NOVELSUncategorized

NAJEEB 6

DEDICATED TO…..

MY BESTY OF LYF HABIBA BUZY???????? LOVE U WUJIGA WUJIGA????????

                 PAGE 6

wai Mai yasa wasu mutane basa tsoran Allah ne? Sai dai a baki kawai, nifa Maryam bacewa Nayi bana son kud’i ba, Yooo ni wacece da Zan’ki son kud’i ai kud’i Abun sone, but in mutum zai
naima kud’i saiya nema ta guminsa, akan wani dalili zan zauna in bata lokaci na inyi typing in rubuta Basira na, bata wani ko wata ba, in siya data da kud’ina ba tare da nace wani ko wata ya siya min ba, sai na gama rubuta y’ar basiran da Allah yayi min sai wani ya d’auka ya dinga neman kud’i dashi, toh Wlh Wlh daka yanzu bazan k’ara d’auka ba, abun ya zama raini dacin fuska, da farko an d’auki novel d’ina har guda uku ansa a okada ba tare da neman izini naba, ansa BA’KIN ALJANI in zaka karanta saika biya 500, ansa FATIMA ZARAH, shi kuma in zaka karanta saika biya 200, ansa DUKIYAR MARAYA,  wanda barawon ya canza mishi suna izuwa dukiyar marayu, in Zaka karanta saika biya 300, akan wani dalili, ni Ina rubuta littafi a kyauta sannan wani yaje ya kaimun okada yana amsan kud’i da Littafina Wanda Nina rubuta bashi ba, nima fah ina son kud’in bawai banso ba, amma nayi a kyauta, akan wani dalili Kai ko ke zaku dinga siyar da novel din mutane without our permission, sannan Bayan haka wasu suna bud’e group akan in zasu tura maka novel complete saika biya kud’i, kuma Abun haushin basu suka rubuta novel d’inba, novel dinmu da muka rubuta suke saidawa, wasu ma saisu cire sunanmu akan novel din su saka nasu, Toh Wlh duk wani wanda ya k’aramin haka Wlh bazan d’auka ba, ba cika baki ba ko fariya Wlh akan hakkina Zan iya Shari’a da mutum, Abu d’aya shine in samu number d’in mutum, shikenan an wuce wajan,na fad’a zan k’ara fad’a maryam novel d’ina kyauta ne kar ku yarda ku biya kud’i domin a tura muku novel d’ina, ga sunan littafai na Zan fad’a, *FATIMA ZARAH
DUKIYAR MARAYA
 BA’KIN ALJANI
 BANDA ZABI
AMINIYA TACE
 KISSA KO MAKIRCI
 SUHAILAT
TAMBARIN TALAKA 
JAWAHEER 
SAINA AURESHI
MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
BARIKI NA FITO
SAI YANZU WANDA NAKE RUBUTAWA NAJEEB
Gaba d’aya kyauta ne karku yarda wani yace saikun biya kud’i ya tura muku, kuma inna k’ara Kama wani yana saida min da novel saina d’auki mataki



Zarah tace Kai granny mata har uku? Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad’in sunyi mishi yawa ai. 

Granny tace rabu da dan banza, koya zabi d’aya koya auresu duka, dan wannan karan bazan mishi wasa ba, inda a kauye ne da yanzu an fara maganan zai aurar da y’a, amma wai sai yanzu zaiyi aure, wannan lalacewan har ina, wlh ni rayuwar Bariki batai min ba.

Ibtisam tace uhm toh saiki koma kauyen ai ki zauna, Muma sai mu huta 

Granny taja tsaki tare da fad’in basai ki Mai dani ba, mutuniyar banza, fita tayi dan taji muryan d’an Nata yana waya, alaman ya fito 


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Alh Abdullahi yana ganin Granny ya kashe wayar yana gaidata cikin girmamawa tare dayi mata ya hanya.

Tace Alhmdlh Ai Kai zance ma ya hanya kaida ka dawo daka k’asa Mai tsarki.

Zama yayi suka fara fira da Uwar tashi, suna cikin firan mum tazo itama anayi da ita,  Alh Abdullahi yace Ina mamana ibtisam? 

Mum tace suna ciki ita da zarah, bari in kirasu, tashi tayi ta nufi d’akin sai gasu tare sun dawo, ibtisam gaida uncle din Nata tayi cikin girmamawa, ya amsa tare da sakin fuska yace kin Kawo takardun naki koh, y’an makaranta. 

Granny tayi caraf tace dakata ni dan Allah, wai ku Mai yasa bakwa maganan aure saina karatu? Kallesu yara duk sun girma suna shirin tsufa a gida, kwata kwata bakwa maganan aure, saina karatun banza da hofi, toh Wlh na gaji, bazaku sa a dingayi dani ba, ina tafiya ana nunani ba, nazo ne muyi magana akan yaran nan dan Wlh wannan karan rai zai baci in akak’i bin abunda nazo dashi, nazo ne akan maganan auran wannan dan banzan najibu naga ku kaman Abun bai dameku ba…. 

Dad yace mama Nima Ina bukatan NAJEEB yayi aure Sosai, amma har yanzu ya’ki magana, ko ince ya’ki fito da Mata .

