HALIN GIRMA 12

Har dare sosaii yana shashen Ammin, ta hada komai abubuwan da ya tabbata zasu dace da tsarin fatimar sa, shi din ma akwai tanadin da yayi mata amma ba yanzu ba, sai ranar da dubban mutane suka shaida, ya zama ita ta zama shi, a ranar zai nunawa duniya kalar gatan da take dashi a wajen sa.
Da sassarfa ya karasa part dinsa, Kai kace wani uban aiki yayi saboda yadda yake jin sa a gajiya. Kwanciya kawai yayi bayan ya aika mata da cool night text message ya kashe wayar sai bacci, baccin da yake yi a duk lokacin da ya samu kansa a dakin sa na cikin gidan.
Zai iya cewa ya jima beyi bacci me dadin na ranar ba, ko dan abinda ya faru a ranar ne? Ko Kuma dai dan ance gida daban yake, dama bahaushe na cewa kowa ya bar gida… wanka ya soma yi, ya fito domin ya karya dan yasan komai na kammale a ajiye yana jiran sa. Zaman karyawa yayi, yayi dialing number dinta yana kallon plate din da ake zuba masa abinci, da hannu yayi masa alamar ya isa, ya karba ya soma ci jin bata daga ba, a yar mu’amular da yayi da ita, ya lura tana da bawa kowanne abu muhimmanci idan har shi ta saka a gaba, misali idan tana aiki takan ajiye wayar ta waje daban ta kammala aikin, haka idan tana wani muhimmi abun bata hada shi da komai har sai ta gama. Tunanin sa ne ya katse lokacin da kiranta ta ya shigo nasa. Murmushi yayi yana jan tissue ya goge bakin sa, yayi rejecting kiran sannan ya bi bayan yana kishingid’a a jikin lallausan tumtum din dake kusa dashi.
Da sallamar ta, ta daga kamar ko wanne lokaci, ya amsa mata shima kafin ta dora da gaisuwa
“Ina kwana?”
“Lafiya lou, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lou, yasu Ammi? Ka same su lafiya?”
“Kalou kowa, ya sister Maryam da jiki?”
“Gata ta samu sauki, inaga ma na tafi gida tunda naga ta warke sosai. ”
” A ah kiyi zaman ki! ” Yace da sauri
” Me yasa? ”
” Amm kin gane, kinga tana bukatar ki, ki dan kara mata ko da kwana biyu ko uku ne, zata ji dadi. ”
” Owk tam. ”
” Yawwa. ”
” Ina kika shiga dazu na kira no answer, kitchen? Ko shara? ”
” Ya ka sani? Ina kitchen. ”
” Na sanki ai, nasan bakya wuce wuraren nan biyu. ”
” Lallai, kasan abubuwa da yawa akaina, amma ni bansan komai ba. ”
” Zaki sani, karki damu zaki sani fiye da sanin da kowa ma yayi min. “.
Ya karashe maganar cikin sigar tsokana, bata ce komai ba, yasan kuma ba zata ce din ba, shima ba dan tace wani abu yayi maganar ba
“Zan zauna takanas, kiyi min duk tambayoyin da zaki yi min, zan amsa, amma kafin lokacin ina so ki san, nifa soja ne!”
“Soja!” Tace gabanta na faduwa sosai, bata son aikin soja ko miskala zarratin, bata kuma taba tunanin auren soja ba, dan tasan yadda suke very busy da aikin su
“Eh ni soja ne, amma fa irin kurtun nan.”
“Soja dai ai duk soja ne, sunan daya ne.”
“Amma rank din daban daban ba.”
“Uhummm. ” Ta ja ajiyar zuciya, ya sammace ta, kenan dai zaman kadaici be rabu da ita ba, dan sojoji basu da lokacin kansu balle na matan su, yanzu ita kenan…
” Karki damu, ba zan dinga nisa ba kinji? Zan zama ko yaushe kika bukace ni Ina kusa, nayi miki alkawari.”
“Allah yasa, dan da gaske bana son aikin soja wallahi.”
“Saboda me? Aikin taimakawa kasa ne fa, aikin lada ne idan har ka yi yadda ya dace.”
“Na sani, ni kawai bana so ne, basu da time din kansu ballanta na …”
“Na matan su? Haka ko yaushe aka cewa dama, toh ni dai Ina da time dina Ina kuma da na matata, har sai kin gaji kin koreni daga gidan ma wataran.”
“Shikenan.”
“Zaki gani ai, ki zuba ido.”
Shigowar Ya Maryam ya sakata yin shiru
“Ki fito falo ya tafi wallahi, ni kadai kamar mayya.” Tace mata tana rik’e kofar, tun dazu tace tazo falo taki sboda maigidan yana nan, shiyasa Maryam din tazo kiranta da ya tafi, ko yar hira sa yi
“Kice ina gaishe ta, ya jikin nata.”
“Da sauki.” Tace tana janye wayar daga kunnenta.
