HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 8

Ji tayi kukan na sake taso mata, dan dama idan kana cikin halin kuka aka matsa maka da tambaya ko ana so ka maida zance sai kaji sabon kuka ya taho maka,

“Ba komai da gaske ba komai.”

“Dan Allah ki fad’a min menene?”

“Mamana na tuna.” Ta fad’a masa saboda kawai ya kyale ta da tambayar

“Kiyi hakuri, akwai abubuwa da yawa da nake son sani, I ll call you idan na koma, ki daina kuka kinji? Komai zai wuce in sha Allah.”

“In Sha Allah.” Tace tana daidaita kanta.

“Kinyi alkawari kin daina kukan ko?”

“Nayi.”

“Nagode, zan kiraki.”

“Shkenan ka gaida gida.”. Juyawa tayi ta koma ciki shi kuma ya fita ya tarar da Musaddik ya cika yayi fam kamar zai fashe.

“Muje ko?”

“Allah iyakata wajen bishiyar chan, ka kirasu suzo su dauke mu wahalar tayi yawa ai.”

“Naji muji toh.” 

Ya ciro wayar sa ya kirasu cikin kankanin lokaci suka karaso, har suka isa babu wata magana tsakani Musaddik ya sauka su kuma suka wuce.

  A gaggauce ya gama komai ya shirya cikin kayan sa masu kauri, ya zauna yana jawo wayar sa, kafin ya kirata ya samu kiran DG, yayi saurin dagawa yana karawa a kunne. Gaisuwa sukayi ya bukaci ganin sa a Abuja idan an shiga working days, da toh ya amsa masa sukayi sallama ya juya akalar kiran zuwa number Ammin sa. 

“Ammi na barka da dare.”

Yace sanda ta daga wayar

“Barka dai yarona, kana lafiya?”

“Lafiya lou Ammi, ya gida da kowa da kowa.”

“Kowa lafiya, ya aikin naka?”

“Alhamdulillah Ammi, babu dadi gashi ina missing dinki sosai.”

“Ban yarda da wannan zancen naka ba, idan da gaske ne ai kasan in da nake.”

” Ina na zuwa ai, ranar ma wani aikin ne ya taso urgent shiyasa na tafi.”

” Ku kenan aiki, Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

” Amin Ammi, naje naga Takawa ai, har munyi magana ma akan maganar da Bubu yayi min.”

” Eh naji kuwa suna waya jiya, sai dai bamu zauna munyi maganar ba, me yace maka?”

” Akan yarinyar ne dama Ammi, mahaifin ta yace nazo na ga wanshi ya bani izinin zuwa wajenta.”

” Ina jinka.”

” Toh nayi magana da Takawa akan idan har zuwa gidan su ya taso ba sai kowa yaje daga royal family ba, a samu wasu cikin mutanen Takawa din da ya aminta dasu suje neman auren.”

” A wanne dalilin kenan? Ina ka taba jin anyi irin wannan shirmen Muhammad? Idan ma anyi hakan an fad’a maka ba zasuyi bincike akanka ba kafin su baka izinin ganin yarsu ba? Ai dole ne iyaye na kwarai su yi bincike sosai su san wa zasu bawa yarsu.”

” Nafi son duk wannan yazo daga baya Ammi, dama dole su sani amma ba yanzu ba, marikiyar yarinyar ce matsala, idan har taji da wuri zata iya bata abun dan ta jima tana bata wa.”

” Idan hakan ne matsala, toh ka bar komai a waje na, karka manta wanne gida kake magana Muhammad, wargi ma ance waje yake samu, bata isa tayi komai ba idan har taji kai din waye, gaba da gabanta fa, ka daina tunanin komai kayi addu’a, har naji inason yarinyar da dukkan zuciya ta, Allah ya sa ta zama abokiyar arzikin ka.”

” Amin Ammi, in sha Allah ma ba zata sani ba har sai ranar, zanyi duk yadda zanyi bata sani din ba, yadda abin zai dake ta, kuma nayi alkawarin hukunta ta daidai da abinda tayi.”

” Ya sunan diyar tawa?”

“Fatima sunan ta, Iman.”

” Masha ALLAH, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

” Amin.”

” Inyeee, lallai babu kunya Babana? Hadda saurin amsawa ko?”

Dariya ya saka sosai,yayi saurin kashe wayar jin Ammin zata yi masa dan biki.

   

Rik’e wayar ya cigaba da yi a hannu yana juyata,maimakon ya kirata sai wata dabara ta fado masa, take yaji wani dadi ya kamashi ganin ya samu hanyar da zai hana Maman sanin komai har sai lokaci ya kure mata. 

