HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 11-15

” Iman, kinyi bacci?”

 

” A ah.” Tace tana mikewa zaune

 

” Yawwa ungo karbi kisha, fresh milk ce nayi miki warming
dinta.”

 

Karba tayi, tayi godiya ta kafa kai ta shanye tas, ta tashi da
cup din rik’e a hannun ta

 

” Ajiye shi anan zan kira azo a fita dashi.”

 

A saman fridge din jikin kofar ta ajiye ta dawo ta zauna tana so
abinda tasha ya dan yi settling a cikin ta.

 

“Zo ki tayani duba wannan kayan.”

 

Tayi maganar tana bud’e profile dinsu a cikin system din,
gefenta Iman ta zauna suka hau duba wasu jewelries, duk wanda Iman din tace
yayi kyau sai tayi starring dinsu, sai da suka gama tsaf sannan suka dawo kan
wanda akayi starring din suka sake fidda guda biyar masu kyau sosai, biyu gold
biyu azurfa sai daya fashion ne daga wani babban company, a take mummy tayi
payment din da komai sannan tace Iman din taje ta kwanta zata karasa wani
aiki.  

    Tana kwanciya bacci ya dauke ta 
dama ta gama kurewa sosai tana lura da Mummy din bata so ta matsa daga kusa da
ita ne. Cikin bacci tayi juyi ta jita a bayan ta, daga nan bata sake farkawa ba
sai da aka kira sallah.

 

***Gaba yayo ya bar su a chan su karasa siyayyar abinda zasu
siya dan yaga abin nasu bana kare bane, a Kano ya dira domin su karasa abinda
zasu karasa da Bashir saboda yadda lokacin yazo sosai. A gidan sa ya same shi,
suka jira Musaddik ya karaso suka fita zuwa wata unguwa da tafi kama da a
kirata da unguwar talakawa kai tsaye, tunda suka shigo layin Moh ya tabbatar da
zai samu yadda yake so, lallai Musaddik mugu ne na gaske, idan ba haka ba ya
rasa unguwar da zai samo ya siya gida sai irin wannan unguwar. A daidai wani
kofar gida karamin gaske suka tsaya, suka fito a tare wanda zasu gani yana
tsaye yana jiran su, yana ganin su ya karaso bakin sa cike da murna ya gaishe
su, sannan ya bud’e musu gidan yace su shigo.

   Siminti ne gaba daya tsakar gidan sabo yana ta
kamshi, bashi da girma tsakar gidan sosai dan be fi yaci tabarma days da rabi
ba, a gefe yar karamar rijiya ce saboda rashin ruwan unguwar.

   Dakunan guda biyu da suka kasance falle-falle ya
bud’e musu suka shiga nan ma ko ina an masa fenti yana ta kamshi, babu abinda
ba’a saka ba hatta karamin gado da kujeru an saka,da yar karamar tv babu batun
fridge ko cooker gas balle azo maganar su AC da sauran kayan more rayuwa,
kitchen din babu komai dama sunyi da nufin daga gida sai a kawo mata kayan
kitchen suyi amfani dashi. Kitchen din karamin gaske ne dan mutum biyu ba zasu
iya aiki a ciki ba saboda kankantar sa, balle a samu sukunin cika shi da kaya.

   Fitowa sukayi ya rufe gidan yana sake washe baki

 

“Ranka ya dade gidan yayi ko?”

 

“Yayi sosai yadda nake so, sai ka sanar musu ba sai an kawo
kayan gida ba ,iya kitchen ya isa shima karsu matsawa kansu duk abinda babu
zaka saka musu.”

 

“An gama ranka ya dade, sai maganar lefe.”

 

“Ana gobe daurin aure za’a kai, an gama hada komai ina
tunani.”

 

” Nagode Allah ya kara arziki.”

 

Be amsa ba, yayi gaba ya fad’a motar yana kallon tsarin gidan,
murmushi ne ya kwace masa, ya girgiza kansa yana ayyana yadda zuciyar Mama zata
buga ko kuma ta kusan bugawa,yayi alkawarin shayar da ita mamaki irin wanda
bata taba tunani ko hasashe ba.

 

  Kai tsaye wajen gym suka wuce, ya kwana biyu be motsa
jikin sa ba, yana bukatar hakan saboda tafiyar da sukayi be samu lokaci ba.
Dariyar shakiyanci Musaddik ya dinga yi masa, ya tsaya daga abinda yake yana
hararar sa

 

“wai dariyar menene haka? Uhum?”

 

” Naga yadda ka dage kake ta faman daga karafu nan nan ne
wallahi, kar dai ka illata musu yarinya wallahi, kasan dai kai din tsohon
tuzuru ne da yaki auruwa. “

 

Robar ruwan da ya gama sha ya jefe shi dashi, ya goce ta fadi
kasa yana sake tuntsurewa

 

” Ka kiyaye ni wallahi. “

 

” Anki din, daga fadar gaskiya?”

 

” Zan kamaka ne, naga kafarka a gida na wallahi. “

 

” Gidanmu dai. “

 

Towel ya ja ya goge gumin fuskar sa, ya biye wa Musaddik zai
dauke hankalin sa ne ga abinda yake shirin yi. Wayar sa ya dauka akan dan table
din wajen yayi dialing number ta, sai da ta kusan katsewa sannan ta daga.

 

 

“Huh!” Ya furzar da iska yana jan numfashin

 

“Ranki ya dade an gama jamin ajin ne?”

 

“Ina wuni?” Ta kautar da maganar ta hanyar gaishe shi

 

“Lafiya lou, ya gida ya kowa da kowa?”

