HALIN GIRMA 26-30

“Moha gani a part din Ammi fa.”
“Wallahi tun dazu ma, zaka shigo?”
“Owk ina jiran ka.”
Satar kallon ta Iman tayi suka hada ido, sai ta dauke kanta
kamar bata gane me take magana akai ba. Suna zaune a haka har wajen minti
talatin kafin kofar part din ta bud’e, ya shigo yana kokarin daidaita kallon sa
akan Iman da take zaune ta dayan bangaren.
“Ina chan ina jiranki ashe kina nan kin ma manta dani
ko?”
Yayi maganar yana zama a hannun kujerar da take kai
“Nazo gaida Ammi ne, sorry na maka text baka gani ba?”
“Sai yanzu na gani fa, shine nayo nan da sauri na.”
Dariya tayi, ta dan taba shi alamun kai ko? Gyaran murya suka
je, ya kalli wajen
“Samha! I’m so sorry na manta munyi magana kince kina nan,
gaba daya hankali na yayi gaba wallahi,.”
“Uhm ba komai, ai kana tare da Madam.”
“Yes yes wallahi kin ganta, Baby ga Samha my
classmate.”
“Allah sarki sannu.”
” Sannu.” Tace a gajarce tana dauke kai
“Samha this is my wife, baki zo biki ba zamu ciki
tara.”
Yak’e tayi
“Bana k’asar time din, naga Amarya Allah ya sanya alkhairi,
Laila ta fad’a min ai.”
” Kin gama mu wuce?”
Yace yana bagarar da zancen jin ta sako maganar Laila
” Ai bance ma Ammi zan tafi ba.”
” Owk bari na fad’a mata.” Ya tashi shiga ciki, ya
barsu su biyu, murmushi ne a fuskar Iman, a kalla taji dadi da yadda muhammad
din yayi dan ta gane sarai so tayi ta kunsa mata haushi shine har da kiran sa a
gabanta. Be dade da shiga ba ya dawo yace ta tashi su tafi, suka fice suka
barta da bakin ciki. Suna fita ta dauki waya ta kira Laila
” Wai baki dawo ba?”
” Na kusa shigowa ki jirani.”
” Ina nan ina jiran ki, ashe rabon zanga kayan bakin ciki,
haka Muhammad yake rawar kafa akan yarinyar nan?”
” Me yayi?”.
“Kinga yadda ya narke mata kamar bashi ba, kinsan dai
tsaurin sa ko? Toh wallahi a gabanta kamar ruwan sanyi haka ya koma, ni kaina
baki ga yadda ya amsa min a sake ba wallahi, kamar fa bashi ba.”
” Toh an fad’a miki haka ta barshi? Bari kawai na karaso
muyi magana.”
” Shikenan kiyi sauri please.”
Suka ajiye wayar, jefar da tata Laila tayi a gefen ta, ta shiga
jan tsaki a jere cikin bacin rai.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/7/22, 09:08 – Buhainat: Halin Girma
   29
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
******* �
Tana daf da shigowa ta kira Samha tace ta wuce part dinta dan ba
zata iya zuwa wajen Ammi ba, tashi tayi ta fita bayan ta saka wayarta a cikin
purse dinta, taja kofar ta nufi wajen Laila din da ya kasance nata ita kadai
kusa da na Kilishi. A waje suka hadu ita tana fitowa daga mota ita kuma tazo
daidai bangaren, sallamar driver tayi yaran suka dauko mata kaya suka biyo ta,
suka hadu suka rankaya ciki tare da Samha. Bayan sun zaune ne Lailan ta tuge
mayafin kanta da yake dan yalolo da ta yane kan, ji taka kamar iska bata ratsa
kan nata sosai shiyasa duk take jin ranta a jagule babu dadi, ga haushin abinda
ya faru ga na karatun ta da take jin kamar ta rasa komai a yanxu.
“Kin ganki kuwa Queen, ya akayi haka?”
