HALIN GIRMA 11-15

***A falon Ajin ya same
shi yana zaune fuskar sa kamar gonar auduga, da kansa zai je amma sai Bubun
yace ya bari yazo kawai ya huta. Bayan ya zauna ne fadawan suka fice suka jawo
musu kofar.
“Na matsu na sanar da kai wannan albishir din, abinda muka
dade muna jira ne, Muhammad dai yazo da magana, har yana neman aje ayi masa
tambaya!”
Fuskar Bubu ta fad’ad’a,farin ciki ya mamaye shi
” Masha ALLAH! A kanon ne kamar yadda Takawa yace?”
” Eh har binciken da mukayi, nan din ne in Sha Allah.”
” Sai a sanar wa Takawa babu jira, in Sha Allah gobe duk
abinda ya kamata ayi sai ayi, jibi sai aje musu da magana, da tsayayyiyar rana
domin Takawa ya bukaci ayi komai a cikin kankanin lokaci.”
” Madallah…Hakan yayi.”
Tattaunawa suka shiga yi har dare yayi sosai,kafin ya koma
bangaren sa cikin jin dadin labarin auren Muhammad din.
***Jifa tayi da kofin hannun ta, ya fashe a wajen gaba daya
kwalbar ta wawwatsu a dakin, wani irin bakin ciki take a duk lokacin da taji wani
abu da ya danganci Muhammad din. Yau Itace a turakar Bubu amma tasan ba zata
taba samun kansa ba, idan ma ta zafafa zai iya cewa ta bar masa dakin shiyasa
ta yanke wa kanta hukuncin ko da yadawo daga wajen Aji ba zata je ba zatayi
zaman ta tayi tunanin menene mafita a gareta.
“Ranki ya dade, Yarima Muhammad yana waje yana neman
iso.”
” Uban me zai min!!”
Ta daka mata tsawa tana huci, sai kuma ta hau kokarin daidaita
kanta
” A shigo dashi babban falo gani nan.”
Da sauri baiwar ta fice tana mamakin uwar dakin nata.
Zaman sa yayi yana karewa falon kallo, an sabunta komai ba kamar
zuwan sa na karshe ba. Murmushi ne a fuskar sa, yana da yakinin bata da bukatar
ganin shi, ko da gilmawar sa ne balle har ya kai ga zama a falon nata, yana
sane yazo domin ya kara tabbatar da abinda ya sani tun tuni.
A yadda ta fito, da
yadda ta zauna kadai ya isheshi amsar abinda yazo nema, yana kallon yadda take
satar kallon sa cikin kallon da yasan na tsantsar tsana ne tun da ya riga da ya
dade da sanin bata kaunar sa ko daidai da minti daya ne
” Barka da gida, mun sameku lafiya?”
Ya fad’a da yanayin da yasan zai sake tunzura ta.
” lafiya, ya aikin naku?”
“Babu dadi, na gudo ma na dawo gida cikin yan uwa!”
“Ka kyautawa kanka.” Tace a gajarce
Mikewa yayi yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa, ya yi mata
kallon cikin ido tace
“Bari na koma.”
“Baka Sha ko ruwa ba.” Tace tana daga zaune
“Na yafe, bani da bukata.”
Ya dage gira yana juyawa,
da kallon bakin ciki tabi bayansa har ya fice daga falon, ta yarfe hannunta
tana jin kamar ta kamo shi ta tayi ta jibgar shi har sai taga ya daina motsi.
“Ciwon Ido, zanyi maganin ka!” Ta furta tana tashi ta
koma ciki
***Daga nan bangaren Ammin sa ya wuce, yana jin kansa kamar
sabon ango, farin ciki yake ciki shiyasa ma be wani damu da abinda ya faru ba.
Dama yasan kafin ya isa ta samu labarin ko ta wajne Hajja ko Bubu, aikuwa yana
shiga ta tare shi da murnar ta, ya zauna ya tankwashe kafarsa a gabanta tana
jin yadda take lissafo masa abubuwan da za’a bukata na zuwa gidan su
Fatiman. A farkon farko be so wani abu
na sarauta ya shigo ba, amma kuma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba, shiyasa
yayi amfani da damar nan wajen hadawa Mama gadar zare, dalilin tafiyar ta da
shine ya assasa bayan ya kira Khalil a waya ya karanta masa yadda duk yake so
ayi, babu musu ya amsa kuma ya tabbatar masa da zai yi komai daidai. Dazu Kuma
ya kira shi ya tabbatar masa da Maman ta iso tun wayewar gari. Da wannan ya yi
gaba wajen aiwatar da saura shirin sa da ya tabbata zasu yi matukar girgiza
kowa ba Maman kawai ba.
