HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 12

 Halin Girma    12

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

***Kai tsaye ya wuce zuwa chan gaban Bubun, fadawa na aika masa da kikari, kirarin da yake jin sa har cikin kansa, sai dai baya taba bari yayi tasiri a gareshi, hasalima yi yake tamkar be san me suke cewa ba. Dukawa yayi kamar yadda yake a al’adah ya gaida Bubun, ya amsa masa da ka ba tare da yace komai ba, a irin wannan zaman Bubun baya magana sai ta kama, sanin haka ne yasa Muhammad din ya koma daga bangaren dama ya zauna kafin sauran yan fadar su shiga kawo masa gaisuwa. Amsawa yayi duk a jimlace, ya hakimce a gefe yana sauraron  zaman yake wakana. Kasancewar zaman na gab da tashi ne yazo, shiyasa yayi tunanin ba za’a wani ja lokaci ba, sai yaga an dauki lokaci ana maimaita abinda aka fad’a a baya, ya sani sarai hakan tsarin bubu ne, kila kafin ya iso ya shirya hakan saboda shi, murmushi yayi yana satar kallon Bubun da shi din ma shi yake kallo. A karon farko yaji tausayin mahaifin nasa ya kamashi, yadda yake kokarin ganin ya damka mulkin a hannun sa bayan shi kuma bashi da ra’ayin hakan, amma kuma be tursasa masa ba, ya cigaba da bin sa a hankali zuwa lokacin da yake ganin ya dace.

   Be san ta yaya zai fahimtar dashi ba, amma yana da dalilin sa babba da ya saka shi tsayawa akan bakan sa, akwai babban kalubale a gabansa idan har ya amince da muradin Bubun , amma ta yaya zai iya gujewa hakan? Bayan babu wanda yasan dalilin sa? 

   Yana jin sanda zaman ya kare, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi ya daga idon sa sama yana kallon tsaruwar fad’ar, komai na ciki me tsada ne da kawa, haka duk wani abu da yake ciki me muhimmanci ne ga masarautar.

  Tunanin Bashir ne ya fado masa, da ganin da yayi masa da fitsararriyar yarinyar nan, Bashir yana direbobin Masarautar Kano wanda ya sanshi sosai saboda kaudin sa da hayaniyar sa, kafin ya auri wata mata wadda ake kyautata zaton auren jari yayi, tun daga lokacin kuma ya bar masarautar sai jefi jefi yakan je ya gaida Fulani idan ta kama. Yayi mamakin ganin sa da zabgegiyar mota amma da ya bincika ya gane komai, sai yaji hakan yayi matukar yi masa dadi, yayi Kuma daidai da tsarin da yake son dora su akai.

   Dawowa yayi daga tunanin jin kamar an taba shi, ya kalli wanda ya taba shin sai ya fad’ad’a fara’ar fuskar sa, 

“Aji!”

“Tunanin me kake haka Muhammad?” 

” Babu komai, mun same ku lafiya?”

” Lafiya lou, ya aikin? Amma kazo kenan ko? Zaka dade?”

” In Sha Allah!”

” Sannu da zuwa.” Yace yana mikewa

” Zuwan ka dana ji ne ya sakani zuwa , Ina fatan idan ka huta zaka shigo, akwai batutuwan da nake so mu tattauna.”

” Muje na taka maka, dama nima akwai maganar da nake so muyi.”

” Toh toh madallah.”

” Muhammad.”

Bubu ya kira sunan sa yana daga zaune

” Na’am Bubu!”

” Naji dadin ganin ka da shiga irin wacce ta dace da kai, Ina fatan dorewar hakan.”

” In Sha Allah Bubu, zan kokarta.”

” Madallah da kai.”

” Allah ya kara girma.”

Tashi yayi suka fice tare da Aji, hannun su cikin na juna, Maimartaba ya jinjina kansa yana mamakin tarin kaunar da suke wa juna, har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tafiya tunanin abubuwan da aka tattauna don cigaban al’umma. Sai dai yana fara tunanin, tunanin ta ya shigo ya katse masa duk hanzarin sa, ya rasa dalilin da ya saka a duk sanda ya tuna da maganar yake jin duk wata walwalar sa da farin cikin sa ya ragu, musamman a dan tsaikon nan, sai yake jin tamkar ana dakatar dashi da yin wani yunkuri. Shi din mutum ne me riko da addini matukar gaske, baya taba bawa maganganun da za’a zo a fad’a masa muhimmanci ko kad’an, sai dai a duk abinda ya shafi Muhammad baya wasa, yana ji a ransa kar fa abinda tsohuwar matar ta sanar masa ya zama gaskiya, tsoron hakan ya hanashi gabatar da komai cikin sauri yake bin komai a hankali, ba kuma wai dan ya gasgata maganar ta dari bisa dari ba, sai dan yana ji da tsoron sharrin masu sharri, be san me suke shirya wa dan nasa ba, sai dai be gaza ba, babu dare babu rana kullum cikin nema masa kariya yake a wajen ALLAH, ko ma menene tabbas zai zo masa da sauki.

