HALIN GIRMA 22

Karuwar kukan Laila ya sake sakata cikin yanayin da ta shiga, har Maimartaba ya karaso bakin dakin tana tsaye kamar an dasa ta, bata san me zatayi ba. kallon ta yayi kafin ya maida kallon sa cikin dakin, yayi musu kallo daya wani abu me dacin gaske yana tokare shi a goshi. Juyawa yayi sai a lokacin kwakwalwarta ta kai mata sakon waye wanda ya shigo din, da sauri ta zube a wajen ta gaishe shi cikin muryar ta da take rawa sosai.
Be amsa mata ba, sai daga mata kai da yayi ya juya ya fice yan rakiyar sa suka bi bayan sa cikin tunanin dalilin zuwan Bubun shashen Moh.
Kasa daga kafarta tayi daga wajen, ta jingina da bangon dakin tana karanto duk addu’ar da tazo bakin ta, ji tayi kamar ana mata magana, ta dago tana kallon cikin dakin
“Amarya! Kinyi farin gani ko?”
Me zata ce? Shiru tayi tana maida idonta ta rufe shi ruf tana kokarin ajiye abinda ta gani din da kuma abinda zuciyar ta take haska mata waje daya.
“Anya? Anya kuwa? Muhammad? Me ya faru? Me yake shirin faruwa? Wacece wannan din?”
“Karki wahalar da kanki tunanin wacece ni, sunana Laila, gimbiya Lailah.”
Yawu me karfi ta hadiye, ta hau kokarin daidaita kanta waje daya, shigowa taji an sake yi, ta daga idonta da sauri wannan karon wata babbar mata ce ta shigo a hargitse, tayi saurin yin kan wadda ta kira sunan ta da Laila tana rik’e ta, tana kallon yadda Lailan ta cigaba da rusa kuka kamar Allah ya Aiko ta, matar na bata baki jikin ta na rawa sosai. Daga ta tayi da sauri, ta yafa mata mayafi ta rik’e hannun ta, suka zo daidai in da Iman din take tsaye, matar tayi mata wani mugun kallo, ita kuma Laila tayi mata murmushin da ta tsaya mata a rai. Fita sukayi tayi saurin zuwa ta sakawa kofar key, ta dawo ta durkusa a k’asan falon ta shiga kuka, kukan da take ta kokarin rikewa dan bata son su ga weakness dinta, dama chan ita mutum ce me taurin zuciya da wuya kaga weakness dinta, shiyasa yanzun ma ta daure har suka fita.
Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta share hawayenta, a kalla zata so taji ta bakin shi, kar ta yi judging dinsa da abinda ko a musulunci babu hujja, dan bata gansu suna aikata wani abu mara kyau ba. Duk da ta na kokarin karfafa jikinta da zuciyar ta akan ta bari taji komai, amma kuma jiki da zuciyar ta ta sunyi sanyi, sanyin da take jin kamar komai ya kare mata, kasan zuciyar ta tana jin zafin sa, tana jin haushin sa amma kuma bata da damar yanke masa hukunci.
A yan awannin da tayi a cikin gidan nasu ta fuskanci akwai wani Babban al’amari da ya shafi Moh dinta. Tana jin kamar gadar zare aka hada masa har ma da ita. A nutse take duk da abin ya kadata, dan babu matar da zata ga wata mace a dakin mijinta cikin yanayin da taga Laila ba tare da taji komai ba, sai dai ta yarda da addu’a dan haka ta dage sosai har ta soma jin nutsuwa na saukar mata.
Bata san dadewar da tayi a wajen ba, taji kamar motsi a dakin, ta tashi ta dubo cikin rashin sa’a ta cire takalmin ta, ta taka glass din da yake fashe a wajen, kara tayi hakan ya farkar da Moh gaba daya, ya mike da sauri kansa yayi wani irin sarawa da be taba jin irin sa ba, jiri yaji yana neman kayar dashi yayi saurin komawa ya zauna yana dafe kan, bayan kamar sakan goma ya mike a hankali ya fito.
