NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 13

???? *WA ZAI FURTA?*????
              1⃣3⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

???????????????????????? *For Gaje Abu*
???????? Alaweez???????????????????????? Ana mugun tare.

*Ya Allah ka Kara Mana katangar karfe da masu bakinciki damu* *Hassada ga Mai rabo taki ce duk Wanda Allah ya tarfa ma garinsa nono wallahi ko ana mazuru ana shaho sai yasha* masoyana ga taku????????????????????

     ***************
*KADUNA RIGASA*

Tayi zaune falon suna labari da hajiya bayan ta sako doguwar hijab.
Ta kawo Mata lemu da naman kaji……gidan Alhaji shamsu naje shine na biyo ni in ganku tunda Shi ya kwammace yayi ta kullenku da ya barku zumunci.
Murmushi tayi kawai.
Ya kuke ba wata damuwa dai ko?
Babu damuwa, ta mike tsaye bari na Kira ummin ku gaisa.
  Da gasken gaske hankalinsa ya tashi sha”‘awar Amira ta addabeshi.
Da farko yaji haushin kwalelen da ta mishi amma da ya tuna haramcin yin haka saboda ya shiga hakkin Ummi, sai ya bata uxuri.
Ya shiga toilet dinta yasa ruwan zafi ya warwatsa a jiki saboda ya Sami sauki, sannan ya fito.
Zaune suka tarar dashi suna labari da hajiar, ya kasa dauke idonsa daga Amirar duk inda tayi idanun sa na kanta har Ummi ta Shaka.
Koda suka raka hajiyar Sashen Amirar ya koma.
Ya riko kugunta wallahi gobe sai kin gane kurenki……
Wai Ina Kika saki Kaya haka bayan nasan ke ba ma’abociyar su ba ce?
Inji waye? Ina ra’ayi Kaine naga kamar basa birgeka…….wallahi Ina so. Da kin tsaya dazun tabbas da ba kiss kadai zanyi ba……….. Maganar ta makale ganin Ummi ta banko kofa kamar an biyo ta….


        **************
*Federal University dutsinma*
   ……Malam ba Wanda kake tunani bane get lost…. Ya bude baki zai Kara magana ya fiddo mishi idanu I said get lost ya fada cikin tsawa………. Wai Kai baka girmama manya ne?
This is not your business mutane fa Yanzu kasar nan a firgice suke kamar…..kamar kowa ya haukace irin ka?
Da sauri mutumen ya kalleta, sai kawai ya tashi yabar wurin.
Ya kamata kasan darajar mutane fa……naji kiyi hakuri go….ya Mata nuni da baki.
Kana korata ne don na Fara fada maka gaskiya……. Bilkisu muje…… sadeeq ne ya karaso da sauri.
Sadeeq kayi ma Anwar fada abunsa ya Fara wuce gona da iri ta Yaya zai ringa yi wa magidanta tsawa babban mutum mai kima…… Dan Allah kiyi hakuri ban karawa…ohhh my God.
Ya akayi ne? Inji Sadeeq.
Ta juya suka jera suna tafiya tana magana cikin fada fada, Shi ya raina kowa, mutum da kimarsa yayi mishi magana mistakenly it might be ya mishi Kama da wani ne Wai kaga wulakancin da ya mishi? Haka kawai ya janyo ma kansa dauri a banza…….. Kiyi hakuri Zan Kara mishi nasiha don Anwar Kam sai dai nasiha ba fada ba.
Suna wucewa ya saki ajiyar zuciya……. Ya ruga mota.
Yana Zama ya kirata a waya, kamar bazata dauka ba tana kokarin hawa jirgin bayan sun rabu da sadeeq…….
Hello…fly mode Zaki Sanya wayar ki Kuna landing in the next 40-50 minutes I’ll call..okay?
Naji, thank bye….ta latse wayar.
Yayi dariya, Bilkisu rigima.
……. Yana bude mota ya shako wuyansa…..Dan ubanka me yasa kakeyi Mata boye boye?