Granny ta tsuke baki tare da fad’in sai ka tsaya jira saiya fito da Mata ai, naga alama Kai ke d’aure Mai gindi yake iskanci Wlh, amma zanyi maganin ka Wlh, gobe zani yola da safe zanje in tawo da  yara cikin dangi ya zaba wacce yake so, dan Wlh wannan karan dole yayi aure sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in koso suke saina mutu banga y’ay’ansu ba, Nina tsufa yanzu banda wani buri face inga yaransu Kafin in mutu, amma naga kuke d’aure musu gindi, kuka take wi wi wi tana share majina da riganta 

Alh Abdullahi cikin Tashin hankali yake bata hakuri tare da fad’in mama duk yanda kika ce hakan za’ayi ki zabo mishi wacce tayi miki sai a d’aura mishi insun fahimci juna 

Suko su zarah da ibtisam dariya suke k’asa k’asa, suna kallon wannan jaraban ta Granny, tsohuwa sai iya jaraba 

Granny tace a’ah Zan Kawo su da yawa, inya zaba sai in maida su, daka nan sai a d’aura aure, inda so samu ne da tare dashi zamu ma,amma Nasan bazai jeba, kuma ina son kona tafi kar wanda ya mishi maganan auran saina dawo.

Dad yace duk yanda kika ce mama hakan za muyi.

Tashi tayi tana fad’in nidai na fad’a maka, gobe karfe 6 Zan tafi saika tashi da wuri dan asan abun yi, bari inje in kwanta 

Bayan Granny ta wuce suma su zarah suka wuce suna dariya, tare da fad’in Wlh Granny zata ballo ma NAJEEB aiki harda kuka, ita kam ibtisam dad’i take ji, don ta tsani NAJEEB gwara a mishi aure da y’ar kauye din zata fi kowa murna

Mum kam itama tana son dan nata yayi aure, sai dai bada irin matan da Granny tace zata bashi ba, tafi son a barshi ya kawo da kanshi akan a zaba mishi, tunda taga shi zai zauna dasu, amma zata zauna ta saka ido ta gani 

Alh Abdullahi Bayan Tashin granny Kai ya girgiza,  domin yadan Indai yana son ganin farin cikinta da albarka a rayuwa dole yayi abunda tace, kuma yasan koda ta kawo matan Indai NAJEEB ne gata gashi, shima Dad d’in yana son dan nasa yayi aure.

Washe gari kaman yanda Granny tace karfe shida dai dai aka sakata a mota ciki harda su zarah da ibtisam da sukace zasu bita, granny tace babu inda zasu, in suka bita a Ina zata saka y’an matan, dole suka hakura mum ta bata su dambun nama, cin cin, cake da sauransu, nan driver yaja suka tafi, cikin mota Mai k’iran Prado, duk da Dad yaso su bar tafiyan zuwa gobe suje a jirgi, granny tace yau zata tafi basai gobe ba, dole Dad ya hakura.

Su zarah gida suka koma, har zata kwana ta tashi tana kallon ibtisam tace Bari in duba d’akin bros in gani, tun jiya yace insa a gyara, kullum sai angyara amma in yazo in ba’ayi wasa ba sai yayi complain yace an bata mishi wani abu, ai gwara Granny ta mishi auren yaje can ya k’arata, tabe baki ibtisam tayi tare da juya baya ta kwanta abunta.

Ibtisam ba ita ta Farka ba sai wajan 11, koda ta tashi Zarah bata d’akin, d’aukan wayarta tayi taga lokaci, tace Kai nasha bacci Sosai, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito tasa wata jallabiya ba’ka sannan ta d’aura gyalen jallabiyan, zama kiran kabir ne ya shigo wayanta, inda ta d’auka suna ta fira daka karshe yace zaizo ya ganta anjima da yamma.

Tace Allah ya kaimu, yace ta bashi address Sunan Layin ta fad’a mishi da no din gidan, yace OK saiya kirata 

Koda suka gama waya, shuru tayi tana d’an tunani, ta rasa mai yasa take d’an jin kabir cikin ranta kwata kwata ko sati d’aya basuyi da had’uwa ba, jiya da yace zai kirata, bai kira ba duk ta damu, toh mai hakan ke nufi? Lokaci d’aya tayi murmushi tare da fad’in dan shine namijin dana Fara kulawa, kuma yana da hankali gashi ya iya magana Mai dad’i dasa nutsuwa. 

Jin muryan Zarah tayi tana fad’in Ashe kin dad’e da tashi tunda har kinyi wanka, ina can ina taya mum aiki, wai yau ita da kanta zatai abinci d’anta zai zo.

Ibtisam da bata son maganan NAJEEB tace uhm, Zarah tace muje muyi breakfast tun d’azu nake jira ki tashi muyi tare, yunwa nakeji, yanzu na shigo in tasheki Ashe kin tashi. 

Tashi Itbtisam tayi suka fita a dinning suka zauna suka fara cin abinci, bayan sun gama ibtisam tayi kitchen ta gaida mum, tare da fara tayata aiki, suna aiki suna fira, rabin firan duk na NAJEEB ne, shi yasa Itbtisam tayi shuru, sai dai takan yi magana jefi jefi, a haka har suka gama, aka jera komai akan dinning, wayar mum ce tayi k’ara dauka tayi cikin harshen turanci tace son har kazo kenan? Driver yana nan tafe Nasan yama kusa zuwa? 

Yace mum nama ganshi saina k’araso, tace ok my only son tare da kashe wayan. 

Mum ta kalli su Zarah tace harya k’araso, tunda ibtisam taji haka ta tashi ta wuce d’aki, domin bata son ganinshi balle ya k’ara raina mata wayau, ita rabonta dashi ma zaiyi shekara ko fiye ma 

Tana d’aki tana jiyo maganansu harda na NAJEEB daya dawo, ciki harda Dad Sun dad’e suna fira sannan ya tashi ya nufi part d’inshi danya samu ya wuta.

Ibtisam tana nan kwance Zarah ta shigo tace baki fito kun gaisa da Bros ba. 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button