HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30

” Bani wayata.”

 

“Hauka nake? Kije ki kira min ruwa kenan, ai kinga na baki
wayar nan ko? Toh nasan me na taka in da ko kinje sai kin dawo da
kafarki.”

 

Matsar da ita yayi ya fice yaje ya dora ruwa, yayi zafi ya juyo
mata a wani babban bawo ya kai mata toilet ya dawo ya sake sungumarta tana
dukansa da komai ya kaita, ya danna ta ciki ta dinga ihu tana tashi amma sai da
ya daddanne ta har ta hakura ta zauna, sannan ya fito ya barta a ciki, ya nufi
gate ya samu me gadi ya dawo ya ja masa kashedi akan kar ya kuskura ya barta ta
fita sannan ya fice daga gidan da baya saka ran dawowar shi sai dare yayi sosai
saboda Hajjajun sa da yasan ta tama zata kare masa tanadi tsaf dan ba abinda ta
tsana kamar tarayya ita da wani akan abu guda!

 

***Tana zaune ya dawo daga sallar, ya chanja kayan jikin sa zuw
doguwar jallabiya maroon colour me kyau, bata kai masa har k’asa ba, tashi tayi
suka hadu a hanya sannan suka karasa tsakiyar falon, ta wuce zuwa dining area
din ta dauko warmers din ta dawo ta jere su a k’asan bayan ta ciro table mat ta
shinfid’a akan carpet din

 

“Me yasa zaki bawa kanki wahala bayan duk wannan aikin kina
da wadanda zasuyi.”

 

“Ban iya zama haka nan babu aiki ba wallahi, ni nama
sallame su tun dazu nace su je zan neme su.”

 

Jinjina kai yayi yana yaba mata, tashi yayi ya tayata suka
karasa sakko da sauran kayan, sannan yayi serving nasu a plate daya, da spoon
daya, debowa yayi ya nufo bakin ta yace

 

“Oya, it’s my duty bud’e bakin ki.”

 

Dariya ta saka ta bud’e bakin a kunyace ya saka mata, sannan
shima ya diba ya ci dadin girkin ya ratsa shi, lumshe idon sa yayi ya bud’e
yana ware su akanta

 

“Da gaske kice kika yi abincin nan?”

 

“Da gaske!”

 

“Wow… Alhamdulillah Ya Allah, I’m blessed ta ko ina,
Allah nagode maka, abincin nan yayi dadi sosai,Allah yayi miki albarka.”

 

“Amin.”

 

Ta amsa tana jin dadi sosai, babu abinda mace take so irin idan
tayi abu a yaba, tana fatan ya dore har gaba, hakan yana karawa mace karfin
guiwa wajen kyautata ma mijinta. Cikin nishadi suka gama cin abincin, ya sake
tayata suka tattare kayan zuwa kan dining din, in da masu aikin zasu kwashe
daga nan zuwa kitchen. Falon suka dawo suka zauna, ya matso kusa da ita ya
ajiye kansa a saman kafarta, yace

 

“Ina jinki, bani labarin yadda akayi.”

 

Dan muskutawa tayi ya gyara shima, tayi murmushi me sauti ya
maida mata yana jan kunnensa

 

“Na matsu naji!”

 

“Abinda ya faru bayan ka fita, na dawo daki na zauna ina
tunanin mafita, duk tunanin da zanyi nayi babu wani abu da nake ganin zamu iya
rik’e shi a matsayin hujja, duk da haka ban karaya ba, inaji da yakinin Allah
ba zai bata nasara ba, hakan ya saka ni tashi na dauro alwala, nazo nayi
nafila, na sake rokon Allah akan ya taimaka ya bayyana gaskiya, bayan na idar
ne kawai nayi deciding bari na shiga kitchen na ga abinda yake wakana, domin a
rayuwa ta kitchen na daya daga cikin wuraren da ya zama tamkar daki na, domin
nayi masa sabon gaske. Na tarar da ma’aikata da yawa suna ta hada-hadar hada
girki, shine na karbi aikin namu, nace su ji da nasu. Muna aikin ne sako ya
iso, a cikin envelope din nan…”

 

Ta nuna masa tana mika masa

 

” Flash ne a ciki, wai inji wata mata sanye da nikaf tace a
bani, a haka sakon yazo.”

 

Jujjuya envelope din yake a hannun sa, tambarin gidan ne a jikin
envelope din, wanda ba kowa ne yake samun ta ba sai jinin gidan… Cigaba tayi

 

“Shine nazo na saka a jikin Tv, abinda na gani ya saka ni
rawar jiki, nayi sauri na nufi daki na dauko system dinka da kayi amfani jiya,
naci sa’a na sameta a bud’e, na saka flash din a jiki nayi copying komai a
wayata sannan na tura maka, na kuma kiraka da nufin nace ka duba amma kuma har
ta gama ringing baka daga ba, a lokacin babu irin tashin hankalin da ban shiga
ba, na dinga kaiwa da komowa a tsakani ina fatan ka daga wayar ko kuma ka duba
sakon kafin lokaci ya kure. Ganin shiru shiru babu alamar zaka daga, sai na
yanke shawarar zuwa da kaina, har fadar dan ba zan iya jurewa ba, har na dauki
abinda zan dauka na fito na kuma kira wadda zata rakani, sai ga kiran ka.”

