HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30

Jifa tayi da dankwalin kanta da shahararriyar me kwalliya da ta
taho kafa da kafa tun daga Abuja tazo ta tsara mata shi, ihu ta saki ta hau
jifa da kayan dake saman dressing mirror dinta, ta riga ta gama duk wani shirin
ta, ya akayi haka ta kasance? Wacce irin sa’a ce da yarinyar da har komai zai
kasa tasiri akanta? Me take takama dashi? Me take ji dashi? Kanta ta hau
bubbugawa a jikin bangon kafin ta fashe ta kuka, ba zata dauka ba, bata san ya
zata iya rayuwa babu shi ba, bata sani ba.

   Aikowa Bubu yayi a tafi da ita, lokacin Kilishi
na wajenta, tana bata baki, bata san me zata ji ba, da fasa nad’in Kamal din ko
da abin kunyar da Iman din ta jawo musu? Kamar mahaukaciya haka ta nufi
bangaren Bubun. Shi kadai ne a turakar sa, bayan an tashi daga zaman ne ya dawo
gida dan yana so ya huta, tension din da ya shiga a kwana biyun nan ba kad’an
bane shiyasa yace babu zaman fad’a har sai bayan kwana biyu idan ya huta sosai,
be ga muhammad ba tun bayan an tashi daga zaman, bayan ya saka an aika da bayin
nan gidan gyaran hali sai kawai ya zarto nan ya kuma bada umarnin a kawo masa
Lailan, sai gashi sun shigo ita da mahaifiyar ta, kan Lailan tsaya ta shigo sai
dai kamar wadda aka bubbugewa guiwa haka ta koma, kwarjinin Bubun ya sakata
shiga hankalin ta, fuskar sa a daure take tamau babu ko digon fara’a hakan ya
sakata shan jinin jikinta, dan bata taba ganin sa a haka ba, sosai yake sakewa
da ita har suyi hira, yana son ta sosai tamkar shine ya haife ta,sai gashi yau
ta kasa kwakkwaran tsaiwa a gaban sa, ta makale daga gefen wata kujera tana
leken fuskar sa.

  Be bi ta kan Kilishi ba, dan ba ta ita yake ba, ya kira
sunan Lailan da kausashshiyar murya, bata iya amsawa ba, sai matsowa da tayi da
jan kafa ta gurfana agaban sa.

   Sanarwar shigowar Muhammad ta dakatar da maganar
da Bubun yayi niyyar yi, ya shigo kansa tsaye zuciyar sa fes ko babu komai
yasan ya wanku tas a wajen Bubu, dama kuma babban tashin hankalin sa ace Bubun
na fushi dashi.

  Ganin su ya saka shi juyawa, amma sai Bubun ya dakatar
dashi, ya dawo ya zauna a gefe yana jin kamar dakin yayi musu kad’an, kamar
idan ya cigaba da zama yana shakar iska daya da Laila zai iya nakasta ta. Ammi
ce ta shigo tare da Iman tana bin ta a baya, fuskar Ammi fes ba zaka taba gane
halin da take ciki ba, daidai saitin kafarta Iman ta zauna kanta a k’asa sosai
kwarjinin Bubun ya cika ko ina na dakin, ganin su ya saka muhammad din sakin
ransa, ya dinga satar kallon Iman din cikin so da kauna.

  Gyaran murya Bubu yayi, ya shiga bayani da harshen da
yake tunanin duk zasu fuskanta, muryar sa na fitar da amo me tsoratarwa, babu
wasa ko digo a cikin maganar sa, ta in da yake shiga bata nan yake fita ba,
yayi wa Lailan tas, ya kuma tabbatar mata da sai ta karbi hukunci daidai da
abinda ta aikata, gaba babu wanda zai yi sha’awar aikata irin abinda ta aikata,
karshe kuma yace y haramta mata karatun nata baki daya, ta dawo gida kenan ba
zata koma ba, tunda babu abinda ta sake daukowa sai mugun hali.

  Ko gezau batayi ba, dama kuma babu wanda ya saka ran zata
girgiza ko ta tsorata, kanta dai yana k’asa dan bata isa ta hada ido da Bubun
ba, amma tana zaune kekam har ya gama ya kuma juya kan Muhammad da Iman ya sake
basu hakuri musamman Iman da ta shigo gidan ta kuma fara da karo da irin wannan
abun, kachokam ya dora laifin Lailan a akansa, ya sallame su ya zama daga shi
sai Kilishi.

  Gaba Ammi tayi zuwa bangaren ta, tare da Iman dan bata
bukatar sake jin komai hakan ma ya isa, Allah ya kawo komai cikin sauki, ba
zata kuma bata lokaci a abinda ya riga ya wuce ba, shi dama sharri dan aike ne,
duk in da yaje sai ya dawo.