 

“Alhamdulillah.”

 

“Masha ALLAH, yaushe Abba yace zaki dawo?”

 

“Be fad’a ba, amma naji Mummy tace ba zan dawo ba sai
ranar.”

 

“Ranar? Yaushe kenan?”

 

” Ka cika tsokana wallahi, nima ban sani ba.”

 

“Ke kuma kin cika kunya ba, sai kici sai ranar auren mu
kawai.”

 

” Allah zan kashe wayar.” Ta fad’a tana turo baki,
dariya yayi yace da sauri

 

” Allah ya baki hakuri Matata.”

 

Shiru tayi tana wasa da album din hotunan da Mamma ta bata bayan
ta mata bayanin kowa da yake jiki.

 

“In sha Allah ana gobe za’a kai lefe, kinsan sha’anin
rayuwar, Allah yasa be makara ba.”

 

” Be makara ba, Allah ya saka musu albarka.”

 

“Amin Matata, nagode sosai da bani dama da kikayi, in sha
Allah ba zaki yi Dana sani ba.”

 

“Kullum godiya? Ni me nayi?”

 

“Ai wai kinga dai yanayin yadda abubuwan suke.”

 

“Babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

 

“Amin Amin amarya ta.”

 

Yar karamar dariya tayi, shima ya tayata kafin suyi sallama.
Mamma ce ta shigo dakin rik’e da jaka babba, sai me aikin gidan dake biye da
ita da wasu kayan suma da yawa, ajiye su sukayi a gefe me aikin ta fita kafin
ta sake dawowa ciki dauke da tray da aka doro chicken pepper soup da wani cup
shima cike da abu kamar kunu, sai wani da akayi ma hadin fruits aka saka madara.
Dora shi tayi a saman drawer ta fita ta barsu.

    Da hannu Mamma tayi
mata alamar ta taso, ta taso ta zauna a k’asa in da Mamma din ta nuna mata,
tray din ta sakko mata dashi tace maza ta cinye naman tas, idan ta gama akwai
bakuwar da zata shigo wajenta, Itace me jakar chan. Tun zuwan ta gidan take
faman shan abubuwa, a dan lokacin tayi masifar chanjawa, tayi kara fari da kiba
jikinta ya sake murjewa sosai. Ita kanta tana jin da gaske ta kai mace, tana
jin zata iya karawa da ko ma wace amma a dah, bata da wannan confidence din.

   Bata kyuwar cin duk
abinda aka bata dan da bata samu wanda zai dubeta ba balle har ya bata abinda
yasan zai amfane ta. Shiyasa ta bada himma take yin duk abinda za’a sata.

 

***A bangaren gidan su Iman kuwa, bayan dawowar Abba sai da suka
sake wani rikicin da Mama, wanda ya saka kowa ji har aka dinga ganin baiken
Maman, amma kishi ya rufe mata ido matar Abba Musa na zugata tayi masa tijara
son ranta, be kula ta ba don a yanzu baya sakata cikin jerin masu hankali, yana
mata uzurin kishi ne ya sakata yin wasu abubuwan. Bayan kamar kwana biyu da
dawowar sa ta same shi har daki ta bashi hakuri abinda ya bashi mamaki sosai,
hakura yayi ya sakko amma ba wai don ya hakura da maganar Iman ba, yana nan sai
ya yi mata hukunci daida abinda ta aikatawa yar sa.

   Shirye shirye ya
kankama sosai, mama babu zama kullum tana hanyar kasuwa tun da ta samu labarin
cewa Bashir yace iya kitchen kawai zasuyi, hakan yayi mata dadi shine ta maida
hankalinta sosai wajen kawata kitchen din dan ta tabbata gidan ba karamin gida
bane, dole ne su fita kunya ta hanyar hada mata kitchen din yayi sosai.

   Duk abinda ta tambaya
Abba bata yake dan baya son wata doguwar magana, hankalin sa gaba daya yana kan
maganar auren Iman, da yadda daurin auren zai kasance domin yasan za’a yi taro
ne irin wanda ba’a taba yi ba, manyan mutane zasu halarta da yan siyasa da
manyan sarakunan k’asar nan da ma na ketare. Duk abin nan Mama bata san komai
akai ba, bata taba tambayar shi game da Iman din ba ko yadda nata tsarin yake,
shiyasa kawai shima ya rufe ta ruf ya barta da abinda take yi.

   A yadda tsarin bikin
yake, alhamis za’a yi kamu, juma’a a daura aure sai asabar dinner kamar yadda
Zeenat din suka zauna suka tsara ita da Bashir bayan ya sanarwa Moh da tsarin
ya kuma bashi go ahead.

  Tsarin bikin da su kuma
chan masarauta suke shirya wa biki ne gagarumi za’a yi a Kano da Adamawa,
kowanne kuma kwanaki za’a dauka anayi tun daga asabar din washegarin bikin, na
Kano za’a fara kafin a koma adamawa in da za’a kai amarya.

   Kamar yadda yake a
tsari, ranar alhamis za’a karbi lefe, lefen Zeenat da Iman, wanda Mama tayi
gayya, gayya irin ta ban mamaki, tana Kuma sanarwa mutane suzo suga lfen Zeenat
dan ta tabbatar za’a ga kayan da baa taba gani ba.

  Yan uwa da abokkan
arzikin Mama su suka cika gidan, aka shirya kaya na mamaki, aka gyara gidan.
Wata sister Mama ce tazo ta sameta tana zaune cikin kawayenta ana shewa, ta
jata gefe hankali a tashe tace

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button