Uncategorized

WAYAFI SONTA 5


 
p5

 …Gaba d’aya mutane suncika mak’il agurin da abun yafaru…arude akayi asibiti dasu Dan tabbatar da sunada Rai ko kuwa,yyinda suke mamakin meyasa Wanda yyi bankar yagudu?”

Kasancewar  bbu nisa dg Gurin zuwa gdnsu zainab….hakan yasa ,gidajen 2 suka Sami labarin abinda ke faruwa”gaba d’aya mama d Inna Basu ahaiyacinsu…..cike da tashin hankali suka d’unguma cikin motar baffa sule, zuwa asibitin da aka sanar musu ankai Umar da zainab…. yyinda goggo haule tayi zamanta gd… emergency aka nufa dasu su duka”yyinda wadanda suka kawosu suka tsaya jiran

tsammani! Saiga su baba ,Abba,baffa sule ,mama,Inna sunnufo Gurin cikin tashin hankali…. adedenan likitoci 2 suka fito suna share gumi, fuskarsu kad’ai zaka kalla kasan bbu lfy” guda yadube su yace Ina iyayensu suke?”abbayace gamu” dr  yace pls kibiyoni office….

Bbu Wanda yazauna acikin baba d Abba da Baffa Sule! Dan su Inna na waje..Dr yyi gyaran murya kafin yace kusan ita k’addara da jarabawar rayuwa bbu Wanda yawuce ajarabesa ko ak’addaresa da Mai kyau ko akasanin haka! Cikin tashin hankali suka ce eh hakane kasanar Mana meke faruwa ne dasu?” Dr Kai duk’e yace KULLU NAFSIN  ZA’I KATUL MAUTE…. ALLAH ya karb’i ran wannan namijin….kuyi hakuri kuyi Masa addua hakan shi yafi” dabai mutuba gsky akwai matsala! Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un su baba suka furta atare!!

abba yace ALLAHU AKBAR! Yah ALLAH ka jik’an Umar kayimasa rahama ,halinsa nagari yabisa….Yana fad’a kwallar daya rik’e tana zuba….baba kansa aduke yake yyi shiru shida Baffa Sule…can baba yakalli Dr Ido jawur yace ita zainab wane Hali take?”

Cike da tausayinsu Dr yace gsky itama tana cikin had’ari sbd kwakwalwarta t juya sosai zuciyar ta ta buga sbd abin yafirgitata Ina zaton agabanta akayi,tayi doguwar suma sai anjima zata farfad’o…saidai da wuya ta farfad’o tana mgn gsky….cikin tashin hankali abba yace banganeba likita?”

   Dr yace kuyi hakuri! gsky irin k’arar datayi ta wuce tunani har abin yashafi mak’ogwaronta dole amata aiki “saidai damuwar gudace “gsky kudin aikin sai sunkai kusan miliyan 2 da rabi sbd ak’asar waje za’a matashi..k’asar waye??” Suka maimaita atare…Dr yace eh gsky insha ALLAH da ammata zata Sami lfy….Amma dukda haka zata iya farkawa kuji tayi mgn abun ALLAH Amma Ni abinda muka gani bayan mun binciki lafiyarta kenan…Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un kawai suke maimaita wa Dan sunsan basuda wannan kud’in aikin ko baffa sule dayafisu wadata “agdn uban gdnsa  yake a kabasu part guda sbd gdn nada girma…. sannan Kuma motar dayazo da ita” batashi bace…Abba yace mungode Dr “abamu gawar Umar muje amasa suttura”ita Kuma zainab abarta ta farfad’o muga yanayin jikin nata”Dr yace to shikenan muje…nan suka fito,suka Sami su Inna d mama duk atsatstsaye” nan abb yajasu agefe cikin fahimta yasanar dasu abinda ake ciki’,

amma be Fadi ,suncezainab bazata iya mgn….

 

 

Da k’arfe 6 na marece akayi zana’idar Umar”Wanda yasami shaida sosai aunguwarsu  da abokansa na skuul….Inna da mama sunsha kuka ,gefe guda Kuma suna tausayin zainab akan babban rashin datayi….bayan sallar magarib aka cigaba da karban gaisuwa yyinda , saratu (k’awar zainab) da anty uwani k’anwar mama  suke asibitin gun zainab da har sannan bata farfad’o ba andai Mata allurai ansaka Mata drip”…..gefe guda Kuma goggo haule har cikin zuciyar ta a taji dad’in mutuwar d Umar yyi kodan kada ya auri zainab yakula da ita…tana nan zaune ana karban gaisuwa da ita….

 

 Gab da sallar asuba  zainab ta bud’e Ido”ta kalli d’akin “ta kalli su saratu da anty uwani dake gyangyadi….atake abubuwan dasuka faru suka dawo a brain d’inta” azatonta Kobe mutuba…. Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata…k’ok’arin kuka take Mai shashsheka Amma saitaji hakan yagagara! saita bud’a Baki da nufin yin salati ,sai taji kamr anrufe bakin ,yyinda bakin ke motsi ” cikin k’idima take salati had’e da bud’e Ido sosai ko azatonta mafarki take….Amma Ina ,gashi Baki na motsi Amma batajin maganar ta ta fito,Amma kunnenta najin k’arar fankar dake d’akin…motsi tahauyi … adedenan Kuma anty uwani ta farka….da sauri ta nufi zainab tana cewa sannu zainab! Ya jikin,Ina ke Miki ciwo,Kona Kira nurses ko Dr???”” kallonta kawai zainab keyi” tanajin metake cewa Amma ita takasa mgn” yyinda takejin tamkar antokare Mata mak’oshi….hawaye ke sintiri afuskarta,ita bama wannan ba Ina Yaya Umar nata?”