   Sauri-sauri yake ya isa gida a tunanin sa Iman
chan tayi, ya matso yaji yadda akayi ta samu evidence din, a lokacin da ya riga
ya cire rai, tsaida shi Laila tayi, ya tsaya yana juyowa,

 

“Ni ka wulakanta ko cap…”

 

Ai bata kai karshen maganar ta ba, ya dauke ta da wani
gigitaccen mari, marin da ya dauke mata ji da gani na wani lokaci

 

“Ni ka mara?”

 

“Shine kawai abinda nake ganin zan miki na huce, duk da
addinin musulunci ya hane mu da dukan mace, musamman ma a fuska, amma bani da
zabi, nayi duk kokarin da zanyi nayi avoiding dinki, amma saboda ke jaka ce sai
da kika saka ni aikata abinda nake gudu, idan kika cigaba da shiga rayuwata ko?
Wallahi sai na miki abinda baki taba tunani ba.”

 

Hannun ta dafe da fuskar ta, ta kasa cewa komai har ya juya da
nufin barin wajen, cikin daga murya yadda zai ji tace

 

“Sai dai idan kashe ni zakayi, amma nayi maka alkawarin sai
ka aure ni, ko kana so ko baka so!”

 

Be tsaya ba, dan bashi da lokacin batawa, yana kyautata zaton
Laila ta haukace, ko kuma tana shaye-shayen kayan maye, idan ya biye ta zai iya
mata illa, dan yadda yake ji kamar ya saka hannu ya shake mata wuya har sai ta
bar numfashi.

 

  Sababbin masu kula da kofar ya tarar, suka gaishe shi ya
amsa musu da kai, har ya wuce ya dawo ya nuna su da yatsa

 

“Idan har na samu wani abu daga gareku, wallahi tallahi sai
kun yabawa aya zakinta.”

 

Ya wuce su yana juyo su suna bashi hakuri da alkawarin ba zasuyi
komai ba, kofar ya buga da karfi, ba zai cigaba da zama a cikin gidan nan ba,
idan ma ya zauna toh fa ba zai iya da tsarin su ba, tafiyar sa zai wata k’asar
ya huta sosai, ko da zai dawo amma sai ya tabbatar da ya samu enough time da
matar shi, ba zai yiwu wasu banzaye su nemi hana shi morewa ba,daga yin auren
sa.

  Abincin dake saman dinning ya kalla, ya wuce ya hau
bubuda dakunan yana neman ta, bata cikin ko daya, ya dudduba toilets nan ma
bata nan, ya zata nan zata wuto be yi tunanin Ammi zata bi ba.

  Dawowa yayi falon ya kwanta rigingine ya rage volume din
tv ya rufe idon sa. Bacci ne ya soma daukar sa, yaji kamar ana taba shi, bud’e
idon yayi ya ganta a tsaye a wajen kafar sa, kallon kayan jikinta yayi daga
sama har kasa, doguwar rigar material ce me budadden hannu, sai kanta dake rufe
da inner cap, murmushi tayi masa ya mayar mata yana mika mata hannu ta daga
shi, make kafada tayi alamun a ah, ya sake mika mata ta noke, marairaice mata
yayi yana sake mika mata hannun, karba tayi da nufin dagashi amma sai ya saka
karfi ya jawo ta, ta fado kansa ya saka hannu ya zagayeta a jikinsa.

 

“Dama na san haka zakayi, shiyasa naki.”

 

“Toh laifi nayi? Mutum da iyalin sa halaliyar sa.”

 

“Zuhr ake kira toh ai.”

 

“Don’t tell me azahar tayi.”

 

“Tayi, har ma nayi sallah ta.”

 

“Ohh… Ya Salam rayuwar nan tana gudu.”

 

“Wallahi, tashi toh kayi sallah.” Tace tana kokarin
daga shi, maida ita yayi yace

 

“Zan tashi, amma sai kin min tausa, I’m weak kwana biyu ban
fita exercise ba.”

 

Gefen kadarsa ta danna masa, zuwa saman chest dinshi

 

“Gashi nan na gama.”

 

“Ojoro, wannan ai ba tausa bane, danna ne.”

 

Dariya ta saka

 

“Menene banbancin?”

 

“Tausa daban danna daban, ji fa yadda kika danna min kafada
kamar wani katako.”

 

Dariya ta kwashe da ita sosai, irin wacce be taba ganin tayi ba,
tsayawa yayi yana kallon ta yana admiring dinta, komai idan tayi burgeshi yake
sosai, sai da ta lafa sannan ta ga irin kallon da yake mata sai kuma taji
kunya, ta dora fuskar ta a saman kirjinshi tana dannawa.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button