HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30

“Sarkin kunya.” Ya mike yana dagata, zama sukayi akan
kujerar ya rik’e hannun ta cikin nashi

 

“Thank you so much, kin taimaki mijinki a lokacin da yake
cikin tsananin bukatar taimako, dama mace ta gari itace me taimakon mijinta
idan ya shiga matsala, I’m very proud of you, bari nayi sallah nazo ki bani
labarin yadda akayi, I hope baki saka kanki a matsala ba ko?”

 

Girgiza masa kai tayi

 

” Ko daya, kayi sallah ga abinci na shirya mana da
kaina”

 

“Really? Kece kika girka?”

 

” Nice.” Tayi folding hannunwanta a kirjinta tana
murmushi

 

“well-done, hakan yayi min dadi, bari na zo naci girkin
amarya ta.”

 

Dariya tayi ya shige ciki ita kuma ta zauna tana jin dadi sosai.

 

***Cikin dare ya tashi, ya kalli Hajiya Layuza dake shirge kamar
kayan wanki, bayan ta hanashi sakat da zalamar sa ya samu ya bata maganin bacci
shine tayi bacci, sadaf-sadaf ya sulale ya fice yana kallon hanya sai dakin da
Zeenat take. Tura kofar yayi yaji ta a rufe, ya shiga kwankwasawa a hankali
kamar barawo, cikin baccin wahala Zeenat din ta farka taji kamar ana taba
kofar, tsoro ne ya kamata ta, ta makale a wajen daya tana zaro ido,

 

” Zeenat kina ji? Bashir ne dan Allah bud’e min. “

 

” Ba.. bazan bude ba.” Tace tana sake makalewa a jikin
ginin dakin

 

” Dan Allah ki cece ni, ki bud’e muyi magana akan tafiyar
ki gida, na samo hanyar da zaki koma gida cikin ruwan sanyi, dama naji an ce an
janye yajin aikin da jami’oi suke, bud’e kiji.”

 

” Da gaske kake? “

 

” Da gaske nake, bud’e dan Allah kafin ta gane bana nan ta
biyo ni tazo ta tafi dani. “

 

Tashi tayi ta bud’e kofar, tana gama budewa ya fado daga shi sai
gajeren wando, wani iri taji tayi saurin dauke kanta, kamar wanda yasha wani
abu kawai taga mutum yayo kanta, ya dakume ta yana kokarin rabata da kayan
jikin ta, dukan sa ta shiga yi amma kamar ingiza shi take, toshe mata baki yayi
sosai ta hanyar saka abu ya daure bakin yadda ihun da zatayi ba zai fito ba.
Duk yadda tayi kokarin ganin ta hana shi amma sam be hanu ba, sai da ya karbi
sadakin sa, ya kyaleta yana maida numfashi, kamar wanda yayi tsere da zaki.
Bayan kamar minti goma ya tashi da sauri ya fice daga dakin ba tare da ya kalli
in da take ba.

   Tun tana kuka har ta daina ta galabaita sosai, ko
hannun ta bata iya dagawa balle tayi wani kwakkwaran motsi ko ina na jikinta
ciwo yake balle uwa uba chan kasanta da take jin kamar zata mutu dan tsabar
azabar da take ji

 

 

 

2/3/22, 21:11 – Buhainat: Halin Girma

      28

 

******* �

Jan kafa ta dinga yi har zuwa wajen da jakar ta ke ajiye, ta hau
zazzage ta ko Allah zai sa taga wayar ta, tun da tazo gidan bata sake ganin
wayar ta ba, gashi tana matukar bukatar tayi magana da Mama, ji taka kamar
mutuwa zatayi saboda azabar wahalar da take ciki. Bata ga wayar ba, sai yan
kayan ta da Bashir din ya dauko mata daga wanchan gidan da yafi mata nan sau
dubu duk kuwa da rashin haduwar gidan amma chan a kalla zata samu yancin ta, ba
kamar nan da take xaune karkashin matar Bashir din ba.

  Kwanciya tayi a tsakiyar dakin, tana cigaba da rera
kukan ta, har zuwa lokacin da taji ana taba kofar, kafin ta bud’e ta zuro kanta

 

“Uban me kike wai har yanxu baki fito kin yi ayyukan ki
ba?”

 

Ta tsinkayi muryar ta har cikin kwakwalwarta, matsawa tayi amma
bata tashi ba, shigowa tayi a fusace ta mik’ar da ita, ta k’wala ihu cikin
azaba tace.

 

“Dan girman Allah kiyi hakuri bani da lafiya.”

 

Da sauri ta saketa, ta ja baya tana kare mata kallo

 

“Kutmar U! Ni Bash zai munafunta? Kan bala’i amma wallahi
sai na yi masa rashin mutunci, dan wulakanci duk yadda nake kaff-kaffa amma sai
da ya zagayo ya taba yarinyar na? Ni xai zawo wa raini!”

