HALIN GIRMA 26-30

“Dan Allah kayi hakuri.”
Ta hau bashi hakuri ganin ya dauki hanyar da yar kwakwalwarta ta
gaza dauka balle ta gane karatun. Tsayawa yayi chak da abinda yake, ya soma lallashin
ta cikin kalamai masu dadi da kwantar daa hankali, a hankali ta dinga samun
nutsuwa har ta dawo da nutsuwar ta, ta saduda ta saddakar ta mika wuya, domin
dama ance shi aure yakin mata ne, toh tabbas wannan yana daya daga cikin manya
manyan yakin matan. Ba zata iya cewa ga kalar wahalar da tasha ba, duk da yayi
matukar kokari wajen ganin bata sha wahala sosai ba, amma kuma dole ne, sai dai
a hankali a hankali komai zai daidaita haka rayuwar take haka kuma kowa yayi
har ya saba. Ita dai bata san sanda wani baccin wahala ya kwashe ta ba, a hakan
ba tare da ta gyara ba, sai chan cikin dare ta farka ta zame jikin ta, ta wuce
toilet ta gyara kanta sosai sannan ta dawo dakin ta kwanta tana shigewa jikin
sa, sake rungume ta yayi tsam a jikinsa bacci ya sake awun gaba da ita.
  Da yake tafiyar wuri zai saboda ogan sa da yake
son gani, ya saka yana sallar asubah yayi mata sallama ya tafi, kamar ta
hanashi tafiyar haka taji amma bata nuna ba, dan ta lura da muhimmancin tafiyar
tasa shiyasa ma bata nuna damuwar ta ba, bayan gari yayi haske sosai Ammi ta
aiko aka tafi da ita chan shashen ta, daga nan kuma aka kaita ta gaida Bubu, ya
saka musu albarka sannan ya hada da nasiha akan rayuwar zaman aure wadda ba
zaka taba iya gane ta ba sai ka shiga cikin ta.
 Sai dare ta dawo bangaren ta, tayi wanka ta dauki waya
da nufin kiranshi sai ga kiran nashi ya shigo, sunyi exchanging text message
amma basuyi magana ba tun da ya tafi, whatspp yace ta hau ya kirata video call
suka dade suna waya, kamar kar su rabu da k’yar suka hakura suka kwanta.
Kwana biyu da tafiyar
sa, babu wani abu da suka samu daga ita har Muhammad din, duk da yace yana
kokarin sa daga chan din ma amma sam hankalin ta ya gaza kwanciya, gaba daya
bata cikin hayyacin ta kwata kwata dan ko sunyi waya korafin ta kenan.
Duk shirin da ya kamata
Laila tayi taa gama, ta saddakar dole ne ya aure ta, dan bashi da wata hujja
duk wata hujja ma bata bar mishi ba, shiyasa take shirin ta hankali kwance kuma
shiri gagarumi dan biki zatayi na kece raini, ita kanta Kilishi sai ta zama yar
kallo, amma kuma ita kanta tana son auren ya yi wu, dan rashin samun mafitar
Muhammad din shi zai taimaka sosai wajen cikar burin ta, dan ta riga ta gama
aikawa duk wasu manyan masarautar sakon abinda muhammad din yayi, ta kuma san
ba zasu taba bari a zaba musu muhammad din a matsayin shugaba ba.
Ana gobe wa’adin da Bubu
ya gindaya masa ya dawo, shi kansa ba a nutse yake ba amma yayi kokari sosai
wajen kwantar mata da hankali. Takanas yaje ya samu Aji sukayi magana be baro wajen
Ajin ba sai dare sosai, yayi tunanin ma zai tarar tayi bacci amma sai ya ganta
a zaune tana jiranshi.
Tsokanar ta ya hau yi
har sai da ya tabbatar ta manta, suka kwana cikin farin ciki sai dai asubah
nayi duk jikinta yayi sanyi, duk abinda take yana kallon ta, ya kuma kara
tabbatr da da gaske tana son shi tana kuma kishin shi sosai, sai dai bata son
ta nuna kishin nata a fili, ta barshi a zuwan kawai tana tayashi ne. Da wuri ya
shirya ya fice ta biyo shi har kofa kafin ya fita, ta rik’e shi sai hawaye,
janta yayi zuwa falon ya rarrasheta ya samu da k’yar tayi shiru ya fice yana
waya da Musaddik.
