HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 26-30

***Suna shiga part dinsu tun daga kofa ya daga ta sama, ta saki
siririn ihu tana kankame shi, da gaske taji tsoro dan bata yi tunani ba, sai ji
tayi anyi sama da ita, kin ajiyeta yayi sai da ya kai karshen falon sannan ya
zaunar da ita ya bita ya zauna a gefenta yana dariya

 

“Kin fiyaa tsoro Allah!”

 

“Ai it was unexpected shiyasa.”

 

“Ba wani, tsoro dai kawai, ki yarda, you have to be strong,
kinsan dai ance a wife of a soldier is a soldier!”

 

” Wasa suke suma wallahi.” Ta saka dariya

 

” Haka dai aka ce.” Yayi dariyar shima

 

 

“Yawwa… Dazu na gani a WhatsApp wai anyi calling off
strike?”

 

” I can’t say, bari na kira naji, amma zaki koma ne? Ko a
samu wata school din daban?”

 

” Duk yadda akayi yayi.”

 

” Owk toh bari naji.” Yace yana ciro wayar sa daga
aljihu, yayi dialing number wani lecturer abokin sa, suka gaisa sannan ya
tambaye shi, baa gama daidaitawa ba amma dai akwai yiwuwar komawar nan kusa.
Ajiye wayar yayi ya fad’a mata yadda sukayi

 

“Matsalar k’asar nan kenan, yanzu fisabilillahi fiye da
9month ana strike amma gwamnati tayi shiru? Shikenan karatun yara ya lalace
akan wani dalili mara tushe, it’s so unfortunate gaskiya.”

 

“Wallahi har sai mutum ma ya gaji da zaman, babu dadi
sam.”

 

“Dole ai, Allah ya kyauta.”

 

“Amin.” Tace sai sukaayi shiru, chan kuma yace

 

“Bari muga idan basu daidaita ba, kawai sai mu chanja ko
Base ne, ko kuma wata private uni din na Kano.”

 

“Owk Allah ya zaba mana mafi alkhairi.”

 

” Amin Matata!”

 

*** Tare suka shiga ciki bayan sun kammala duk abinda ya kamata
su kammala a falon, zama yayi ya kunna system ya shiga aiki ita kuma ta wuce
toilet dan ta watsa ruwa tazo ta kwanta. Sharp sharp tayi wankan ta fito sanye
da rigar da ta cire , be kalle ta ba, har ta isa gaban wardrobe ta dauki wata
mara nauyi iyakar ta kasan guiwa, dan duk sauran kayan da take dasu anan ba
zata iya kwanciya dasu ba, idan ma ta saka tasan shi, zai iya yin karfa karfa
ya hanata yayi amfani da damar yayi mata wayo. A gajiye take jin ta yau din ba
wai don tayi wani aiki ba, bata san dalili ba gaba daya jikin ta ciwo yake
mata, wankan da tayi take saka ran zai dan saka taji dama-dama.

  Kallon ta yayi bayan ta
sako rigar, yayi mata alamar tazo, ta taho ta zauna agefen sa, ya cigaba da
aikin da yake na hada kan wasu takardu masu muhimmanci sosai, yana lura da ita yadda
jikinta yayi sanyi sosai, jawo ta yayi bayan ya dan matsar da system din, ya
kwantar da kanta a jikin shi

 

“Goodnight sweet dreams.” Ya rankwafo yayi mata peck a
kunci, lumshe idon ta tayi bacci na cin karfin ta sosai. Be san iya adadin
awoyin da ya dauka a wajen ba, ya dade sosai har sai da ya fara jin
bishi-bishi, sannan ya rufe system din, ya gyarata a hankali sannan ya tashi
yana mika, alwala yayi yazo yayi sallah raka’ah biyu, ya lura da ko shafa’i da
wutri da ta saba yau bata yi ba, be san wanne irin bacci take ji haka ba, dan
har ya gama aikin sa ya tashi ko motsawa batayi ba. Taimaka mata yayi zuwa
gadon ya kwantar da ita ya lullube mata iya kafarta, sannan ya kwanta bayan ya
rage kayan jikin sa ya rage daga shi sai boxer kawai.