Ya kyalkyace da dariya, 
Wane babban mutum ne kayi ma wulakanci a gabanta…… Wallahi su Alhaji murtala ne kasan Shi ya cika shisshigi Ina Jin saukarsu kenan.
Ya zaro ido? Shi ka yankwana???
Kwarai kuwa……anjima idan yazo lissafi Kuma fa me zaka ce mishi?.
Inaaaa bazan bashi fuska ba yasan bana son haka gaban mutane.
Ya kalleshi, jirgin kayan nan fa ya iso tun last week, jibi zanje Lagos nayi clearance a Fara distribution…….
Masha Allah.
Amma me yasa baka son Bilkisu tasan Kai wanene?
Yayi murmushi saboda Suma suna da kudi Kuma…… Kuma ubanwa??….. Ko makaranta kaki nuna ko Kai wanene Wai me yasa kake haka?
Yayi Yar dariya, Kuma fa yarinyar ta gane Zan masifa amsa questions irin lokacin da tasan ni first class ne.
Kana son Bilkisu ko Anwar?…..
Ya kalleshi bana son irin wannan tambayar taka na Fara gajiya da ita, saboda ka kasa fahimtar baka da amsarta Yanzu……mtseww nonsense. Ya Kai mishi duka.
 Tarihinka Zan Bata Dan ubanka, Zan fada Mata Kai din wanene….. Da kayi nadama irin Mai ban tausayin nan wlhi.
Sadeeq din suka Fara ajiyewa  sannan so gida unguwar makil da jama’a Yan maula kofar gidan ba masaka tsinke ………

*TUSHEN LABARIN*
Babban gida ne a Kano, Alhaji Hamza hamshakin Dan kasuwa ne Wanda aka sani ko’ina a fadin duniyar.
Yaranshi shidda hudu Mata sai biyu maza.
Matansa uku, Allah bai azurtashi da yawan yaran ba,sai yawan dukiya.
Ta farkon hajiya maimuna keda Yara hudu, maza uku mace daya, ta biyun Allah bai Bata haihuwa ba hajiya Jamila, sai karamar keda Yara biyu mace daya namiji daya Kuma Wanda ya kasance Auta a gidan watau mahaifin Anwar  (Alhaji Yusuf ).
Ya tashi cikin tsana da tsangwama ta Yan uwa, ganin hakan yasa mahaifiyar Shi ta maida hankali ga karatunsa fiye da harkar kasuwanci.
Babu Wanda mahaifinsu bai jaraba ba cikin yaransa maza 3 Amma dukkan su sai da suka ha’ince Shi.
Yusuf bai da lokaci ma bare a kwatanta kullum Yana makaranta.
Ya gama jarabawar aji shidda suna jiran sakamako mahaifin su Allah yayi mishi rasuwa daga ciwon ciki.
Nan da nan rikicin rabon gado ya taso.
Aka raba rabo na son zuciya.
Cikin gidajen da suka gada shida Yar uwarsa da mahaifiyar sa suka koma can wata unguwa.
Allah ne gatanta shine jigonta.
Ya ce zai ci gaba da kasuwanci kawai tunda ga jari sun samu.
Nan da nan ya Fara fita China Yana saro turaruka Yana rabawa manya manyan shaguna a garin Kano.
Tun Yana tsayawa Kano kadai har ya Fara kaiwa kaduna, zariya……wasa wasa sai ya bulla har Lagos, Abuja da sauran wurare.
Arziki Kashi…….. Nan da nan ya Kara da cosmetics, takalmomi, jakunkuna…..Kai kayan masarufi……..kafin kace kwabo Yusuf ya taso da zafi….hakan yasa mahaifiyar sa bata duba karancin shekarun sa ba tace lallai sai yayi aure.
 Bai da ko budurwar ma saboda bashi da wannan lokacin.
Itace ta nemo mishi diyar kawarta Yan asalin Yola Fulani basa ko hausa cikin gidansu, lokacin duka bai wuce shekara ashirin da biyu ba.
