HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

“Zaki gani ai, ki zuba ido.”

 

Shigowar Ya Maryam ya sakata yin shiru

 

“Ki fito falo ya tafi wallahi, ni kadai kamar mayya.”
Tace mata tana rik’e kofar, tun dazu tace tazo falo taki sboda maigidan yana
nan, shiyasa Maryam din tazo kiranta da ya tafi, ko yar hira sa yi

 

“Kice ina gaishe ta, ya jikin nata.”

 

“Da sauki.” Tace tana janye wayar daga kunnenta.

 

“Ashe waya kike shine kika yi luf, toh ki gaishe shi, in
kin gama Ina jiran ki.”

 

Ta fita ta ja mata kofar

 

“Bari na barki kuyi hirar ku, zan sake kira anjima.”

 

Kamar ta tambaye shi maganar zuwa gidan amma ba zata taba iyawa
ba, sallama tayi masa ta ajiye wayar ta fita wajen Maryam.

 

 

Yana sane sarai yake ce mata komai, baya so tasan komai sai anyi
komai ya kammala, ba zai ma gaya mata zuwan nasu ba, Abba kawai zai wa text ya
sanar masa, idan yaso sai ya turo Musaddik ya sameshi ya sake fad’a masa Incase
ko be ga message din ba. Haka kuwa akayi, yana masa text din ya gani, yayi
saurin kiran kowa ya sanar dasu zuwan bakin, anan suka fara tunanin abinda ya
kamata suyi, baki daga irin wannan babban gidan dole ne ayi abinda za’a fita
kunya. Sun dade suna shawarwarin su kafin su tsaida matsaya, nan da nan suka
shiga shirin tarbar su cikin tsarin da suka san ba zai zama wani iri ba.

 

Abba na zaune kiran Mama ya shigo wayar sa, shi kadai ne a gidan
sai Habib ta tafi da Zeenat da Marwan, shiru gidan babu kowa kallon tv yake a
zahiri amma a badini tunanin masu zuwa neman auren Iman yake a gobe, yaso ya
sanar wa mahaifiyar ta zuwan nasu da komai akan maganar sai dai baya samun ta a
waya wajen kwana uku kenan, yasan tana business sosai kamar ma tana fita
kasashe saro kayayyaki shiyasa yayi tunanin ko kila bata k’asar ne.

   Kallon wayar tasa yayi,
har lokacin haushin Maman yake ji musamman abubuwan da ya gano akan irin rikon
da tayiwa Fatiman tsawon lokaci be gane komai ba, har Marwan ya titse ya
tambaya ya kuma gaya masa komai abinda ya sake daga masa hankali sosai kenan.
Kiran ne ya sake shigowa ya daga ba dan yaso ba, dan dai kawai be san ko wani
abu bane emergency ya taso, sallama tayi ya amsa ciki ciki. Dama tasan za’a
rina shiyasa kawai ta tafi kai tsaye akan dalilin kiran

 

“Dama Zeenat ce ta ce na sanar da kai iyayen Bashir zasu zo
gobe idan Allah ya kaimu.”

 

“Su bari jibi gobe Yaya yana da abinda zai yi.”

 

Yace mata kai tsaye

 

“Amma da ka barsu sunzo goben ba dole sai wajen Yayan ba
ai.”

 

“Haka tsarin mu yake tun farko, babu Kuma dalilin da zai
saka na chanja yanzu dan anzo auren nawa yayan, idan har ba zasu iya bari sai
jibin ba sai ki nema musu wanda zasu gani a goben.”

 

“Abin be kai haka ba ai, Allah ya kaimu jibin.”

 

“Amin.”

 

 Yace ya katse kiran yana
Jan tsaki, wato duk dadewar ka da mace ba zaka taba sanin wasu daga cikin
halayen ta ba har sai abu ya faru, lallai. 
Shi kadai yake ta wannan tunanin har lokacin da zai kwanta yayi, ya
kwanta da addu’ar Allah yasa komai ya tafi dai-dai goben.

