HALIN GIRMA 11-15

“Welcome sister!” Yace bayan macen ta saketa ta zauna
tana maida numfashi
“Welcome sis!”
Tayi saurin fad’a itama tana hararar sa
“Sannun ku.”
Tace tana murmushi tana mamakin su,
“na riga shi ganin ki, na rigashi yi miki magana dan Allah
ni kadai zaki so kinji? Dama kullum ina jin haushin bani da big sister sai
wannan coconut head din , sai gashi na samu yanzu, I’m so happy wallahi, da
k’yar na bari aka gama islamiyya yau wallahi.”
“Amaani kin cika surutu wallahi, ai sai ki barta ta huta
ko?”
” Tell her Mamma, wallahi kamar na bugeta yau din nan ta
bani haushi.”
” Kaifa ya sunan ka?” Ta tambaye shi
” Amaan.” Amani tayi charaf ta rigashi fad’a sannan ta
dora
“Nice hassana, shine husaini, na girme shi so nice
babba.”
 Â
Murmushi Iman tayi, so adorable yaran,
“Oya ku wuce kowa ya cire uniform dinsa kuzo muyi dinner,
nasan Iman ta gama gajiya tana so ta huta”
Mamma tace tana mikewa
” Zayd, Ya Mubarak dinner na table.”
” Ni sai nace gida gaskiya, I’m full.”
Ya Mubarak yace yana gyara zama sosai. Kama hannun Iman Mamma
tayi, suka wuce dining din tare da Zayd yana mata tambayoyi. Mommy na jinsu
bata saka baki ba, dama kuma ita haka take da kara sosai, komai nasu Itace akai
amma bata taba nuna musu iyaka akan nata, shiyasa suma duk wani abu da ya shafe
ta toh sune a gaba gaba, sai ta koma gefe ta zama yar kallo. Bata da hayaniya
kamar dai Iman koman ta a nutse takeyi musamman kuma abun da ya hadu da arziki
sannan ga ilimi both boko da islamiyya. Kujera taja gefen Iman din da suka bar
mata ta zauna daidai lokacin Amaan da Amaani suka dawo kowa ya sauya kayan sa
zuwa na zaman gida. Amaani na kokarin fara surutun ta suka hada ido da Mommy,
kallon da tayi mata kadai yasa taja bakin ta tayi shiru har suka gama babu
wanda yayi magana.
  Falon suka dawo, a lokacin Ya Mubarak da Zayd
suka yi musu sallama akan zasu dawo gobe kowa da family dinsa, har bakin mota
Mommy ta rakasu ta dawo sai kawai ta wuce dakin ta, ta bar Mamma da yaran suna
hira, ta lura da yadda Iman din ke jin kunya da rashin sabo amma kuma tasan
wace Mamma ba zata taba barin ta ba har sai ta tabbata ta sake dasu, balle uwa
uba iyayen magana su Amaani su kadai ma sun isheta.
  Kwanciya Mommy tayi farin cikin zuwan yarta na
ratsa ta, wayar ta ta dauka ta kira number Abba, lokacin ya gama cin abinci
kenan yana kokarin duba wasu papers dinsa a computer yaga kiran nata, tsaywa
yayi da abinda yake yi ya daga.
“Nagode sosai IB, naga Iman fiye da yadda nayi tunanin
ganin ta, hankali na ya kwanta dan na tabbatar da tarbiyyar ta, kayi ma maman
tasu godiya dan Allah. “
” ‘yaya amana ce a garemu da dole mu kula dasu da tarbiyyar
su, domin dole ne Allah ya tambaye mu a ranar gobe kiyama, banyi komai ba face
abinda ya zama wajibi na.”
Ya fad’a yana jin chan kasa zuciyar sa da zata samu labarin
abinda ya faru a zaman Iman din da Maman daku tabbas za’a iya samun matsala,
abu daya ya hanata yin wani katabus akan maganar Iman din, tabbatar mata da
yayi akan bata da matsalar komai, kuma tana hannu na gari.
  Sallama sukayi ta runtse idon ta, hasashen irin
shirye shiryen bikin da zatayi kawai take, ba zata bari ta koma ba har sai tayi
mata nata kalar gatan da zata tabbatar da ita din yar gata ce.
  Turo kofar akayi, ta daga kai ta kalli Iman din
cikin rakiyar Mamma.
” Sai ki gudo ki bar mu? Gamu toh mun biyo ki.”
” Na zata wajen Hajiya kuka yi ai.”
” Munje chan din ma.”
” Ok.” Tace tana mikewa zaune.
” Bari na duba yaran chan, ina ga daga haka zan kwanta, sai
da safe Iman.”
Murmushi Iman tayi ta amsa sannan mummy tace
“Sai da safe Yaya.”