Shekarar su daya cif da Aure aka haifi Anwar…..bayan ta haifeshi kuma tace ga garinku nan Shi bai San mahaifiyar sa ba.
Tunda ga lokacin ko maganar Aure baya so.
Anwar ya tashi hannun kakarsa, Yana Dan shekara 2 bayan an yaye shi yayar babansa Aunty murja tayi Aure.
Ya kasance gidan daga Shi sai kakarsa mahaifinsu ba mazauni bane sai Yan aiki dake kula dasu suna musu dawainiya.
Duk Yan uwansa arzikin ya tsiyace sun dawo karkashin sa…..
Cikin kankanin lokaci ya nunka mahaifinsu kudi linkin baninkin.
Yan uwan cutarsa sukeyi amma kullum kudin kamar ana Kara musu taki.
Ya mallaki kaddarori iyaka, kamfunna a Nigerian ba inda baya dashi komai Yana shigowa dashi Kuma ana yi na cikin gida.
Anwar na primary school ya Kara Aure, ba hausa Amma mazauna saudiyya yarinya Mai hankali da sanin ya kamata…….watansu uku da Aure hatsarin jirgi ya rutsa da Alhaji yusuf.
  Anji mutuwar sa a kasa Baki daya, sanarwar rasuwar ya barar da tayin cikin Amarya.
Illahirin dukiyar Anwar da kakarsa suka gaje ta, Nan take ta ce ta yafe ma Anwar komai na mahaifinsa amma nata na mijinta a fiddo Mata, haka akayi kuwa aka Bata ta karawa yarta murja.
  Kafin marigayin ya rassu Yana yawan fadawa mahaifiyar sa amintattun mutanen sa da wadanda ke cutarsa. Baya boye Mata komai.
Cikin amintattun hada Alhaji murtala ( wadanda suka hadu da Anwar airport ), shine kan gaba wajen Jan ragamar kasuwancin.
Tsaron shaguna aka ba wasu daga cikin macuta.
Allah da nashi iko, sai ya dubi maraitar Anwar ya Kara bunkasa dukiyar……..
Yana j.s one wata Rana an dauko Shi school sun shawo layin gidan su kawai suka ga yaro gabansu da Keke……da karfi suka taka birki ji kake kuuuuuu…. Yaron ya Fadi da karfi lokacin da keken ya daki motar Kan ya karye tayar ta lauye….Shi Kuma ya karya musu madubi ya karci motar.
Anwar na kwance bayan sit, yaki ko motsi tunda yaga abinda ya faru ya kishingida bai Kara dagowa ba……. Drivern ya fita mutane suka taru sosai, ihu kawai yaron keyi Yana kururuwa wallahi sai an biyashi keken sa, kowa yasan laifin yaron ne amma sai aka goya mishi baya.
Shurun tayi yawa hakan yasa Anwar din fitowa, ya kalli Umar driver yace ya akayi?…….
Sai kawai yaron ya cakumo wuyan Anwar, na rantse da Allah ban sakin sa sai an biyani kekena…….. A hasale Anwar din ya kalleshi cika ni ko Kuma wallahi in maka mugun duka anan…ya fizge tare da ingijeshi yayi taga taga…..Nan Yan unguwa kowa ya Fara darewa an San Hali…..
Ya Kara shako wuyansa….. Umar yayi wuf ya fizgeshi…… Sai abun ma yaba Anwar dariya.
Keken nawa yake?
Koma nawa yake wallahi sai kun biyani, don ba inda zakuje ya babbake hanya Yana ware kafafu.
Shigo muje …..Akan wannan shegen keken…..wani nushi ya Kai mishi a gefen fuska, Nan da Nan suka rukume fada…kichaaa…kachaaaa.
Mutane suka yo kansu da gudu…….kowane sai haki yake.