   Kwanciya yayi ya ja blanket har saman kansa, sannan ya kirata yana jin ringing din na tafiya daidai bugun zuciyar sa.

***Da safe ya so ya makara bayan ya koma bacci da asubah, kiran Musaddik ya tuna masa abinda suka shirya, a gaggauce ya tashi ya shirya, ya kimtsa kansa cikin shigar Khakin sa, ya fito a sojan sa, kayan sun yi masifar karbar sa, yanayi da tsarin zubin halittar sa sunyi daidai da kayan, shi kansa yana jin sa ontop a duk lokacin da ya samu kansa cikin irin shigar kayan. 

   A hannu ya rik’e wular ya fito suna ganin shi suka taso da sauri, duk suka k’ame su biyun kafin daya ya bud’e masa motar daya kuma ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan.

   A chan permanent site din sukayi zasu hadu da Musaddik, yana isa yaga motar sa a waje, be shiga ba ya kirashi a waya ya fito ya same shi. Tare suka fito da Ja’afar, Musaddik ya zura kansa cikin motar yana kallon sa.

“Ya riga yazo, yana reception yana jiran MD ya hada shi da oga at the top”

“Ga kuma Oga kwata-kwata anan ba.” Ya kalli Ja’afar suka kwashe da dariya

” Me ka shirya masa Oga?

” Ni na isa Captain? Ai ban isa ba Wallahi. Duk abinda ka shirya min dai, ni ai bani da say.”

” Ya akayi be gane ka Musaddik bane wai?”

” Ba zai gane ba ai, I’m not in charge of staff din wajen, wannan aikin admin human resources ne, plus kaga chan sabon branch ne nan kuma main site.”

” Haka ne kuma, yanzu zan jira anan.”

” Yes Sir!” Ya Sara masa suka kwashe da dariya

Khalil na zaune cikin zulumi yana fatan haduwar da zasuyi da shugaban wajen ya zama alkhairi, yana so ya dawo da aikinsa as soon as possible yadda zaifi jin dadin kwace Iman da karfin ikon sa, da yan kudaden sa a aljihu. Fitowar MD ya saka shi tashi da sauri

” Yawwa Ibrahim, yazo yana parking lot, sai kaje ka same shi, best of luck.”

” Nagode sir, Allah ya kara girma.”

” Amin.” 

Saurin fita yayi, ya tarar da motoci biyu a wajen, duk da bakin glass, tunanin wacce a ciki ya bi numbers din motar da kallo. _Royalty_ aka rubuta a jikin plate din babbar da tafi kyau da sheki, wajen ya nufa kirjin sa na dukan tara tara, kafin ya karasa yaga murfin bayan motar ya bud’e, anyi masa fitala. Kofar ya nufa ya zura jikin sa bakin sa dauke da sallama, sai da ya zauna ya daidaita a ciki, kofar ta rufe ruf ya shaki kamshin motar me dadin gaske, ya juyo sukayi ido hudu da wanda ko a mafarki be taba hasashe ko tunanin gani ba.

“Hello Ibrahim.”

Moh yace yana sakar masa wani irin murmushi me dauke da ma’anoni masu yawan gaske 

“Me… Me ban gane ba?” Ya hau k’inkina ya ma kasa daidaita maganar sa.

“Sunana Muhammad Ahmad Santuraki, Also known as Captain Moh, shugaban wajen nan gaba daya, nice to meet you.”

” Nooo! Impossible! This most be a joke, Kai din? Kai din? Kai… Kai Kai din?”

” Calm down and take a deep breath, karka hargitsa kanka dan akwai sauran surprises, na farko karka taba wulakanta mutum baka san shi din waye ba.”

” Innalillah wa inna ilaihi rajiun.”

Ya shiga maimaitawa ba kakkautawa, gaban motar ya kalla yaga sojoji ne su biyu majiya karfin gaske, kowannen su fuskar sa murtuke take babu alamun dariya, jiran umarni kawai suke kamar mayunwatan zakuna, hadiye wani mugun yawo yayi yana jin sanda Muhammad din ya bada umarnin tada motar ,be iya bud’e baki ya hanashi ba, yana jin sanda motar ta soma tafiya a hankali har ta daidaita akan babban titi, kafin me tuka motar ya kara taka motar da gudun gaske

“Shikenan na gama yawo.” Ya furta a zuciyar sa be san maganar ta fito fili ba.

Murmushi Muhammad yayi ya taune gefen lips dinsa yana ayyana kalar rashin m din da zai masa.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button