HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30

***Tana idar da sallar la’asar sai gashi ya shigo, ba kayan da
ya fita dasu bane a jikin sa, wasu ne daban da sukayi mata kama da sababbin da
ba’a taba sakasu ba, gaishe shi tayi a ladabce tana daga kan sallayar, ya amsa
yana zama, yanayin sa ya nuna a gajiye yake, sai ta tashi ta ninke sallayar ta
ajiye ta nufi kitchen ta dauko masa ruwa da soft drink, akan tray ta doro ta
dawo falon ta ajiye masa tana rissinawa, saurin tayata yayi yana hadawa da
hannun ta da tray din, sukayi dariya a tare ta zauna a gefen sa tana zuba masa
ruwan. Karba yayi yasha, sosai saboda tunda ya fita be saka komai a cikin sa
ba, gashi sam baya jin yunwa so yake kawai su tafi.

 

“Ga abinci akan dinning ko na kawo maka nan?”

 

“Waye yayi?”

 

“Nice.”

 

“Owk zanci, amma ki zubo min a plate ba da yawa ba, sai ki
taimaka min da fruit please,.”

 

“Ok.” Ta mike bayan ta karbi cup din ruwan ta ajiye,
taje ta zubo masa abincin ta kawo ta koma ta yanko fruits din ta kawo, yana
kwance ya mike kafafunsa, har sai data zauna a gaban abincin sannan ya sakko
yana saka spoon din a gaban sa ya soma cin abincin hankalin sa a kwance, sosai
yaci dan beyi tunanin zai ci kamar haka ba, sannan ya sha fruits din kadan,
bayan ya gama yace

 

“Thank you…Abincin yayi dadi.”

 

Blushing tayi cikin jin dadin yabon da yayi mata, ta hau tattare
kayan zata kwashe ya rik’e mata hannu

 

“Ki barshi yaran chan zasu gyara idan mun tafi.”

 

“Ai ba wahala, bari na kwashe kawai.”

 

Sakin hannun nata yayi, ta dauki tray daya, cikin takun da bata
san tana dashi ba, ta shiga takawa zuwa kitchen din, kallon ta yake har ta kule
kafin ya dawo hayyacin sa, yana kallo ya sake dawowa ta kwashe sauran ya sake
bin steps din nata da kalllo, ba zai iya hakura ba, musamamn idan ciki ya
dauka, ga kuma abunka da sabon angon da be san ya isa ba, tashi yayi har da dan
saurin sa, ya sameta a kitchen din tana tattare dattin plates din, sam bata ji
shigowar sa ba, sai ji tayi an rungume ta, ta baya. Ta juyo a dan tsorace kafin
kamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kitchen din.

   Manne bayan su yayi waje daya, ya dora kansa
saman gadon bayanta, ya shiga goga mata bayanta da kan nasa.

 

“Ba… Bari… Na karasa gyara kayan.”

 

“Barshi, ai dama ba aikinnki bane, ga aikin lada me
yawa.”

 

Ya sake chusa kansa sosai, tsam ta dauke hannun ta, sanda taji
hannun sa na yawo a daidai tsakiyar cikin ta, yana shafawa har zuwa kasan rigar
ta, rik’e jikin kitchen cabinet din tayi dan ji tayi kamar zata fadi, Allah
yaso ta dafe wajen. Daga ta yayi sama chak, ya wuce falon zuwa bedroom dinsu,
ya dire ta yana mata murmushin mugunta,  a matukar tsorace take dashi
amma kuma ba zata hanashi ba, dan ba zai taba bata damar da zata hanashin, yabi
ya kanainayeta da salon kaunar shi me tsayawa a makoshi!

   Sai da suka bata lokaci sosai, dan har wani dan
guntun bacci yayi bayan nan, da k’yar ta tashe shi yayi wanka ya shirya, suka
fita a mota zuwa wajen Ammi, daga nan suka fice daga masarautar da magribar
fari!