Yau naga bala’i Kai wane irin Dan iskan yaro ne?……. Mugun bugu Zan maka, wallahi na gane fuskar ka matukar ka Kuma zagin keken Nan sai nabarka kwance saboda zufar ubana ce….ita wannan motar zufar uwarka ce da ka fado Mana ko baka ga ka Mana barna muma……
Sunfi awa ana abu guda daya Anwar yace Basu biya Shi Kuma ya hanasu tafiya……har hajiya ta Kira waya taji shiru.
Hankalin ta a tashe ta fito…… Tasa aka iso da ita wurin da ake rigimar .
  Yaron ta kalla lokacin da ta iso tace zo muje a siya ma wani keken….ta kalli Umar saka wannan mota……Yanzu naji magana…ya figi hannun Anwar zo muje tare kada a yaudareni…….suka fada motar hajiyar da tazo ciki.
Anwar na shakkar hajiya baya kaunar bacin ranta duk duniya.
A motar yaji tana waya….. hello Yanzu Yanzu Aiko da sabon Keke Mai inganci na Dan samrayi sa’an Anwar .
Suna shiga Anwar yayi saman bene da gudu cikin bacin Rai.
Suka zauna falo Shi da ita…..ta kalleshi ya sunan ka?
Yace *sadeeq* da sauri.
Babanka ya siya maka ne?
Eh, ya zumburo baki cewa yayi idan nayi na daya a makaranta zai siya mun, yau kwananshi biyu fa da saye!.
Tayi murmushi…..to ba sai ya Kara siya maka wani ba idan yaje kasuwa?……ai ba a kasuwa yake yin faskare ba nan kusa da gidan mu ne kullum…..dai dai Anwar na saukowa bene….ta ce innalillahi faskare yakeyi?
Eh, shine yayi ta tarawa ya siyo mun keken.
……..hansa’u!!!!!!! Ta kwala ma cikin Yan aikin Kira. Da sauri ta karaso, kawo ma yaron nan abinci.
Ya washe baki Yana Murna,Nan da Nan Anwar yaji tausayin sa musamman da aka kawo abincin yanayin yanda yakeci.
  Ya tashi kawai yabar gun.
Da gudu Anwar din yayo baya cikin firgici jin ihu ba kakkautawa……..Ashe sabon keken ne aka shigo dashi..
Kawai ya dunga buga tsalle Yana ihu da rawa….. Da hajiya da Wanda ya kawo keken sukayi ta dariya…… Kai Wai baka da hankali ne ? Ya daka mishi tsawa ka bani tsoro a banza wajen hauka……Allah ya baka hakuri  Yanzu ko duka na kayi bana ko kallon ka…mtsew ya yi hanyar daki.
Ya ruga ya kamoshi…..zo muje mu dana tare kafin na tafi a titin cikin gidan Nan…… serious ya kalleshi…are u mad?
Baya jin turanci ko kadan ya figi hannun sa kazo mu je ka tukani in tuka ka kowa ya Rama ma kowa sannan in tafi…… Sai kawai Anwar din ya bushe da dariya….Ni yau na hadu da matsala.
Hajiya ta Sanya musu ido kawai da tsiya ya fidda Anwar din…..
Ta kalli labaran da ya kawo keken…..yaron can dole ya Zama abokin Anwar saboda zasuyi dai dai…….. Shi yasa na tsani karatun kasar waje Ina so yayi anan yasan duniya……. Arziki irin na yaron nan Yanzu Yana da hadari a gareshi……. Hayaniyarsu take jiyowa suna ta wasa.
Da abu yayi dadi a mota aka Kai sadeeq har gida da sabon keken sa da ma tsohon Basu da nisa sosai.
Mahaifansa sukayi ta godiya, tun daga ranar kullum sadeeq sai yaje gidan su Anwar wasa su hau Keke, shillo kamar kananan Yara.
Shakuwarsu yasa Anwar din kawai yace a maida su school daya suka dauki nauyin karatun sa.
  Abin mamaki tun a lokacin sai Anwar din ya ringa mishi kandakun kada yaje Yana bada labarin gidan su.
