HALIN GIRMA 26-30

” Yes sir!”
Har ya juya sai kuma ya tsaya.
” Get ready, we are leaving tomorrow in the
afternoon!”
” Yes sir!”
Suka kara hada baki wajen fad’a sannan ya juya ya bar su a wajen
da sassarfa. Dayan dakin ya shiga, ya hau bincike wasu kaya da sauri da sauri,
ba zai yarda a taba masa ita ba, idan har ba zasu iya tsayawa iya kansa kawai
ba, toh zai yi abinda zai girgiza su matuka. Ya dan dau lokaci a dakin, sai da
ya tuna ya barta ita kadai ya kuma san tsoro take ji, sannan ya koma da sauri,
ya tarar bacci ya dauke ta, ta takure waje daya tana fitar da numfashi kad’an
kad’an. AC din dakin ya rage, zuwa low ya dawo ya gyara mata kwanciyar, ya kura
mata ido yana jin son ta na kara ruruwa a zuciyar sa, ba zai bari banzar
al’adar gidan su ta taba ta ba, zai yi duk abinda zai yaga ya kareta da dukkan
karfin da yake dashi.
  Da asubah ya tashe ta, sukayi sallah a dakin,
sannan ya fita ya shigo mata da micijin robar yana mata dariya
“Matsoraciya, nina fa na shigo dashi jiya by mistake, abun
wasan yaran chan ne suka bani, ashe sai na yar dashi ban ma lura ba.”
Shiru tayi tana kokarin daidaita maganganun nasa da abinda ta
gani, idan har ba gizo idon ta yayi mata ba, toh tabbas tafiya ta ganshi yana
yi, har ya kai kofar dakin kafin ta daina ganin sa.
“Common!” Yace yana son dauke tunanin ta
“Babu komai fa I promise you.”
“Amma na ganshi fa yana motsi!”
“Imagination ne kawai nothing else, karki damu ki kwantar
da hankalin ki.”
Shiru tayi tana kallon sa, yanayin sa yayi mata kama da na wanda
yake so ya dauke hankalin ta, amma idan ba haka ba babu yadda za’a yi taga abu
yana tafiya da idonta ya zama imagination kuma, hore mata idon yayi yana jawo
ta jikinsa
“Karki yi ta tunani kinji? Anjima zamu wuce ma, Abuja zamu
fara zuwa na gaida Mummy, daga nan muyi tafiyar mu gidan mu mu sha soyayyar
mu.”
“Da gaske?”
“Da gaske mana, are you happy?”
“Naji dadi sosai, bari na fara hada kaya na, da wuri zamu
tafi ko? Ko sai da yamma.”
“Yamma!”
Komawa tayi ta zauna tana jin kamar yamman ya mata tsayi
“Zanga Aji ne, sannan bana son kowa yasan mun tafi sai Ammi
kawai, shiyasa ba zamu dauki yaran chan ba, i mean ma’aikatan gidan, akwai
screening da za’a yi musu kafin su biyo mu.”
” Owk Allah ya kaimu.”
” Amin my beautiful wife.”
Murmushi tayi, ya dauko musu al’qurani me girma suka shiga
karantawa, ya dinga admiring muryarta da yadda take bawa kowanne harafi hakkin
sa, cikin nutsuwa da fitar da tajweed a duk in da ya dace. Sai da rana ta fito,
sannan sukayi wanka, suka shirya a tare suka fita don karyawa, bud’e warmers
din yayi, ya kakkala sannan ya saka aka kwashe masa su daga wajen, ya aika part
din Ammi aka karbo musu breakfast din, taso ya barta tayi amma ya hanata, ya
kuma ki gaya mata dalilin da ya saka shi sawa a kwashe abincin da aka girka a
part din, bata ce komai ba, ta barshi a zuwan kawai zata ji koma menene daga
baya, dan ta lura yadda ya boye masa kanta kafin aure akwai abubuwa da yawa da
yake boyewa a yanzu ma, duk da haka ba zata zarge shi ba, zata bashi lokaci
sosai ta kara fahimtar shi, jikinta na bata akwai wani abu da shi kadai ya
sani, sai ko Aji da take ganin kusancin su yafi na kowa hatta mahaifiyar sa da
mahaifin sa.
 Bayan sun gama breakfast din ne ya fita, cikin shigar
kayan sojoji da suke masifar yi masa kyau, cikin rakiyar yaransa ya nufi part
din Kilishi, wanda tun kafin ya karasa sakon zuwa nasa ya ishe mata, tana zaune
ta gama karyawa, tashi tayi da sauri ranta na baci, tasan zuwan sa babu abinda
yake jawo mata sai bacin rai. Daki ta shiga ta chanja kaya, ta zauna tana jiran
sanarwar isowar sa. Tana jin sanda ya shigo, dan har falon ta na ciki ya shigo,
ya zauna fuskar sa fes dauke da farin ciki, idonsa na kan kofar da zata fito,
ya dan dauki lokaci a zaune har ya fara tunanin ko ba zata fito ba, agogon
hannun sa ya kalla, ya daga kai ya kalli na jikin bangon dakin, a tare suke
tafiya dakiya daya, sauke idon sa yayi yana murza agogon nasa, takun tafiya
yaji, yaki d’agowa amma yasan itace,sai da ta zauna sannan ya dago yana
dubanta, yayi murmushi cikin salon girmamawa yace
“Barka da gida ranki ya dade.”