 ***A falon Ajin ya same shi yana zaune fuskar sa kamar gonar auduga, da kansa zai je amma sai Bubun yace ya bari yazo kawai ya huta. Bayan ya zauna ne fadawan suka fice suka jawo musu kofar.

  

“Na matsu na sanar da kai wannan albishir din, abinda muka dade muna jira ne, Muhammad dai yazo da magana, har yana neman aje ayi masa tambaya!”

Fuskar Bubu ta fad’ad’a,farin ciki ya mamaye shi

” Masha ALLAH! A kanon ne kamar yadda Takawa yace?”

” Eh har binciken da mukayi, nan din ne in Sha Allah.”

” Sai a sanar wa Takawa babu jira, in Sha Allah gobe duk abinda ya kamata ayi sai ayi, jibi sai aje musu da magana, da tsayayyiyar rana domin Takawa ya bukaci ayi komai a cikin kankanin lokaci.”

” Madallah…Hakan yayi.”

Tattaunawa suka shiga yi har dare yayi sosai,kafin ya koma bangaren sa cikin jin dadin labarin auren Muhammad din.

***Jifa tayi da kofin hannun ta, ya fashe a wajen gaba daya kwalbar ta wawwatsu a dakin, wani irin bakin ciki take a duk lokacin da taji wani abu da ya danganci Muhammad din. Yau Itace a turakar Bubu amma tasan ba zata taba samun kansa ba, idan ma ta zafafa zai iya cewa ta bar masa dakin shiyasa ta yanke wa kanta hukuncin ko da yadawo daga wajen Aji ba zata je ba zatayi zaman ta tayi tunanin menene mafita a gareta.

“Ranki ya dade, Yarima Muhammad yana waje yana neman iso.”

” Uban me zai min!!”

Ta daka mata tsawa tana huci, sai kuma ta hau kokarin daidaita kanta

” A shigo dashi babban falo gani nan.”

Da sauri baiwar ta fice tana mamakin uwar dakin nata.

Zaman sa yayi yana karewa falon kallo, an sabunta komai ba kamar zuwan sa na karshe ba. Murmushi ne a fuskar sa, yana da yakinin bata da bukatar ganin shi, ko da gilmawar sa ne balle har ya kai ga zama a falon nata, yana sane yazo domin ya kara tabbatar da abinda ya sani tun tuni.

  A yadda ta fito, da yadda ta zauna kadai ya isheshi amsar abinda yazo nema, yana kallon yadda take satar kallon sa cikin kallon da yasan na tsantsar tsana ne tun da ya riga da ya dade da sanin bata kaunar sa ko daidai da minti daya ne

” Barka da gida, mun sameku lafiya?”

Ya fad’a da yanayin da yasan zai sake tunzura ta.

” lafiya, ya aikin naku?”

“Babu dadi, na gudo ma na dawo gida cikin yan uwa!”

“Ka kyautawa kanka.” Tace a gajarce

Mikewa yayi yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa, ya yi mata kallon cikin ido tace

“Bari na koma.”

“Baka Sha ko ruwa ba.” Tace tana daga zaune

“Na yafe, bani da bukata.”

 Ya dage gira yana juyawa, da kallon bakin ciki tabi bayansa har ya fice daga falon, ta yarfe hannunta tana jin kamar ta kamo shi ta tayi ta jibgar shi har sai taga ya daina motsi.

“Ciwon Ido, zanyi maganin ka!” Ta furta tana tashi ta koma ciki

***Daga nan bangaren Ammin sa ya wuce, yana jin kansa kamar sabon ango, farin ciki yake ciki shiyasa ma be wani damu da abinda ya faru ba. Dama yasan kafin ya isa ta samu labarin ko ta wajne Hajja ko Bubu, aikuwa yana shiga ta tare shi da murnar ta, ya zauna ya tankwashe kafarsa a gabanta tana jin yadda take lissafo masa abubuwan da za’a bukata na zuwa gidan su Fatiman.  A farkon farko be so wani abu na sarauta ya shigo ba, amma kuma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba, shiyasa yayi amfani da damar nan wajen hadawa Mama gadar zare, dalilin tafiyar ta da shine ya assasa bayan ya kira Khalil a waya ya karanta masa yadda duk yake so ayi, babu musu ya amsa kuma ya tabbatar masa da zai yi komai daidai. Dazu Kuma ya kira shi ya tabbatar masa da Maman ta iso tun wayewar gari. Da wannan ya yi gaba wajen aiwatar da saura shirin sa da ya tabbata zasu yi matukar girgiza kowa ba Maman kawai ba.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button