Zainab kinyi shiru ko jikin?” Muryar anty uwani ta katse Mata tunani….anan Kuma saratu ta farka sbd maganar anty uwani….nan taje tanawa zainab sannu ! Nanma zainab batayi mgn sunjiba sungadai bakinta na motsi ,ga Kuma hawaye na zuba afuskarta….nan anty uwani ta je ta Kira Dr…bayan yagama dubata yace kiyi hkri zainab wannan abin daya faru dake jarabawar ki ce “ALLAH ya Baki ikon cinyewa kinji?” Insha ALLAH zamu sallameki zuwa anjima inhar iyayenki sunbada kudin yimiki aiki to zaa tafi dake misra”Amma nasan kinajina saidai Baki iya mgn!kuka sosai zainab keyi ,ita bama tataba Ina Yaya Umar?”

 

Kallon Dr din tayi taga biro gaban aljihun cot di’nshi ta nuna Masa yamiko Mata… yyinda anty uwani da saratu ke kukan tausayin zainab jin tazama Benita”zainab ga tafin hannunta ta rubuta Ina yah Umar Dina?” Yaya jikinsa?”

Zama Dr yyi kan kujerar gaban gadon ” yafara mata wa’azi kafin yasanar Mata…. girgiza Kai take tana kuka had’e da furta Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un! kasancewar Dr din nada ilimin addini sosai ,yyimata nasiha akan tadage tayita ma Umar addua”kuka kawai zainab keyi tana tuna maganganun dayata mata Wai tayafe Masa Kuma ta Masa addua….nanma su saratu da anty uwani suka k’ara Mata k’arfin gwiwa,akan komai zatayi bazai dawoba,abinda zatayi t nuna tsantsar k’aunarta agareshi shine yimasa addua….

 

 

Anty uwani ta Kira abba akan anjima zaa sallamesu, Kuma zainab ta farfad’o….d sauri Abba yace tana mgn?anty uwani tace ah ah… had’e da sanar Masa anyiwa zainab nasiha akan ta rage damuwa….kafin suyi sallama….duk abinda suke bukata a asibitin da abinda aka kashe,mlm ne yabiya ( kakan zainab) kafin abasu sallama Gurin k’arfe 2 na Rana,suka hau adaidai ta….tun farkon shiga layin aka ajiyesu…. zainab gabanta nata faduwa duk yadda tazo daurewa takasa ,hawaye kezubo Mata,idanunta harsun kumbura” anty uwani na rik’e d hannun ta ” suka nufi k’ofar gdn su zainab” da akayi rumfuna mak’il d jama’a agurin”d’agowa zainab tayi tagasu baba gefe,gasu Hamza d Ido,abokan Yaya Umar na unguwar duk sunyi jigum jigum alamar dukda ankwana dayin mutuwar suanjinta har yanzun…cikin gd suka wuce,anty uwani ta nufi d’akin mama da zainab duk dangi da Yan uwa tausayinta sukeji,abakin k’ofar d’akin suka hadu da anty mariya(matar baffa sule) zainab ta fad’a jikinta tasaki kuka dukda bbu sauti” cike da tausayinta anty mariya tayi bed room din mama da ita tana Bata Baki sbd suna shiri sosai da zainab…inhar sunzo garin kaduna to suna tare da ira..sai rarrashinta akeyi ,wasu na Mata gaisuwa…..

 

Bayan sati d’aya da rasuwar yy Umar “zainab dukta rame batason cin abinci ga Bata mgn ,Dan yanzun harta fara koyon maganar bebaye dukda ita keyiwa mutum nuni da body language , yyinda suk wanda zai Mata mgn toyimata take sbd ansan tanaji… yyinda aka zauna akayi meeting da yan’uwa akan laluran zainab kowa ybada abinda yasawaka ,baba duk kadarorinsa yasiyar Amma abin sai hakuri”sai Dr yabasu shawara akan afara kaita asibitin zariya d Kano ko andace…shine aka tsaida maganar sati na sama za’a kaita…

 

 

Zaune zainab take kan kujera Yar tsigunne da wayar yah Umar ahanunta ,spack 2,tana kallon wayar tana tunawa dashi ,hawaye nazubar Mata, goggo haule dake tsintar wake,ta kafeta da Ido tana cewa uhumm duk Wanda yamutu yafamutu kenan y’ar nan baya dawowa,kinbi kintakure Rai haka…. tafad’a tana tabe baki…. adedenan wani yaro yyi sallama had’e da cewa Wai ance zainab tazo inji Hamza(abokin Umar)

Zaro Ido goggo haule ta yi had’e da cewa ohni Naga abinda ya isheni Wai yarinyar data nakasa ake aikowa tazo tad’i?” Wani kallo zainab ta d’ago tanawa goggo haule….uhum… ALLAH sarki nagodewa ALLAH daya jarabi y’ata ,dansai Mai Imani ake jarabta,wasu sbd duhun Kai da jahilci Basu tunanin kosu Basu wuce ALLAH yyimusu jarabawar datafi tamuba”insha ALLAH sai zainab ta Zama abin kwatance da koyi Kuma sai mutum yazauna a inwarta,bama yiwa kowa mugun nufi ko hassada Amma duk Wanda yyimana sai yaga abinsa…. mama tafad’a tana yiwa goggo haule wani mugun kallo,kafin ta dubi zainab tace tashi kije , ALLAH yasan dake….

 

Share

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button