 

***Duk cikin su babu wanda ya makara, suka tashi aka hau
gaggayara gidan harabar da lungu da sako su Habib suka taimaka aka tsaftace ko
ina, dama dai a gyara yake saboda takanas aka dauki me aikin kula da wajen amma
duk da haka idan suka tuna bakin da zasu zo sai suga ya kamata a sake gyara ko
ina.

   Wajajen sha biyu cikin
jagorancin Musaddik suka iso, cikin manya manyan motocin alfarma da aka rubuta
Emir Kano 1 guda biyu sai guda biyu dauke da tambarin Adamawa Palace.

  Cikin kankanin lokaci
unguwa ta dauka, mutane suka dinga lekowa daga gidajen su dan tabbatar da
abinda yaran su suka je suka fad’a musu, kowa ya leko sai ya rik’e baki cikin
tunanin abinda ya kawo irin mutanen gidan.

   Cikin matuakr girmamawa
Abba suka karbe su, sai dai sunyi tunanin zasu gansu a matsayin mutanne da basu
kai ba ko kuma level dinsu ba daya ba, amma sai suka ga akasin haka, cikin
girmamawa, karamcin da dattako suka zo musu, suka nuna Halin Girma, halin
babban gida babu fariya ko nuna su din wasu ne, cikin tattautasa harshe da
girmamawa suka nemarwa dan su kuma jikansu Muhammad auren Fatima. A take Abba
yace an bashi. Su kuma nan take suka gabatar da ranar da suke so a saka, babu
musu nan ma Abba ya amince suka tsaida wata daya kachal, shi din ma saboda
Muhammad din ne ya bukaci haka, amma idan sune toh sati biyu zasu saka.

  Babu wani bata lokaci
abinka da manyan mutane, masu Halin Girma, suka yi komai cikin sauki sannan da
zasu tafi suka gabatar da kyaututtuka daga iyaye da kakannin Muhammad din da
yake cikin al’adarsu idan za’a zo neman auren. Tarin kayan da suka kasance mota
guda sai da suka bawa su Abba mamaki, a gefen Abba aka ajiye mukullin motar
nufin su har da motar da duk abinda yake ciki kyauta ce ga sirikar Sarki Ahmad
Santuraki, da iyalan gidan sa kafin zuwan ta, sannan suka yi musu sallama suka
tafi.

 

 

#HafsatRano

#ZafafaBiyar2021

Not edited

Ignore typos

 

 

 

 

Masu sharing sannun ku da kokari kunji? Allah ya shirye ku idan
masu shiryuwa ne, idan kuma ba masu shiryuwa bane toh… Kun san sauran dai😀

1/12/22, 21:41 – Buhainat: Halin Girma

    13

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

 

 

***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da
abinda yake cin sa a zuciya. Tabbas sun amsa sunan babban gida, haka sun nuna
Halin Girma da dattako na irin manyan mutane da suka san mutunci da yakana.

   Fadar irin tarin kayan
da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a zuciyar Abba,
yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin
tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su,
sai dai dole ne suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman
din ne, tun daga kan sutura zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai
tamkar ba’a san darajar su ba.

   Haduwa suka yi suka
tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta zama ta rashin
tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin
baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan
sa har wasu dake waje su samu damar aiwatar da mummunan kuduri akan su.

  Tabbas shawarar tayi dan
da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa kawai a take aka
fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe
kafin bikin yazo kusa sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta
tafi dasu tunda dama su chan babu wani tsoron rashin tsaro ta ko ina zagaye
suke da Jami’an tsaro. Karshen magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne
tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar suka tashi bayan Abba ya sanar musu da
zuwan iyayen Bashir a gobe kamar yadda Mama ta shaida masa.

  

Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin
sa’a kuwa kiran ya shiga, bata wani jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin
sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum a bakin Iman din, maganar da sak ta
mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa yake jin ba zai iya
mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a
tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko
babu, a dai kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da albarka Yaya a
tsakanin su.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button