  Cikin dare sosai taji
ishirwa, irin wadda bata taba jin irin ta ba, tashi tayi ta lallaba ta fito
bayan ta duba fridge din dakin ta tuna babu ruwa a ciki, ta manta kuma bata
kawo ba dan bata bar kowa cikin masu aikin sun taba shigar mata dakin ba,
iyakar su falo shima dan babu yadda zatayi ne amma ko yaushe suna BQ sai wani
abu me muhimmanci sannan take kiran su.

   A kitchen ta samu
ruwan, tasha sannan ta dauko karamin katan na ruwan ta taho dashi. Falon yayi
dim amma kuma akwai dan haske kadan da ya hasko ta corridor din kitchen da yake
a kunne, kafarta take sawa a hankali tana tafiyar har ta kai tsakiyar falon, da
yake falo ne katon gaske da sai kayi tafiya tsakanin kitchen da corridor din
bedrooms din, motsi taji kad’an kad’an, tana matsowa yana karuwa har ta kusa
kai wa corridor din abinda ta gani a wajen ya sakata daskarewa a wajen. Chak ta
tsaya ta kwalla wata irin kara da ta tashi Moh daga bacci, ya mike a firgice
yana kiran sunan ta, sai kuma yayi hanyar fita daga dakin da sassarfa kirjin sa
na bugawa da karfi!

 

 

 

 

BIYAN BASHI ⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️😂😂😂😂😂

2/7/22, 19:06 – Buhainat: Halin Girma

      30

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

******* �

 

A durkushe ya ganta tana kuka ta rik’e kanta, saurin durkusawa
yayi a gabanta yana janye hannun nata

 

“Menene?”

 

“Miciji!”

 

Tayi maganar tana nuna masa wajen, saurin kalla yayi amma be ga
komai ba, ya yunkura zai tashi ta kankame shi sosai tana fashewa da kuka.
Hannun ta ya kama zuwa wajen switch din falon, ya kunna haske ya bayyana a
ilahirin falon, wurwurga idonsa ya dinga yi a gaba dayan falon amma be ga komai
ba,

 

“Aina kika ganshi?”

 

“Adaidai nan zai shiga dakin chan!”

 

“Tsaya .” Ya tsaida ita yana sake dubawa amma babu
komai. Riketa yayi ya kaita daki, tayi saurin rikeshi ganin zai fita

 

” Dan Allah karka fita ka barni.”

 

” Kinaji? Calm down babu abinda zai faru, yanzu zan
dawo.”.

 

Sakin sa tayi, ya fita ya taso securities din a gaba, suka zo
suka hau bincika falon da ko ina na part din,ciki ya koma ya sameta ta
kudundune a saman gadon still jikinta be bar rawar da yake ba, tana addu’a kasa
kasa, daga gani kasan ta tsorata sosai dan bata taba ganin shi haka a zahiri
ba. Jawota yayi jikin sa, ya mannata da kirjinsa yana shafa mata baya kad’an
kad’an.

 

” Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin
ki.”

 

Da kai ta amsa masa, zuwa lokacin ta fara dawowa nutsuwar ta,
sai wani uban juyi da taji cikin ta nayi,ta dora hannun ta a saman cikin yana
yatsine fuska, kallon hannun nata yayi, ya dauki nasa ya dora a saman nata yana
tayata shafa cikin,

 

“Ciwo?”

 

“Eh.”

 

“Sannu zai daina, bari na dubo ko sun gama dubawar.”

 

Ya kwantar da ita ya fita, a tsaye ya same su rik’e da abu me
kama da maciji, matsawa yayi yana dubawa cikin son karin bayani

 

“Macijin roba ne ranka ya dade!”

 

“Roba?” Yace cikin yanayin mamaki

 

“Me ya kawo shi nan? Me yasa bamu ganshi ba tun da rana sai
yanzu…”

 

“Waye da waye suka shigo part din nan?” Ya fad’a yana
daure fuskarsa tamau. Rantse rantse suka hau yi, kowa na son kare kansa, wata
uwar tsawa ya daka musu, duk suka nutsu suka kame suna masu saukar da kansu
k’asa

 

“Kwana daya tal na baku, ku gano wanda ya shigo part din
nan har ya ajiye wannan shirmen, koma waye sai ya fuskanci hukunci me
tsanani!”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button