A durkushe ya ganta tana rik’e kafarta da har ta fara jini, da sauri ya karaso ya durkusa a gabanta yana kama kafar
“Me ya same ki? Me kika taka.”
Kokarin janye kafarta tayi, ya sake kama kafar ya rik’e yana kallon kafar cikin tausayawa.
“Cika min kafata.”
Tace ba tare da tasan me yasa ba, kawai ganin sa ya sakata jin haushin sa. Kin cika mata kafar yayi, sai ma daukar ta da yayi gaba daya duk da yadda yake jin sa babu kwari, ya ajiye a gefen gadon ya dauko first aid box din sa yazo ya durkusa a gabanta ya gyara mata kafar Allah ya taimaka kwalbar bata shige ba.
“Yaushe kika zo nan? Ya akayi nayi bacci? Me ya faru aina aka samu kwalba a wajen nan har kika taka? Ina masu kula da wajen?”
Ya jero mata tambayoyin cikin son tuna wani abu, da Ido kawai yake bin sa kamar me son karantar sa, sai dai bata ga komai ba sai tsantar gaskiyar sa a yadda yake maganar. Janye kafarta tayi ta mikar da ita a saman gadon, ya dawo ssman gadon ya zauna yana jan kafar ya dora akan cinyar sa.
“Bacci ne ya dauke ni bayan na sha juice daga nan kuma bansan me ya faru ba, kin dade kina jirana? Da baki tashe ni ba?”
“Bana so na katse maka barci ne.” Tace ganin duk ya damu, ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa ya gyara mata kafar yadda zata ji dadi, ya mannu a jikinta.
” Kiyi hakuri, kaina ne naji yana min ciwo sosai shine kawai nazo na dan huta bansan zanyi bacci ba.”
” Ba komai.”
Tace tana rufe idon ta
” Bacci?”
” Umm.”
Tace a gajarce dan bata son doguwar magana tana son tattara bayanan da ta samu ta hade su waje daya kafin wayewar gari.
Tashi yayi ya fita bayan ya maida rigar sa, ya hau k’wala kiran ma’aikatan wajen, da sauri ya shigo yana raba ido, masifa ya fara yi masa akan dalilin barin kwalba a hanya, hakuri yayi ta bashi yayi saurin gyara wajen sannan ya fita.
Ji yayi duk jikin sa yana masa ciwo, chan k’asan zuciyar sa kuma wani irin feeling ne da be san dalili ba, ji yake kamar idan har be samu abinda yake so ba zai iya rasa ransa, yana wanka yana tunani har ya kammala ya fito daure da towel iya ka guiwar sa, kallon in da take kwance yayi, ta dunkule waje daya kamar me jin sanyi.
Kaya ya saka sannan yayi sallah ya duba wayar sa yaga misscalls da yawa, ganin dare yayi ya saka shi ajiye wayar ya hawo gadon yana juyo da ita tana kallon shi. Hawaye ya gani a saman kuncin ta, ya saka hannu cikin mamaki yace
“Kuka?”
Kamar wadda take jiran kiris ta shiga rera shi sai dai babu sauti, rikicewa yayi ya hau tambayar ta menene, bata amsa masa ba, ta cigaba da kukan ta wanda ita kanta bata san me yake sake tunzura ta take kukan ba, da farko ta zata zata iya daurewa sai daga baya ta gane duk dauriyar ta wannan ya wuce in da take tunani, kishin mijinta ne ya sakata kuka. Magiya ya cigaba da yi mata akan ta fad’a masa dalilin kukan ta amma taki, rungume ta yayi a jikinsa yana lallashin ta amma kamar kara ingizata yake, ya rasa yadda zai, ga wani irin abu da yake jin yana taso masa. Kasa daurewa yayi ya hade bakin su waje daya, da karfi tayi kokarin turashi ta amma ta kasa!
Rano????
*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*????????????
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*????????
09134848107
[ad_2]