“Barka dai, ya iyali?”
“Lafiya kalou kalou, kamar yadda kike fata a kowanne
lokaci.”
Yak’e tayi, tasan magana ya fad’a mata, dan ya saba gasa mata
ita dama, murmushi ya sake yi yana lankwasa hannayen sa baya
” Haka ake so ai, sai a sake kula sosai.”
” In Sha Allah, za’a kula kulawa me kyau, duk wani me
sharri Allah zai maida masa kansa ma, saboda addu’a itace makamin mumini, kuma
matakin duk wata nasara.”
” Haka ne!” Tace tana gid’a kanta. Mikewa yayi cikin
salo na burgewa, ya dan rankwafa yace
” Na barki lafiya!”
” Nagode!” Tace tana danne zuciyar ta, bayan sa tabi
da kallo har ya fice gaba daya,
“Ahhhh!” Tayi kara tana jifa da trow pillow din dake
kusa da ita,kamar ta shako shi haka taji, gashi kamar masifa yasan duk wani
shirin ta, ta rasa yadda zatayi dashi ya zame mata tamkar kadangaren bakin
tulu! Ya kuma zame mata ciwon ido, da za’a bata makami ace ta kashe mutum daya
toh tabbas shi zata kashe, bata son ko ganin wulgawar sa.
  Laila ce ta shigo, ta tarar da ita cikin halin da
take ciki na bacin rai, bin ta tayi da kallo har ta dauki jakar ta, ta bud’e ta
dauki ATM cards din Kilishin, ta juya zata bar dakin.
“Laila!” Tsayawa tayi ta juyo
“Ina zaki? Me kuma zakiyi da Atm dina?”
“Haba Mah, tunda har na dauka ai amfani zan dashi.”
” Shine ba zaki iya fada min ba?”
” Da ma fa na saba dauka kuma bana fad’a miki, why
now?” Sai ta juya ta cigaba da tafiyar ta
” Zan dawo dashi wani payment kawai zan.” Sai data kai
karshen kofar sannan ta fad’a, ta saka kai tayi ficewar ta, kwafa Kilishin tayi
ba tare da ta sake cewa komai ba.
****Bayan fitar sa ne tana zaune da waya a hannun ta suna
chatting sama-sama da Ya Maryam,rabin hankalin ta na kan Tv sai tana duba sakon
lokaci zuwa lokaci, ta kira Abba bata same shi ba, kila ko ya fita ko kuma baya
kusa da wayar. Kara wayarta tayi a tunanin ta Abban ne, sai taga number Ya
Maryam ce, dauka tayi tana tashi zaune
“Ina ta magana a whatspp kin sauka, yanzu aka kira ni a
gida Aunty Bilki ta haihu!”
” Dan Allah!”
” Wallahi yanzun nan kuwa ta haihu.”
” Masha ALLAH, me aka samu?”
” Ina ma na tsaya tambaya? Murna ta saka ni kiranki, kinga
al’amarin Allah, bayan ta cire rai, dama ba’a cire rai da rahmar
Allah.”
” Wallahi, kai Masha ALLAH, nayi murna sosai Allah ya bata
lafiyar shayarwa.”
” Amin ya Allah, zuwa kano ya kamaki.”
” Gaskiya, dama yau zamu bar nan din, amma Abuja zamu wuce
daga nan zamu dawo Kanon.”
” Ah shikenan ma, ki kirata toh kafin nan, bari na kira
Amira itama na fesa mata.”
” Owk ki tura min number ta, Inaga kamar bani da ita
yanzu.”
” Ok tam, zan ajiye miki a WhatsApp.”
” Yawwa.”
Ajiye wayar tayi farin ciki na kamata, after all a karshe dai
itama ta samu nata babyn, shekara ashirin da aure amma bata taba ko batan wata
ba, sai yanzu Allah yayi, dama dai sunji kishin kishin din ciki ne da ita
musamamn da bata zo bikin da akayi ba, sai mutane suka kara tabbatar da zargin
su, boye labarin sukayi sun fi so kawai aji haihuwa daga sama. Duk da bata da
yawan magana amma tana masifar son kananan yara, musamman jarirai zuwa 4years
haka, ko magana sukayi sai taji dadi, shiyasa take son kaninta Marwan ba kuma
tajin komai idan Mama ta sakata aikin sa.
  Daukar number aunty bilkin tayi, ta kirata tayi
mata murna sosai, suna wayar kiran Abba ya shigo, ta katse na Aunty Bilkin ta
daga nasa suka gaisa, anan yake fad’a mata labarin haihuwar ta nuna kamar bata
sani ba tayi farin ciki sosai, bayan sun gama wayar ne ta kira Mamma take fad’a
mata zuwan su, amma bata san ko a yau din zasu iso ba ko sai gobe dai, murna
tana jiyo su Amaan ta wayar kamar zasu shigo ciki saboda karadin su.
 Â