HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

“Gani fa ga mutumin ka.” Musaddik yace yana dagawa

 

“Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video
Call.”

 

Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar
Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana
durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi
kawai yace

 

“Oga Bashir barka da warhaka.”

 

“Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan
gidan da kaje Neman aure bane nima naje, wallahi kuskure ne kawai amma kayi
hakuri.”

 

“Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai,
kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama yan uwa tunda zamu auri yan
uwa.”

 

“Tuba nake ranka ya dade!” Yace yana kasa da kansa

 

“Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na
baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan har kayi min yadda ya dace akwai
babban tukuiwaci.”

 

“Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko
menene .”

 

“Yaushe za’a je tambyar maka auren?”

 

“Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa
wallahi.”

 

Girgiza kai yayi

 

” Ba za’a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu
wata daya!”

 

” Wata daya!” Ya zaro ido

 

” Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai
bana son na rasata ne.”

 

” Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun
daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai kawai kayi duk abinda nace
kayi.”

 

Dukawa yayi jiki na rawa

 

” Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace,
ba zan yi komai ba sai da sanin ka.”

 

” Good, yanzu aikin me kake?”

 

” Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya
tashi.”

 

Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son
zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu
gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious.

 

” Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik,
bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi cikin tsari , Ina so gobe ka
dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai
sake goge shakku ko wani tunani akanka.”

 

” Nagode ranka ya dade, nagode nagode.”

 

” Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko
kadan!”

 

” Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka.

 

Daga masa kai Moh yayi sannan yace

 

” Guy!”

 

” Yeah Captain!” Musaddik yace yana matsawa daga wajen
da Bashir din yake

 

“Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa
ba, amma dai bana so a samu matsala har zuwa ranar daurin auren, watch him and
report anything da be maka ba.”

 

“Karka damu, babu ma abinda zai faru. “

 

” Yau nayi zaman fad’a, kamar nayi kuka wallahi, wannan
yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce makwafcin sa kaza, wannan suzo
maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa,
maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya
zaman da zan Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. “

 

” Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu
ayi musu yadda suke so. “

 

” Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na
zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci yake siyo ma da martaba ba komai Bubu
zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. “

 

” A harkar me? “

 

” Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni,
kwana kad’an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo I can’t wait. “

 

” Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin
ne ba komai ba. “

 

” Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani
sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji jiki kawai. “

 

” Dan air. ” Musaddik yace yana dariya

 

” Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa
yasan uztaz. “

 

” Nima haka ai. “

 

” Fadawa wanda be sani ba toh. “

 

” Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin
malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane da zata shigo hannun tuzuru irin
ka wallahi. “

 

” Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci
zan.”

 

” Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. “

 

” Musaddik.!!! ” Ya furta da karfi

 

” Sorry sir, angon Fatima. “

 

” Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai
frog jump. “

 

” Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment
din dai Captain. “

 

Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye
lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar gefe ya kwanta dan rama baccin da
Bubu ya katse masa.

1/18/22, 19:54 – Buhainat: Halin Girma

     15

 

_*Zafafa biyar na kuÉ—i ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki
karanta. Muna haÉ—aki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan
cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar
zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

 

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

 

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

 

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

 

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

_________________________

 

•••••••••�

 

Kasa fitowa tayi, tana taraddadin yadda zasu karbe ta, ji tayi
an bud’e kofar bangarenta, taji muryoyinsu a lokaci daya suna mata sannu da
zuwa

 

“Yau ga Fatima,sannu da zuwa dota, sannu da zuwa.”

 

Wata farar mata da a kalla zatayi sa’ar Mama ta fad’a tana riko
hannun ta. Da wani irin yanayi take kallonsu su dukka, kowannen su kokari yake
ya nuna mata kansa, mutum daya dage gefe tsaye ta harde hannayen ta a kirjin ta
ta daga kai ta kalla, tun isowar su wajen ita kadai ce bata yi magana ba. Wani
irin shock taji ta furta Mommy a tsakanin lips dinta, gyada mata kai matar tayi
da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana sakin kuka, bata chanja ba ko kad’an
daga yadda take a hoton ta da take dashi tun na zamanin yan matantaka, duk da
ganin ta da ita a zahiri kadan ne amma ko yaushe zuciyar ta na manne da hoton
mahaifiyar ta.

   Tafi sukaji an saka daga bayan su, duk Kuma sai
suka saka dariya har Iman din da kunya ta kamata ta sake shigewa jikin
mahaifiyar ta tana jin wani irin son ta da kaunar ta.

 

“Muje ciki ko?” Babban namijin ya fad’a yana nuna musu
hanya da hannun sa. Sakin Mom din tayi, matar farkon nan ta kama hannun ta zuwa
ciki hanyar da ta ga sun fito dazun.

   A falo suka yada zango, kowa a cikin su kokari
yake yaga ya nuna mata soyyayyar sa, da kallo kawai take binsu cikin mamakin
dalilin da ya saka basa neman ta tsawon lokaci haka duk kuwa da soyayyar ta da
ta hanga a tattare da family din. Tana da bukatar amsa saboda tasan yadda
kowacce uwa take kulafucin danta musamman ita da aka dauke ta da karancin
shekarun ta, tabbas a farko farko ta kan zo ta ganta tare da wani babban namiji
duk kuwa da karancin shekaru basa barin ta tuna komai amma tabbas ta san anyi
haka kuma Abba da kansa ya kara sanar da ita a wani lokaci da ta tambaye shi.

   Kamar an jeho su suka shigo su biyu, suka yo
kanta da gudu macen ta rungume ta tana sakin ihu, namijin kuma ya durkusa a
kusa da su yana dariyar farin ciki

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button