kira ko? Wannan irin hot guy
din ba’a musu jan aji wallahi, kinji kuwa? Haka yake kashe ki da soyayya? Hmmm
lallai yau ga wanda yafi D-D na.”
Banza Maryam din tayi mata tana murmushi, ta karbi wayar ta
ajiye a gefe ta karasa kwashe danwaken ta zuba a flask ta zuba ruwan zafi akai
ta rufe, ta soya man ta hada komai a babban tray ta dora Maryam din na tsaya a
akanta tana mata hirar Moh din ita a dole sai taji wani abu daga iman din amma
tayi mata fumfurus
“Mara lafiya ba’a cika son shi da yawan magana ba, muje na
kai miki abincin falo.”
Dukan ta kara kai mata ta goce tana dariya, suka jero Maryam din
na rik’e da bottle water ta ajiye mata komai a falon ta zuba mata sannan ta
dauki jakarta tace
“Ina ne dakin?”
Da baki Maryam din ta nuna mata lokacin ta cika bakin ta da dan
wake. Dakin ta nufa ta shige ta rufo kofa sannan ta cire hijab dinta ta ajiye a
agefen gadon ta zauna tana kallon wayar, kunya da nauyin kiran sa take amma
kuma tana bukatar kiran nasa, tayi missing dinsa da muryar sa gaba daya. Kiran
nasa tayi tana tashi tsaye lokacin da ta soma ringing, be daga ba, amma kuma
tana katsewa ya biyo kiran a take.
“Assalamu alaikum.”
Tayi sallama wayar a hannun ta bata saka a kunne ba
“Wa alaykisalam.”
Ya amsa sai yayi shiru, itama shirun tayi tana saka abinda zata
ce
“Shine baka kirani ba?” Ta samu kanta da fad’a ba tare
da tayi tunani ba. Abinda dama yake son ji kenan, tayi missing dinsa in dai har
tayi korafi akan rashin kiran, murmushi yayi wanda taji sautin sa ta cikin
wayar
“Kinyi kewa ta kenan ko?”
“Um um.” Tace da sauri
“Kawai dai na kikkiraka bata shiga, kuma Abba ya bani sako
shine kawai dama.”
“Ohh, sakon Abba ne yasa kika kira ni ba don kinyi kewa ta
ba?”
Shiru tayi dan a zahirin gaskiya ba hakan bane, tana bukatar ji
daga gareshi, tana bukatar comforting words dinsa, tana bukatar shi kawai ma in
short.
“Ni kuma kinga nayi kewar ki, sosai sosai komai ma da nake
anan din yinsa kawai nake ba don naso ba, kiyi hakuri kin kirani, ina wajen da
dole na kashe waya, shiyasa har kika jini shiru haka.”
“Ok.” Tace a ba tare da tasan me zata ce ba
“Ya gida ya kowa da kowa?”
“Alhamdulillah, yasu Ammi? Ka samesu lafiya?”
“Lafiya lou, banje gida ba, yau nake shirin zuwa in sha
Allah.”
“Ok tam, karka manta ka gaishe ta.”
“Ba zan manta ba, zance mata sirikarta na gaishe ta, zan
kira sai na bata kuyi magana.”
” Um um ba zan iya ba.”
” Kunyar ta kike ji? Irin kunyar surkutan nan ko?” Ya
kyalkyale da dariya
” Ni dai bance ba.”
” Ni kuma nace.”
” Uhum.”
” Wacece Maryam?”
” Yayata ce da akayi bikin su, nazo gidan ta bata da lafiya
zan kwana biyu na dan taimaka mata.”
” Owk ayya, ki duba ta, Allah ya bata lafiya.”
” Amin zataji.”
” Baki fad’a min ba, me Abbanmu yace?”
” Na zata ba zaka tambaya ba ai?”
” Na isa? Ina sane kawai dai.”
” Dama cewa yayi, a turo.”
” Me!!! Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah! Kina
nufin Abba yace na turo magabatana ayi magana? Kenan Abba ya yarda ya bani ke?
Kai mAsha Allah, Alhamdulillah.”
” Wannan murnar haka.” Tace cikin mamaki
” Ba zaki gane ba, ba zaki gane ba Zahraah, Nagode sosai,
Allah ya sakawa da Abba da alkhairi. Nagode nagode, wannan ranar ta shiga cikin
ranaku masu matukar muhimmanci a tare dani, Alhamdulillah.”