Aka ba iyayen sadeeq jari Mai tsoka Banda taimako da zakka sannan hatta Kaya sutura Anwar ke ba sadeeq tun Yana bashi kwance har ta Kai Shima nashi ake siya mishi.
Suna girma Anwar na Kara miskilanci sadeeq Kuma na Kara lakantar sa ciki da bai.
Yana ss 2  ragamar dukiyar sa kaf! Ta dawo mishi mafi karfin kasuwancin yafi karfe a *Dubai* sai ya kasance da anyi hutu yake tafiya sadeeq Kuma ya tsaya Nan Yana wasu ayyukan.
Ko kadan Anwar baida fahari.
Ko a Dubai yasha Kira cikin yaransa yayi acting as shine Anwar din wajen wata Hulda idan tazo.
…… Babu kasar da baya zuwa da sunan kasuwanci.
Shi yasa da jarabawa ta fito ya cike Nigeria jihar katsina Kuma, don ya na son surveying area din ciki da bai, saboda suna da karancin kasuwa a katsina matuka……
Jiragen sa shidda sannan ya na da share a Abu Dhabi airlines suna bayar da hayar jiragen su. Anwar hamshakin Mai kudi ne Amma duk duniya ba abinda ke birgeshi irin ya boye Identity dinsa Yana acting as normal person hakan na saka Shi nishadi Shi yasa karatu kasar waje bai taba birgeshi ba yafi so yayi cikin normal mutane cewarsa masu kudi naturally suna da wani abnormality Wanda basu fiye sanin hakan ba…….. Duk wani taimako da ake bayarwa makarantar fudma daga miliyan daya zuwa sama Anwar ne ba tare da an sani ba.
Yana da tausayin talaka, Abdul Mai shop yasan Anwar masu kudi ne saboda kyautar da yakeyi mishi na ya Kara jari Kuma ya mishi mugun kashedi Koda wasa kada ya fadawa kowa.
  Yana da gadara haka ya tashi fil azal…………
*wannan kenan*

Falon cike da mutane ya shigo duk suka Mike Allah Shi taimakeka…….
Wayarsa tayi Kara , *Bilkisu ce* da sauri ya daga Ranki ya Dade Kun sauka?
Um, gashi ma har na Kama hanyar gida….good nima shigata gida kenan mun biyata gidan su sadeeq….Ayyah, ka Kara mun godiya ga sadeeq Allah ya Kara arziki…..Baki da matsala.
Zamuyi waya Anjima please.
Okay bye….ta latse wayar.
 Ya kalli Alhaji murtala……. Yallabai yau ka dawo ne?
Ya rusuna Allah ya Kara ma daraja eh wallahi.
Yayi Yar dariya Dan Allah idan Kun ganni da jama’a ku daina irin haka bana so Kun San haka, za a ringa kallona bani da tarbiyya matukar Ina tsawatawa Kuma tabbas bana Jin dadin hakan……kuskure ne ayi hakuri in shaa Allah…… Ina takardun jirgin da ake gyara Jidda??
Ya Mika mishi file gashi…………. Sai karfe shidda da Rabi ya shiga ciki.
Tana zaune bisa abun sallah ya shigo…….. Yaro da akidar manya….tsohuwar ta fada.
Yayi dariya hajiya tuwo zanci akwai ko?
Eh, …….. Ya Mike a hada mun kafin na watso ruwa na gaji yau Zaki Sha labari…..
    Tana kwance bisa kafar mommy falo kiransa ya shigo……ta daga hello Anwar.
Ranki ya Dade……ya gajiya?
Ba gajiya yasu mamah?, Ya danyi jimmm, kafin yace Hajiya lafiyarta kalau,
Ohhh, hajiya yake Kiran mamansa?
Yasu mommy ya katseta. Ga mommy nan kusa dani…Ina gaisheta please.
Tana amsawa.
To meye labari?