“Ashe waya kike shine kika yi luf, toh ki gaishe shi, in kin gama Ina jiran ki.”
Ta fita ta ja mata kofar
“Bari na barki kuyi hirar ku, zan sake kira anjima.”
Kamar ta tambaye shi maganar zuwa gidan amma ba zata taba iyawa ba, sallama tayi masa ta ajiye wayar ta fita wajen Maryam.
Yana sane sarai yake ce mata komai, baya so tasan komai sai anyi komai ya kammala, ba zai ma gaya mata zuwan nasu ba, Abba kawai zai wa text ya sanar masa, idan yaso sai ya turo Musaddik ya sameshi ya sake fad’a masa Incase ko be ga message din ba. Haka kuwa akayi, yana masa text din ya gani, yayi saurin kiran kowa ya sanar dasu zuwan bakin, anan suka fara tunanin abinda ya kamata suyi, baki daga irin wannan babban gidan dole ne ayi abinda za’a fita kunya. Sun dade suna shawarwarin su kafin su tsaida matsaya, nan da nan suka shiga shirin tarbar su cikin tsarin da suka san ba zai zama wani iri ba.
Abba na zaune kiran Mama ya shigo wayar sa, shi kadai ne a gidan sai Habib ta tafi da Zeenat da Marwan, shiru gidan babu kowa kallon tv yake a zahiri amma a badini tunanin masu zuwa neman auren Iman yake a gobe, yaso ya sanar wa mahaifiyar ta zuwan nasu da komai akan maganar sai dai baya samun ta a waya wajen kwana uku kenan, yasan tana business sosai kamar ma tana fita kasashe saro kayayyaki shiyasa yayi tunanin ko kila bata k’asar ne.
Kallon wayar tasa yayi, har lokacin haushin Maman yake ji musamman abubuwan da ya gano akan irin rikon da tayiwa Fatiman tsawon lokaci be gane komai ba, har Marwan ya titse ya tambaya ya kuma gaya masa komai abinda ya sake daga masa hankali sosai kenan. Kiran ne ya sake shigowa ya daga ba dan yaso ba, dan dai kawai be san ko wani abu bane emergency ya taso, sallama tayi ya amsa ciki ciki. Dama tasan za’a rina shiyasa kawai ta tafi kai tsaye akan dalilin kiran
“Dama Zeenat ce ta ce na sanar da kai iyayen Bashir zasu zo gobe idan Allah ya kaimu.”
“Su bari jibi gobe Yaya yana da abinda zai yi.”
Yace mata kai tsaye
“Amma da ka barsu sunzo goben ba dole sai wajen Yayan ba ai.”
“Haka tsarin mu yake tun farko, babu Kuma dalilin da zai saka na chanja yanzu dan anzo auren nawa yayan, idan har ba zasu iya bari sai jibin ba sai ki nema musu wanda zasu gani a goben.”
“Abin be kai haka ba ai, Allah ya kaimu jibin.”
“Amin.”
Yace ya katse kiran yana Jan tsaki, wato duk dadewar ka da mace ba zaka taba sanin wasu daga cikin halayen ta ba har sai abu ya faru, lallai. Shi kadai yake ta wannan tunanin har lokacin da zai kwanta yayi, ya kwanta da addu’ar Allah yasa komai ya tafi dai-dai goben.
***Duk cikin su babu wanda ya makara, suka tashi aka hau gaggayara gidan harabar da lungu da sako su Habib suka taimaka aka tsaftace ko ina, dama dai a gyara yake saboda takanas aka dauki me aikin kula da wajen amma duk da haka idan suka tuna bakin da zasu zo sai suga ya kamata a sake gyara ko ina.
Wajajen sha biyu cikin jagorancin Musaddik suka iso, cikin manya manyan motocin alfarma da aka rubuta Emir Kano 1 guda biyu sai guda biyu dauke da tambarin Adamawa Palace.
Cikin kankanin lokaci unguwa ta dauka, mutane suka dinga lekowa daga gidajen su dan tabbatar da abinda yaran su suka je suka fad’a musu, kowa ya leko sai ya rik’e baki cikin tunanin abinda ya kawo irin mutanen gidan.
Cikin matuakr girmamawa Abba suka karbe su, sai dai sunyi tunanin zasu gansu a matsayin mutanne da basu kai ba ko kuma level dinsu ba daya ba, amma sai suka ga akasin haka, cikin girmamawa, karamcin da dattako suka zo musu, suka nuna Halin Girma, halin babban gida babu fariya ko nuna su din wasu ne, cikin tattautasa harshe da girmamawa suka nemarwa dan su kuma jikansu Muhammad auren Fatima. A take Abba yace an bashi. Su kuma nan take suka gabatar da ranar da suke so a saka, babu musu nan ma Abba ya amince suka tsaida wata daya kachal, shi din ma saboda Muhammad din ne ya bukaci haka, amma idan sune toh sati biyu zasu saka.