Kasancewar ranar ne
ranar da Bubu ya shirya ranar da zai sauka ya bawa muhammad mulkin duk da shi
Muhamamd din bashi da masaniya, sai ya zama na gaba daya masarautar ta cika
sosai da manyan mutane, tun a daren jiya wasu suka iso. Hakan ya jawo bubu ya
shiga busy sosai, sai da suka hadu da muhammad din a masallaci yace ya same shi
karfe takwas na safe a bangarensa. Shiyasa ya shirya ya fita da wuri, ya kuma
same shi yana shiryawa,. Kai tsaye Bubun ya tambaye shi idan yana da wata
magana akan abinda ake tuhumar sa? Kai tsaye yace bashi da wata hujja da zai
kare kansa, amma yasan be aikata abinda ake zargin sa ba, shiru Bubu yayi dan
yadda maganar ta karade ko ina har kunyar fita yake a yau, sallamar sa yayi
kawai ba tare da yace komai ba.
Fitowar Bubu ya saka
kowa nutsuwa, fadar tayi tsit bayan ya zauna, wanda suka sanshi suna kallon shi
zasu gane ransa a bace yake,limamin babban masallacin Masarautar ya saka aka
kira masa shi gaba, ya matso gaba, Bubun ya bada umarnin za’a daura auren
Muhammad da Laila. Nan da nan fad’ar ta dauki hayaniya, kowa na kokarin tofa
albarkacin bakin sa!
2/2/22, 18:24 – Buhainat: Halin Girma
   27
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
******* �
Matsowa Limamin yayi ya zauna, sai wambai da zai karbi auren
shima ya matso zuciyar sa fes shirin su ya tafi yadda ya kamata. Dakatar da su
Aji yayi, ya bada umarnin a fara gabatar da nadin sarautar kafin daurin auren
ya biyo baya, babu wanda yayi magana dan babu me ja dashi, sai dai kuma sam
manyan fadar sun ki amincewa da nad’in Muhammad saboda abinda ya faru, Bubu na
zaune be tanka ba, suka shiga tattaunawar gaggwawa in da kaso saba’in cikin
dari suka amince da nad’in Kamal, sai kaso talatin suka nun Muhamamad din, idan
aka samu irin haka toh dole ne a dauki ra’ayin bangare mafi rinjaye, a take aka
gabatar da Kamal a gaban fadar, aka kuma shiga yi masa nad’in cikin yanayin da
ya saka Bubu a matukar tashin hankali, be gamsu da karbar mulkin Kamal din ba
dan akwai gyara sosai a rayuwar sa, ganin da gaske idan yayi wasa komai na
masarautar sai ya rushe, sai kawai ya dakatar dasu. Duk kowa yayi zuru yana
jiran bayanin sa, be san me zaice ba, duk kuwa dashi ne shugaba amma kuma idan
har aka zauna tsakanin manyan fadar aka zartar da hukunci toh shi ma dole ne
yabi. Shiru ne ya biyo bayan dakatarwar da Bubun yayi, kowa na jira yaji abinda
zai sanar.
  Magatakarda ne ya shigo, ya fadi yayi gaisuwa
sannan ya mik’a sakon rubucacciyar wasika daga fadar kwamnatin adamawa akan
sabuwar dokar da aka zartar a daren jiya, aka kuma kayyade shekarun da ake so
duk wani sarki ya cika su kafin zamtowar sa sarki, ajiyar Zuciya Bubu ya sauke
ganin ko kusa da shekarun Kamal be kai ba. A karshe kuma gwamnati ta jaddada
lallai Sarki Ahmad Santuraki ya cigaba da zama akan kujerar sa kafin a samu
wanda zai gaje shi da irin shekarun da yake a rubuce, da kuma cika duk sharadin
da aka gindaya.
 Hayaniya ce ta dauka a cikin fadar, masu kushe abun nayi
masu nuna farin cikin su nayi, shi dai Bubu sai yayi shiru yana duban kowa, sai
a lokacin ya kara tabbatar da masu son sa tsakani da Allah a cikin manyan
masarautar da kuma wadanda da gaske suke son ganin bayan sa.
  Sai da kurar ta lafa, kowa yayi shiru bisa
umarnin Sarki Ahmad din, dan gani yayi abun nasu na neman ya zarme shi kuma
bashi da katabus akan dokar da taxo a rubuce daga gwamnati wadda take da dama
da ikon sakawa ko sauke duk wani Sarki. Jawabi ya soma yi cikin son ganin ya
kwantar da hankalin kowa, da kuma kokarin nuna bashi da masaniyar komai akan
sakon gwamna, duk da dole ne sanar da gwamnati kafin dora sabon sarki kuma
sunyi hakan amma be san ainhin dalilin gwamnati na fito da wannan dokar ba.
