HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

” Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

 

” Amin Zahra nah, Amin Amin. Bari kiga na tashi, banga ta
zama ba a yau zanje na same su da maganar, in sha Allah a kwana daya zuwa biyu
magabatana zasu zo, ayi komai a gama, Allah yasa Abba ya saka mana lokacin
kankani, bansan irin farin cikin da zan ba, Alhamdulillah.”

 

” Uhum.” Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da
yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun tana yar kankanuwar ta.

 

” Zan kiraki anjima, ki kula da kanki.”

 

” In Sha Allah. Ba-bye.”

 

Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci

 

” Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka
tabbatar mana da alkhairi.”

 

Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki.

 

***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan
karon shigar da yasan Bubu yafi so yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi
masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun
kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan
karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi
korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce
me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a
duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take
masa komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi
bayan sa ba.

  Sai da ya gama mata
shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a
nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta
dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma
dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni
labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin
sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan
sarauta!

 

***Abba na zaune ya gama karatun alkur’ani me girma Maman ta
shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar be ganta ba

 

“Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan
ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu.”

 

Daga mata hannu yayi

 

“Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki
ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba, shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi
muku.”

 

“Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah
zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu lafiya lou.”

 

“Allah ya taimaka.” Yace yana kokarin mikewa

 

“Dama magana nazo muyi, gida zanje.”

 

“Allah ya tsare hanya, ya kiyaya” yace kawai cikjn
halin ko in kula

 

“Kwana uku zuwa sati nake son yi.”

 

“Duk yadda kika ga yayi miki.” Ya karasa ficewa. Kwafa
tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba zata hana Zeenat abinda take
so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.

1/12/22, 08:56 – Buhainat: Halin Girma

    12

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

 

***Kai tsaye ya wuce zuwa chan gaban Bubun, fadawa na aika masa
da kikari, kirarin da yake jin sa har cikin kansa, sai dai baya taba bari yayi
tasiri a gareshi, hasalima yi yake tamkar be san me suke cewa ba. Dukawa yayi
kamar yadda yake a al’adah ya gaida Bubun, ya amsa masa da ka ba tare da yace
komai ba, a irin wannan zaman Bubun baya magana sai ta kama, sanin haka ne yasa
Muhammad din ya koma daga bangaren dama ya zauna kafin sauran yan fadar su
shiga kawo masa gaisuwa. Amsawa yayi duk a jimlace, ya hakimce a gefe yana
sauraron  zaman yake wakana. Kasancewar
zaman na gab da tashi ne yazo, shiyasa yayi tunanin ba za’a wani ja lokaci ba,
sai yaga an dauki lokaci ana maimaita abinda aka fad’a a baya, ya sani sarai
hakan tsarin bubu ne, kila kafin ya iso ya shirya hakan saboda shi, murmushi
yayi yana satar kallon Bubun da shi din ma shi yake kallo. A karon farko yaji
tausayin mahaifin nasa ya kamashi, yadda yake kokarin ganin ya damka mulkin a
hannun sa bayan shi kuma bashi da ra’ayin hakan, amma kuma be tursasa masa ba,
ya cigaba da bin sa a hankali zuwa lokacin da yake ganin ya dace.

   Be san ta yaya zai
fahimtar dashi ba, amma yana da dalilin sa babba da ya saka shi tsayawa akan
bakan sa, akwai babban kalubale a gabansa idan har ya amince da muradin Bubun ,
amma ta yaya zai iya gujewa hakan? Bayan babu wanda yasan dalilin sa?

   Yana jin sanda zaman ya
kare, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi ya daga idon sa sama yana kallon tsaruwar
fad’ar, komai na ciki me tsada ne da kawa, haka duk wani abu da yake ciki me
muhimmanci ne ga masarautar.

  Tunanin Bashir ne ya
fado masa, da ganin da yayi masa da fitsararriyar yarinyar nan, Bashir yana
direbobin Masarautar Kano wanda ya sanshi sosai saboda kaudin sa da hayaniyar
sa, kafin ya auri wata mata wadda ake kyautata zaton auren jari yayi, tun daga
lokacin kuma ya bar masarautar sai jefi jefi yakan je ya gaida Fulani idan ta
kama. Yayi mamakin ganin sa da zabgegiyar mota amma da ya bincika ya gane
komai, sai yaji hakan yayi matukar yi masa dadi, yayi Kuma daidai da tsarin da
yake son dora su akai.

   Dawowa yayi daga
tunanin jin kamar an taba shi, ya kalli wanda ya taba shin sai ya fad’ad’a
fara’ar fuskar sa,

 

“Aji!”

 

“Tunanin me kake haka Muhammad?”

 

” Babu komai, mun same ku lafiya?”

 

” Lafiya lou, ya aikin? Amma kazo kenan ko? Zaka
dade?”

 

” In Sha Allah!”

 

” Sannu da zuwa.” Yace yana mikewa

 

” Zuwan ka dana ji ne ya sakani zuwa , Ina fatan idan ka
huta zaka shigo, akwai batutuwan da nake so mu tattauna.”

 

” Muje na taka maka, dama nima akwai maganar da nake so
muyi.”

 

” Toh toh madallah.”

 

” Muhammad.”

 

Bubu ya kira sunan sa yana daga zaune

 

” Na’am Bubu!”

 

” Naji dadin ganin ka da shiga irin wacce ta dace da kai,
Ina fatan dorewar hakan.”

 

” In Sha Allah Bubu, zan kokarta.”

 

” Madallah da kai.”

 

” Allah ya kara girma.”

 

Tashi yayi suka fice tare da Aji, hannun su cikin na juna,
Maimartaba ya jinjina kansa yana mamakin tarin kaunar da suke wa juna, har suka
bacewa ganin sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tafiya tunanin abubuwan da
aka tattauna don cigaban al’umma. Sai dai yana fara tunanin, tunanin ta ya
shigo ya katse masa duk hanzarin sa, ya rasa dalilin da ya saka a duk sanda ya
tuna da maganar yake jin duk wata walwalar sa da farin cikin sa ya ragu,
musamman a dan tsaikon nan, sai yake jin tamkar ana dakatar dashi da yin wani
yunkuri. Shi din mutum ne me riko da addini matukar gaske, baya taba bawa
maganganun da za’a zo a fad’a masa muhimmanci ko kad’an, sai dai a duk abinda
ya shafi Muhammad baya wasa, yana ji a ransa kar fa abinda tsohuwar matar ta
sanar masa ya zama gaskiya, tsoron hakan ya hanashi gabatar da komai cikin
sauri yake bin komai a hankali, ba kuma wai dan ya gasgata maganar ta dari bisa
dari ba, sai dan yana ji da tsoron sharrin masu sharri, be san me suke shirya
wa dan nasa ba, sai dai be gaza ba, babu dare babu rana kullum cikin nema masa
kariya yake a wajen ALLAH, ko ma menene tabbas zai zo masa da sauki.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button