Labari na wurinka ni na iya labari ne?…..mommy ta zameta tare da mikewa…
Ki koya Mana sai ki bani.
Me yasa gidanku babu hayaniya ko yaran sunyi barci?
Auwal da musbah ne suna can dakin su.
Ke Kuma kina makale da mommy ko?…. Tayi Yar dariya ai ta tashi ma ta shiga ciki.
Ya Kano din?
Kauyen Kano dai? gamu ciki ya fada Yana dariya.
Ta ce hmm.
Zan Fara fita kasuwa gobe kin San talaka baya Zama……kana kasuwanci ne?
Eh, Ina bin wani ubangidana Ina mishi tsaron shago cikin sabon gari a garin Kano……kin San kasuwar sabon gari?
Naji dai ana fada.
Okay toh can.
Tausayin sa ya kamata…….rashi bai hanashi gadara da izzah ba, Mai Hali baya barin halinsa….kinyi shiru.
To Allah ya bada sa’a ka samo kudi da yawa Wanda zamuci biscuits next semester….ya kyalkyace da dariya ni Zan siya Miki?
Kwarai kuwa a rama wa kura aniyarta nima sai na ci kudin ka next semester…..hahahaha ya Kama dariya.
Naji Zan dage na samo da yawa.
Ke me Zaki kawo mun tsaraba?
Abinda kake so,
A’a kawai ki dai kawo man ko menene.
Hmmm, tace.
Ko bazan samu ba?
Zaka samu in shaa Allah.
  To me Zaki kawon?
Ka fada Mana me kake so?
A a bani da zabi.
To shikenan ka jira zaka gani.
Na gode.
In kyaleki haka ko?
Okay gudnight ta kashe kawai……. Ya doka tsoki jira takeyi ne?
Yarinyar nan tafini
 gadara wallahi.
  Washe gari bai Sami kansa ba ko kadan, abubuwa sun taso, ba shiri karfe shidda ya bar kasar……
Yanayin abubuwan sai da ya kwana biyu bai samu yayi magana da Bilkisu ba.
Ta nemeshi a waya har ta gaji. 
Da ta Kira sai a Fara nata faransanci Ashe France ya tafi ya Kuma chanza layi.
A Rana ta biyu ana ta meeting a katon office din sa Kira ya shigo through WhatsApp ya kalli turawanya ce kowa yayi shiru,
Ya daga… Hello Bilkisu…. Duk kasuwar ce wayar ka Bata shiga? Ina Kira sai wani yare ko ka Sanya Ni voice mail ne?….. Voice mail Kuma ? Yayi dariya kiyi hakuri wasu kayukane muke shiga Saro tattasai Kuma ba service wurin kiyi hakuri muna lissafi da Mai gida anjima zamuyi chatting……
  Hakan kuwa akayi tun Sha daya suke chatting har kusan biyun dare.
Amma ita dashi lokutan sun banbanta…..
  Daga ranar kuma bai Kara samun lokaci sunyi magana ba.
   Fushi tayi Bata nemeshi ba, Suleiman kuwa duk bayan kwana biyu sai ya nemeta sun gaisa.
Ranar da zai baro France aka mishi waya zasuyi meeting Abuja da managers din, *Next, ShopRite da Sahad*
Dole sukayi landing Abuja.
Motoci shidda kebin bayan tasa biyu na gaba. Saboda tafe yake da nashi mutanen.
Ko a cikin motar waya kawai akeyi.
Bayan an gama meeting din suka zagaya ta kofar shiga ShopRite wurin ice cream security sai kyarma sukeyi yau ga Anwar…… An cunkushe kofar an tsaida masu shiga.
Ya Kira Angelina suna magana………Ai sai ku bamu wuri mu wuce ko?
Da sauri ya waigo *Bilkisu ce* rike da iyayen ledoji……….????✍????


*Ayi hakuri a hankali za a ji yanda labarin ya ke da yanda zai Kare* Banda sauri please mubi komai a hankali.
Zainab wowo ce????????????
????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button