“Menene ma ba zaki gani ba, hmm wallahi bansan waye yayi
min zagon k’asa ba, amma ko waye toh tabbas baya kaunata ko kad’an!”
” Kin binciki Hadimar nan? Ba kince ita kadai tasan da plan
din ba.”
Girgiza kai tayi
” Ba ita bace ba, someone very close to me ne, dan yadda ba
kowa ke shiga part din nan ba, toh lallai wanda yake da direct access da part
din ne.”
” Lallai, gaskiya ko waye be kyauta mana ba, yanzu ya ake
ciki?”
” Wai hakuri? Wallahi ban ba,kinsan yadda nake son Capt tun
muna school haka shima kinsan kaunar da yake min ba kad’an bace, ba zan iya
rayuwa da kowa ba sai shi, bayan haka kinsan matsala ta da Dr. Bryan
Ford.”
” Haka ne, toh shikenan yanzu menene next move dinki?”
” Har yanxu ban dawo daidai ba, I need time to recover
nasan me zanyi.”
” Shikenan, duk abinda zakiyi dai kiyi informing dina, zan
baki shawara yadda ya kamata.”
” I know I can count on you, Nagode Bestie!”
“DM!”
Tayi murmushi yana
relaxing sosai akan kujerar, tana tunanin yadda zatayi amfani da Laila ta samu
cikar burin ta!
Sai wajen tara sannan
suka tafi, bayan Maman sun gama zantawa da Ammi, babbar aminiyar ta ce sama da
kowa a kaf adamawa dan da ita ta fara sabawa lokacin da aure ya kawota, sannan
yaransu ma tare suka taso ita tana da yara biyar compared to Ammi da take da
guda daya tal…
Zuciyar ta fari kal sanda
suka isa gida, ta san ko babu komai zata dinga samun duk information din da
take so ta bakin Laila, tunda tayi masifar yarda da ita fiye da yadda ma ta
yarda da uwarta mahaifiya. Bata da kirki ko kad’an idan har ka shiga gonar ta,
amma kuma tana masifar ganin mutuncin Samha din, dan itace tafi mata kowa a
yanzu, gani take ma babu me kaunar ta sai Samha din kawai. Ko Kilishi ta san ta
Kamal kawai take yi ba tata ba, shiyasa itama bata wani sanar da ita idan
zatayi abu sai dai daga baya, daga Samha sai amintacciyar hadimar ta guda daya
wadda zata iya bada ranta fansa ga Laila din saboda tsabar biyayyar da take
mata.
Wurgi tayi da tarkacen
da ta debo daga mota tayi a saman gadon ta, ta kwanta tana kallon sama ba tare
da ta cire dogon takalmin kafarta ba, murmushi take ita kadai duk kuwa da
abinda Muhammad din yayi ya bakanta mata rai, amma kuma ta raina yarinyar da ya
kira ta da matarsa, a shekaru ba wata babba bace haka ma wayewar rayuwar duniya
sam bata cikin sahun amma kuma tana da nutsuwa a yanayin ta, da kuma iya
handling abu dan yadda tayi da taji da wanda take waya ya matukar bata mamaki,
kamar bata fahimci komai ba bayan sarai ta gane, kuma bata ko bi takanta ba ,ko
ta tuhume shi ko ta chanja masa fuska sanda ya shigo, sai ma ta tarbi mijinta
da fara’ar da ta mantar dashi komai da kowa.
Tashi tayi tsaye ta soma
zagaye a tsakanin dakin tana jin kamar taje ta jawo ta da karfin gaske ta fidda
ta daga gidan, duk yadda suka kai da wayewa amma ya tsallake su ya dauko wadda
bata kai ko rabin ajin sa ba, adah Laila kawai take jin haushi amma yanzu na
Laila ya daina damunta, dan tasan babu wani abu da zatayi sai da sanin ta,
yarinya karama ce yanzu take neman zame mata ciwon ido.