 Shigowa Muhammad yayi, ya samu gefe ya zauna suka hada
ido da Bubu yayi masa murmushi yana tuna haduwar sa da gwamna a daren
shekaranjia, ya kuma je masa da bukatar sa ta son sauya baki daya dokar, ya
bashi kwararan hujjoji masu gamsarwa wanda dama chan mutumin sa ne tun kafin
zamowar sa gwamna, babu abinda Muhammad din zai nema be masa ba in dai be saba
ka’ida da doka ba.
  Babu wanda yasan da wannan shirin nashi, babu
kuma wanda yayi tunanin hakan zata kasance, makasudin tafiyar tasa kenan da be
shirya karbar mulkin ba, ba zai kuma bari Kamal ya samu ba, yana da bukatar
morewa rayuwar sa da Fatiman sa, idan har ya sake ya karbi mulki toh dole akwai
abubuwa da yawa da be isa yayi wa kansa ba, ko ita.
  Bayan gama bayanin Bubu ne, kowa yai shiru masu
tattaunawa da zuciyar su nayi, masu tunanin mafita nayi amma kuma babu me sake
furta komai dan an gama maganar sai kuma wani lokaci idan me dukka ya kaimu.
 Liman ne ya sake dawowa gaba, domin gabatar da daurin
auren tunda an gama da wanchan babin, wambai da fuskar sa ta kasa boye damuwa
da bacin ransa ya matso bayan yayi wa Muhammad din wani kallo da shi kadai ya
san dalilin sa.
  Kamar yadda addini ya koyar, ana aure ne bisa
doran abubuwa guda uku, sadaki, siga da kuma shaidu, wanda duk sun hallara a
wajen, liman ni ya soma magana da gabatar da abinda ya tara su, kafin ya kai
karshe Muhammad ya katse shi, ya taso daga wajen da yake zaune ya iso gaban su
ya durkusa, ya mikawa wambai wayar sa yana komawa ya zauna daga gefen wamban
bayan ya tankwashe kafar sa, idon sa fes akan wamban yana karanta yanayin
fuskar sa. Da farko tsayawa wamban yayi chak da kallon video din, sai kuma ya
saki wayar ta fad’a saman cinyar sa jikin sa a mace ransa y kai kololuwar baci.
 Hannu Muhammad ya saka ya dauke wayar sa,ya mikawa Malam
Liman ya kunna video ya kuma karo volume din sosai yadda duk wanda yake kusa da
wajen zaiji. Muryar Laila ce take magana ita da baiwar nan tata, a daren da
za’a kawo Iman, a lokaci da suke maganar turaren, tun daga farkon hirar su har
karshen ta. A fuskar Bubu zaka hangi tsantsar farin ciki, amma kuma rawanin
kansa ya boye, sai ta kwayar idon sa kadai zaka gane, be ce komai ba dan dama ba
zai ce ba.
  Karbar wayar Muhammad yayi, ya mikawa sauran dake
wajen suma suka kalla, sannan ya kunna na karshe wanda yake nuna Laila sanda
take shiga part dinsa, bayan ta bawa masu tsaron kofar wani abu a cikin
envelope, wannan kadai ya isa hujja, hujja me karfi.
  Girgiza kai kawai Aji yake, dama yasan gaskiya
zatayi halin ta. Laila da Muhammad duk su din nasa ne kuma yana kaunar su amma
kuma ba zai taba goyon bayan karya ba.
  Wata hayaniyar ce ta sake kaurewa, aka hau Allah
wadai da hali irin na Laila, kuma ko babu hujjar nan Laila Itace mara gaskiya,
babu yadda za’a yi idan har cutar da ita Muhammad din yayi a sameta a bangaren
shi, idan har hakan ce ta kasance toh lallai shi za’a samu a nata bangaren amma
sai aka samu akasin haka.
 Aikawa Bubu yayi aka taho da baiwar nan, hade da masu
tsaron shashen muhammad din, tun kafin aiken ya je sun samu labari, sun shiga
matukar tashin hankali dan basu yi tunanin za’a gane gaskiya adan kankanin
lokaci haka ba, basu san cewa duk wanda yace Allah, toh ya gama komai.