 

Kamar wadda ake hankadawa ta fice da sauri, Zeenat na jinta tun
daga kofar ta fara k’wala masa kira, baya kasan da ta barshi haka kuma baya
sama ya riga yasan abinda ya aikata shiyasa ya bar gidan. Sake dawowa tayi
dakin ta tashi Zeenat din tsaye da karfi

 

” Tunda har kin iya kwana da miji sai ki fito kiyi aiki,
babu wani langabewa da zakiyi wallahi sai kin min aiki.”

 

“Dan Allah kiyi hakuri wallahi zazzabi nake ji, jikina duk
ciwo yake.”

 

“Hehehe…” Ta saki shewa tana mata kallon banza gami
da tafa hannu

 

“Idan kinga na kyale ki sai dai idan mashasharar mutuwa
naga kina yi, amma wallahi tunda kika kwana da miji sai kinyi min aiki.”

 

Kuka Zeenat din take da gaske ba da wasa ba, kuma da gaske take
zazzabin take ga wani irin ciwo da ta kasa gane wanne iri ne, a lokacin ne ta
tuna wtaa rana ana ruwan sama, haka Mama ta tursasawa Iman wanke mata wasu kaya
masu yawan gaske,sannan tana wankin tana girki duk kuma a bayan, har aka kare
ruwan nan tana kaiwa da komowa ba tare da Maman ta tausaya mata ta duba halin
da zata shiga ba, a lokacin ita tana kwance a daki tana karatun wani littafin
hausa, sai bayan an gama ruwan ne ta fito ta sakawa cikinta abinci ta sake
komawa.

   Tulin kayan wanke-wanken da yake gabanta ta
kalla, ta sake fashewa da wani sabon kukan, a hankali ta zauna a gefen
dandamalin ta shiga wanke su tana yi tana kuka shabe-shabe.

   Sai da ta gama komai ta gyara gidan tas sannan ta
samu ta sakawa cikinta ruwan tea da take jin shi kadai zata iya sawa a cikin,
ta koma daki ta kudundune tana jin sanda Hajiyar ta bar gidan cikin rakiyar
kawayenta. Bayan kamar minti goma sha biyar da tafiyar ta, ta tashi ta dauki
jakar hannun ta, da mayafi ta fito ta nufi hanyar gate din gidan, fatan ta
kawai ta bar gidan idan har ta fita toh babu ita babu auren Bashir ko me za’a
iya sai dai ayi amma ta gama auren. Har taje gate din bata ga kowa ba, haka
babu me gadi a wajen tayi saurin isa kofar ta kama ta bud’e ta, sai taji ta a
rufe, ta ja da dan ragowar karfin ta amma still ko motsi kofar batayi ba, tana
haka ne sai taji alamun ana saka key ta waje, kafin ta iya barin wajen har
Bashir ya shigo sanye da sabuwar shadda kunnen sa makale da waya yana magana
yana dariya sai dayan hannun nasa rik’e da wayar ta da leda me tambarin sahad
stores.

 

“Zan kiraka oga, nagode sosai.” Ya katse kiran yana
dubanta

 

“Ba dai guduwa zakiyi ba?”

 

“Ban sani ba.” Tace tana matsawa gaba tana cigaba da
kokarin bud’e kofar dan da ya shigo rufe tayi yayi

 

“Muje ciki kiji.”

 

“Babu in da zani, na gama zama a bakin gidan nan, da
muguntar matarka, wallahi gidan mu zani ba zan iya ba.”

 

“Naji toh, amma kizo muje kinga na siyo miki chocolates
masu kyau da gasasshiyar kaza, da yogurt.”

 

“Da yake ka samu mayya ko? Toh ba zan koma ba wallahi.”

 

Sai ta fashe da kuka da karfi, da sauri ya toshe mata baki, ya
sungumeta tana ihu be ajiye ta ba sai da ya kaita dakin, sannan ya dire ta,
gani yayi idan ya biye mata zata tara masa mutane. Yana ajiyeta ya zauna a gefe
yana bud’e ledojin

 

” Nasan kinsha wahala jiyan nan, taso kisha fresh yogurt
din nan zaki ji dadi.”

 

Banza tayi masa ta cigaab da gursheken kukan ta. Ci ya hau yi
yana kallon ta, yana jin da zata yarda da ya sake zuwa karaye, amma yasan yadda
ta sha wahalar nan zai yi wuya ta amince masa, yaga kiran Hajiya wajen sau goma
amma be daga ko daya ba, dan yasan kwanan zancen yanzu ma sai da ya tabbatar ta
bar gidan sannan ya shigo, da ace Zeenat din zata amince masa da lafiya lou,
shiyasa ma ya tsaya yayi mata siyayyar yasanta da shegen kwadayi, amma sai yaga
ko kallo be isheta ba daga shi har kayan hannun nasa. Sai da ya kusan cinyewa
sannan ya tuna ya rage mata, ya mike zai fita ta tsare shi

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button