Har dare sosaii yana
shashen Ammin, ta hada komai abubuwan da ya tabbata zasu dace da tsarin fatimar
sa, shi din ma akwai tanadin da yayi mata amma ba yanzu ba, sai ranar da dubban
mutane suka shaida, ya zama ita ta zama shi, a ranar zai nunawa duniya kalar
gatan da take dashi a wajen sa.
Da sassarfa ya karasa
part dinsa, Kai kace wani uban aiki yayi saboda yadda yake jin sa a gajiya.
Kwanciya kawai yayi bayan ya aika mata da cool night text message ya kashe
wayar sai bacci, baccin da yake yi a duk lokacin da ya samu kansa a dakin sa na
cikin gidan.
Zai iya cewa ya jima
beyi bacci me dadin na ranar ba, ko dan abinda ya faru a ranar ne? Ko Kuma dai
dan ance gida daban yake, dama bahaushe na cewa kowa ya bar gida… wanka ya
soma yi, ya fito domin ya karya dan yasan komai na kammale a ajiye yana jiran
sa. Zaman karyawa yayi, yayi dialing number dinta yana kallon plate din da ake
zuba masa abinci, da hannu yayi masa alamar ya isa, ya karba ya soma ci jin
bata daga ba, a yar mu’amular da yayi da ita, ya lura tana da bawa kowanne abu
muhimmanci idan har shi ta saka a gaba, misali idan tana aiki takan ajiye wayar
ta waje daban ta kammala aikin, haka idan tana wani muhimmi abun bata hada shi
da komai har sai ta gama. Tunanin sa ne ya katse lokacin da kiranta ta ya shigo
nasa. Murmushi yayi yana jan tissue ya goge bakin sa, yayi rejecting kiran
sannan ya bi bayan yana kishingid’a a jikin lallausan tumtum din dake kusa
dashi.
Da sallamar ta, ta daga
kamar ko wanne lokaci, ya amsa mata shima kafin ta dora da gaisuwa
“Ina kwana?”
“Lafiya lou, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lou, yasu Ammi? Ka same su lafiya?”
“Kalou kowa, ya sister Maryam da jiki?”
“Gata ta samu sauki, inaga ma na tafi gida tunda naga ta
warke sosai. “
” A ah kiyi zaman ki! ” Yace da sauri
” Me yasa? “
” Amm kin gane, kinga tana bukatar ki, ki dan kara mata ko
da kwana biyu ko uku ne, zata ji dadi. “
” Owk tam. ”
” Yawwa. “
” Ina kika shiga dazu na kira no answer, kitchen? Ko shara?
“
” Ya ka sani? Ina kitchen. “
” Na sanki ai, nasan bakya wuce wuraren nan biyu. “
” Lallai, kasan abubuwa da yawa akaina, amma ni bansan
komai ba. “
” Zaki sani, karki damu zaki sani fiye da sanin da kowa ma
yayi min. “.
Ya karashe maganar cikin
sigar tsokana, bata ce komai ba, yasan kuma ba zata ce din ba, shima ba dan
tace wani abu yayi maganar ba
“Zan zauna takanas, kiyi min duk tambayoyin da zaki yi min,
zan amsa, amma kafin lokacin ina so ki san, nifa soja ne!”
“Soja!” Tace gabanta na faduwa sosai, bata son aikin
soja ko miskala zarratin, bata kuma taba tunanin auren soja ba, dan tasan yadda
suke very busy da aikin su
“Eh ni soja ne, amma fa irin kurtun nan.”
“Soja dai ai duk soja ne, sunan daya ne.”
“Amma rank din daban daban ba.”
“Uhummm. ” Ta ja ajiyar zuciya, ya sammace ta, kenan
dai zaman kadaici be rabu da ita ba, dan sojoji basu da lokacin kansu balle na
matan su, yanzu ita kenan…
” Karki damu, ba zan dinga nisa ba kinji? Zan zama ko yaushe
kika bukace ni Ina kusa, nayi miki alkawari.”
“Allah yasa, dan da gaske bana son aikin soja
wallahi.”
“Saboda me? Aikin taimakawa kasa ne fa, aikin lada ne idan
har ka yi yadda ya dace.”
“Na sani, ni kawai bana so ne, basu da time din kansu ballanta
na …”
“Na matan su? Haka ko yaushe aka cewa dama, toh ni dai Ina
da time dina Ina kuma da na matata, har sai kin gaji kin koreni daga gidan ma
wataran.”
“Shikenan.”