 

Zaune ya tashi ya jere da ita akan kujerar, yana cigaba da
jujjuya envelope din, yana son gano wanda zai aiko da sakon, duk iya tunanin sa
be samu amsa ba, sai ya ajiye a gefe ya rungumota jikin sa yana murmushi

 

“Thank you so much Baby, nagode sosai da kokarin ki.”

 

“U welcome.”

 

“Ashe dai Ashe ana so na tunda har ake kishi na.”

 

“Kishi kuma?”

 

“Ehen menene? Kishi ne mana, hadda kuka fa daxu da zan
tafi, kamar wanda zai tafi filing daga!”

 

Sai ya tuntsure da dariya yana gwada yadda ta riko shi, turo
baki tayi tana tashi daga kusa dashi

 

“Tayaka jimamin abun nake fa, aiko ba zan kara tayaka
ba.”

 

” Fadi gaskiya dai, kinga za’a kwace miki handsome mijinki,
hankali ya tashi.”

 

” Na shiga uku.”

 

” Ba haka bane? Kinga hanci zur har baka, yarinya taga
handsome guy tace idan bani ba sai rijiyar kusugu.”

 

” Allah kaiko?”

 

” Ai gaskiya ne, ki rantse ba kishi bane.”

 

Shiru tayi ta kyale shi, ta lura yana da so wasa da tsokanar ta,
is like kamar ma yafi jin dadin sakata a gaba yayi ta tsokana, amma ka ganshi
da sauran mutane kamar bashi ba.

 

   Bayan yayi sallar la’asar ne ya sake chanja kaya
ya fita, lokacin yaran sojojin sa sun iso, dama sunyi waya akan suna hanya,
yazo ya baza su a kofar shashen sa in da babu shegen da zai sake gigin shigar
masa, balle har wani abu ya faru, duk da ma ba wani zama zai ba, sati daya zasu
kara ya tattara yayi tafiyar sa Kano daga nan kuma yana tunanin ma k’asar zai
bari, ya rasa yadda zai da abokan aikin sa da suka ce sun shirya masa
kayataccen bikin sword crossing gashi har date din ya wuce sun sake
rescheduling wata ranar, dole ya yarda dan sun kashe kudi sun kuma gayyaci manyan
mutane, shiyasa kawai ya hakura yace zasu zo, daga nan sai suje su ga
mahaifiyar Iman din daga nan suyi tafiyar su Kano Adamawa sai an Baba ta gani.
Akwai tafiyar da zasuyi akan wani babban assignment daga wajen aiki duk da ba’a
saka rana ba, amma baya so tafiyar ta zo nan kusa, yafi so sai sun je sun dawo
ma, amma zai sake tuntuba yaji, yaji kuma iya dadewar da za’a yi idan yaga za’a
shiga rayuwar sa zai iya fadawa dan baya son abinda zai saka shi yin nisa da
Iman din, musamamn ya barta a gidan su ita kadai, be yarda da kowa ba, haka nan
be yarda da duk wanda ya aiko da flash din nan ba, akwai wani hidden bayani a
k’asa, ya riga yasan gidan su, ya san abinda za’a iya da wanda ba za’a iya
ba,be kuma san iya adadin mutanen da suke son ganin bayan sa ba, duk da ya nuna
bashi da ra’ayin saurata ko kad’an, amma ya tabbatar da akwai wadanda suke
tsoron sauyawar ra’ayin sa, wanda suke gudun wani abu ya faru ba abinda suke
fata ko suka tsara ba.

   A wajen Bubu ya shantake dan tare sukayi har
sallar magriba yayi masa tas akan abinda ya aikata dazun akan sakon gwamna, duk
da yaji dadi a kasan ranshi amma be nuna masa ba, sai ma fad’a da yayi masa
akan kar ya sake, ya amsa da toh ba zai sake ba, sannan suka cigaba da hirar su
irin wadda suka dade basu yi irin ta ba.

  Ana magriba Ammi ta aiko kiran Iman din, ta tashi cikin
rakiyar hadiman ta suka nufi wajen Ammin in da ta tarar da wasu baki wanda daga
gani masu muhimmanci ne ga Ammin, gaishe su tayi a ladabce bayan ta gaida
Ammin, sannan Ammi ta gabatar da ita a matsayin matar Muhammad suma ta gabatar
dasu ga Iman din, matar gwamnan Adamawa ce da yarta wadda Iman din ta lura da
girman kanta, dan tun shigowar Iman din ko daga kai batayi ta kalle ta ba, tana
ta danna waya tana cin chewing gum. Share ta ita ma Iman din tayi, suka cigaba
da zaman shiru bayan tashin Ammi da matar suka shiga ciki suka barsu. Wayarta
ta kara a kunne, tana yatsine kafin tace

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button