Fita tayi ta ja musu kofa cike da farin cikin kwanan da ya da
uwar zasuyi yau.
“Dawo kusa dani.”
Dawowa tayi ta zauna daf da Mummy din, ta jawota ta dora kanta a
saman cinyar ta, cikin tattausan lafazi tace
“Kin girma sosai Iman, nayi mamakin yadda kika kara
chanjawa akan last da Dr. Ya tura min hoton ki, amma kuma naga baki da walwala
sosai, ko rashin sabo ne? Ko kuma hakan halitta ne?”
Murmushi tayi me sauti, nutsuwa ta saukar mata, taji da gaske
she’s safe fiye da yadda ta taba ji a rayuwa ta, a hankali ta furta
“Babu komai Mummy.”
“Shikenan, ki kwanta idan kika huta duk maganar da zamuyi
sai muyi kinji?”
Ta shafa kanta tana murmushin. Daga kan ta tayi ta ajiye a saman
gadon ta fita daga dakin. Wajen kayan ta, ta nufa ta ciro wayar ta, tasan ya
mata magana a WhatsApp bata samu sukunin dubawa ba. Misscalls ta gani ta
whatspp call sai messages dinsa da ya turo mata. Sakon ta fara dubawa ta,tabi
kowanne tayi reply ta bar daya da yake tambayar ta size din undies dinta kunya
na kamata. Godiyar kudin da ya bata tayi masa hade da addu’a tana turawa sai
gashi yazo online, maimakon ya amsa sai taga yana kiranta, kasa dagawa tayi
kunyar tambayar da yayi mata na dawo mata
_” Baby menene size din B da P?”_
Haka ya rubuto mata fa, kin dagawa tayi har ta katse ya sake
kira ta kara bari ta katse,
_” Please dan Allah ki daga, kwana nawa banji muryarki ba?
Sam na manta zan iya kiran ki ta whatspp call sai daxu, please ki taimaka ki
daga inaso naji muryar ki wallahi.”_
_” Ni dai muyi chatting.”_
_” Ni dai ki daga, zan sake kira. “_
Kafin tayi reply sai ga kiran sa, ta daga da k’yar tanayin nesa
da wayar. Ajiyar zuciya ya sauke da karfi
” Kin iya rigima wallahi, haka kawai sai anyi punishing
dina ko? “
” Um um. “
“Toh naji, ya hanya? Ya me ya faru?”
Cikin zumudi tace
” Ina cikin farin ciki yau, komai ya tafi yadda ya kamata,
kowa so na yake kamar zai goya ni. “
“Mum fa? “
” She’s just like me, kamar ni take har I don’t care
attitude dinta, amma deep down she’s super happy, na gani a idon ta. “
Dariya ya saka
” Alhamdulillah, nayi miki murna sosai sosai,
Alhamdulillah. “
” Nagode sosai. “
” Yau kwana zakuyi nasan da Mum kuna magana. “
” Anya? Kila ko sai an kwana biyu. “
” Bari ki gani dai. “
” Uhum tohm shikenan. “
” Baki min replying dayan chat din ba, abinda na tambaye
ki. “
Dauke wuta tayi gaba daya kamar bata ji ba, ya sake maimaitawa
yana rik’e dariyar sa, ya gano kunya taji tunda taki daga wayar sa, bata san
halin sa ba lallai, rage murya yayi sosai yace
” Dan Allah ki fad’a min Aunty zata yi min fad’a gobe idan
nace ban tambaye ki ba, dan Allah. ” Shiru tayi masa
” Please ki fad’a min, ko da yake ma zan iya chanka ai,
bari muga… zasu kai size…”
” Innalillahi. ” Tace tana zare wayar gaba daya ta
kashe ta. Tuntsurewa yayi da dariya kamar zai fado daga gado, yayi saurin
komawa chat din ya hau rubuta mata
“Sorry matar Muhammad, daga wasa sai ki yanke min waya? Toh
ai ban gama jin muryar ki ba wallahi.”
Tick daya ya gani alamar ta ma kashe datan gaba daya, gwada
kiran ta yayi aikuwa yaji switch off.
Tsaki taja ta wurgar da wayar , ta rasa me yasa me maxa sam basu
da ta ido, zata dade kuwa bata yi waya dashi ba. Samun kanta tayi da yin
murmushi sai kuma ta hade fuska ta sake jan tsaki. Ya ma bata haushi gaba daya.
Har ta gama shiryawa ta jona wayar a charge amma bata kunna ba
har lokacin Mum din bata shigo ba, gefen gadon ta kwanta cikin lallausan zanin
gadon da yake kamshi sak irin kamshin da mummy din take, tana rufe idon ta, ta
shigo rik’e da cup a hannun ta.