HALIN GIRMA 11-15

“Ina wuni Abban Iman?” Ta gaishe shi jin yayi shiru
bayan amsa sallamar ta
“Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?”
“Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?”
“Tana nan lafiya.”
Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine
ya katse shirun ta hanyar cewa
” Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari
idan auren ta ya tashi, ta samu miji har an tsaida rana wata daya, in sha Allah
a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a matsayin ki na mahaifiyar ta
sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!”
Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da
zata yi aure, rayuwa na gudu sosai, tana tuna lokacin da ta dawo masa da ita,
da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta wanda bata taba tunanin zata
dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take rayuwarta ta kare
gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da zata
fito ta fadi bata tuna yar tata ba, amma ya zatayi? Mutane na fifita al’ada
akan addini. Ta sani sarai uwa ce taka da ikon rik’e yarta har zuwa aurenta,
tare da sharadin kula da duk wata bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan
anji tsoron tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh amma a lokacin wa take
dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin gatan ta
sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai
karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta
kuwa, duk yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik’e ta a wajen ta. Ta bata
kulawa da dukkan gatan da take bukata.
“Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin.”
Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma
ya cika alkawarin sa, zatayi kokari a dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta
da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata
kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya
sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum
ne shi na gari, me kirki da son iyalin sa.
Bayan gama wayar da
sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan
Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban
tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani
Babban tashin hankali a gaba.
Kiran nata yayi, tana
dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama
dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar
gidan.
“Abba na fito.”
“Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na
mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki abinda zai cutar dake ba, ba
kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da
Bashir ki kawo wani ba shi ba,nayi miki
alkawarin tsaya miki kinji?”
Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi
Abban ya dawo da shi yana kuma kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.
” Kina jina zeenatu?” Ya sake fad’a cikin yanayi me
wahalar fassarawa
Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace
” Dan Allah Abba kayi hakuri?”
“Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema
a matsayi na, na mahaifin ki.”
“Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da
Bashir ba.”
Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga
karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu babbar jarrabawa irin yayanka
suyi rashin sa’ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida
akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa
tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma
yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take so shi Maman take goyan ba, dama mafiya
yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra’ayin yarta.
“Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da
kowa, ki kuka da kanki.”
“Abba dan…” Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan
kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda ya dace, a kalla ta yi
kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya
sakko.
“Lafiya?” Mama tace tana kallon ta.
“Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?”
Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja
“Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi
miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?”
Kanwar Maman Atika ta fad’a cikin bacin rai
” Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda
mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana? Iyaye maza sun fi mu tunani da
hangen nesa.”
“Toh Atika ya za’a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da
be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar lelen tasa ta samu, shikenan
kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga
wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita
kuma na tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta.”
“Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din
hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata ace kin bashi dama kinji ta bakin
sa akai.”
“Kyale shi kawai, zai sakko ne.”
“Me yace miki?” Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be
dameta ba.
“Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir.”
“Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na
mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya Hajara kinsan da matsala.”
” Me kika ce masa ke kuma?” Taki amsa atikar ta
tambayi Zeenat din.
” Hakuri na bashi.” Tace tana rakubewa a gefen Hajiya
da tunda aka fara maganar bata saka musu baki ba sai lokacin
” Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi
namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen nesa.”
” Hajiya toh ya za’a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula
kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin ma ta samu saurayin su fuskanci
juna a zo maganar aure.”
” Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi
inda zai Sha wahala.”
” It’s better to marry late than to marry wrong.”
Atika tace tana girgiza kafarta
” Khair in sha Allah, babu abinda zai faru.”
Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya
dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda Abban ya kafe ta tabbata akwai babban
dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin
samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya
mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman
auren babban gida ita kuma Zeenat din na zaune a gida.
***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi
sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar
part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso
ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau
cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu
feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai
lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da boxer kasancewar zafi ya
fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.