 

***

Tun bayan fitar sa bata tashi daga wajen da take ba, sai da taji
yunwa na neman kai ta k’asa, ta tashi ta jawo ledar da ya bari ta cinye
ragowar,tasha ruwa ta kwanta a wajen.

   Har wajen takwas na dare Hajiyan bata dawo ba,
turo dakin akayi, ta dago tana kallon sa, tashi tayi zaune da sauri tana kare
jikin ta, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita, ya ciro wayar sa a aljihu ya
rik’e a hannun sa yace

 

“Zan kira miki Mama,dan ta kira tana son magana dake nace
mata wayarki ce ta lalace, idan kika kuskura kika fad’a mata wani abu sai ranki
ya baci.”

 

Banzan kallo tayi masa, ta warci wayar lokacin da taji tana
ringing, bata jira Maman tayi magana ba ai tana jin ta daga ta rushe da kuka,

 

“Lafiya Zeenat, wannan kukan fa?” Tace a kidime tana
saka handsfree dan Habib yaji shima

 

“Mama dan Allah kice wa Abba yayi hakuri na tuba, dan
Allah!”

 

” Ki nutsu ki fad’a min abinda yake faruwa, menene?”

 

” Bana son auren nan Mama, dan Allah kizo ki tafi dani
wallahi zan mutu!”

 

” Mutuwa? Me yayi miki Bashir din?”

 

Shiru tayi ta rasa me zata ce, dan bata isa ta fadi abinda ya
faru tsakanin ta da Bashir din ba, a sanyaye tace

 

” Mama yana da Mata, kullum sai ta sakani aikin wahala babu
dare babu rana, ga tsangwama, karshe ma Mama a BQ nake wallahi.” Sai ta
sake fashewa da wani kukan,salati Mama ta saka, ta kama zagaye a dakin tana jin
bayanin Zeenat din

 

” Yana ina, bashi wayar.”

 

Tun kafin ta bashi ya karba yana mata murmushi,

 

” Hello Mama.”

 

” Kana ji? Wallahi tun muna shaida juna da kai ka dawo min
da ‘yata, wannan ai wulakanci ne, wallahi ka dawo min da ita kafin kasha mamaki
na.”

 

” Kiyi hakuri Mama, amma Zeenat matata ce,a yanzu nine nake
da iko da ita,dan haka kiyi hakuri dai.”

 

” Kan bala’i, ni kake fadawa haka Bashir?”

 

” Ayi hakuri Mama, gaskiya ce, sai mun sake kira mu gaishe
ki.”

 

Kafin ta sake magana ya kashe kiran, ya kuma kashe wayar gaba
daya ya jefa ta aljihun sa, yayi gaba zai bar dakin ta chakumo shi ta baya

 

” Na rantse da Allah sai ka rabu dani,sai ka sake ni
wallahi ba zan zauna ba, na tsane ka bana son ganin ka.”

 

Maganganun ta sun masa zafi kwarai, amma sai ya danne ya jawota
ya hadata da bangon dakin, ya dalle mata baki sannan ya bi ta da kiss me zafi.

 

“Idan kika sake yi min ihu wallahi sai nayi fata-fata dake,
aure na dake babu saki ko yaji, auren mutukaraba kenan, ko nace miki auren
zobe, idan bakiyi wasa ba sai na tabbatar miki da haka a yau din nan, ta hanyar
zuba miki ajiyar da baki isa ki guje min ba.”

 

Tofar da yawu tayi ta durkushe a wajen tana sakin kuka gwanin
tausayi. Tsallake ta yayi, yayi ficewar sa yana dariyar mugunta, yana son
Zeenat din da gaske, amma kuma ba zai dauki rashin kunyar ta ba, ko kuma ya
kyale iyayenta su taka shi ba, sai abinda yaga dama zai yi da ita tun da dai
shine me iko da ita a yanzu.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button