GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Yes,Inayah.

A marairaice da alamar kuka tace”

Abbi Dan Allah zan bisu inason dubo Heart Nima,
Abbi Dan Allah kada ka hanani….

Bakida lfy Babu Inda Zaki kina wannan kukan
Kisha magani ki kwanta.

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa Yana  maida hankalinsa kan maganar dasukeyi.

Hawaye tafara tana kallon wayar
Su umma na ganin haka suka fice suna cemata saisun dawo.

Zaunawa tayi bakin gadon dakinta Tana cigaba da tsiyayar hawaye sbd tana tsananin buqatan son ganin Heart Dan taga yanayinda yake ciki.

Wurgi tayi da wayarta kan gado tana cusa fuskarta cikin tafukan hannuwanta zuciyarta na radadi.

Hannu takeson dorawa akai ta ringa zumduma ihu da birgima ko zataji sassaucin tsananin qunci da damuwar dake ranta.

Tayaya Zata iya cire soyayyar heart daga ranta bayan yayiwa zuciyarta kyakkyawar Shiga?
Tayaya zasu iya rabuwa da juna sbd kalmar uwa daya uba daya da ake dangantasu da ita?

Batada uban daya wuce abbi Kuma batajin Zata daina daukansa ahakan kokuma daina kallonsa ahakan.

Abbinta fa ake maimaita Mata kalmar mini agurinta.

Kasa riqe kukan tayi ta kwanta agurin tafara rero kuka tana sake Jin zuciyarta kaman zata kama da wuta.

***Su umma yaganah kuwa koda suka Isa asibitin da Dr Abdul yake hankalin Yan uwansa da mahaifiyarsa atashe yake sosai fiyeda tunani Dan kuwa Dr Abdul dai jiki ya rikice.

A jiyan da aka kawosa asibiti daqyar aka samu ya farfado ya kalli mahaifiyarsa da hankalinta ya rarrabu cikin tashin hankali masu girma sbd labarin auren MAJEED da INAYAH ya gigitata sosai,
Zancen ya daketa har Batasan lokacinda itama ta zube qasaba jininta na Neman hawa.

Tabbas AA MAJEED ya nuna Mata shi namijin duniya ne,
Ya Sha gabanta ta hanyar aure Inayah sbd baida niyar bata ‘yarta,
Tabbas Babu shari’a yanzu Kam da Zata karbar Mata Inayah daga hannunsa Amma Kuma idan har Inayah Bata son wannan auren Koda abinda ta mallaka zai qare duniya kowa ya juya Mata baya saita tsaya Sharia ta raba auren anbata ‘yarta.

Su Haj balaraba dasu Alhaji buhari saidai su Alhaji kabiru sukai musu bayanin cikin daya bayyana jikin Hadiza bayan shekaru Wanda yayi sanadin dasuka koreta daga gida
Saidai yanda komai yafaru Bayan barinta gidan shine Basu saniba saisunji daga gareta dashi AA MAJEED din Dan yanzu sune kadai zasu qarasa warwarewa kowa wannan qullin da tunanin dasuka shiga.

Haj balaraba kuka ta ringa rerawa tana yiwa salisu addua suna qara godewa Allah da baa daura wannan aureba da basusan iya Ina tashin hankalin zai kaisuba.

Hajiyarsu suka kira suka Dan sanar da ita komai a taqaice to dayake tasan da maganar cikin da haihuwar bayan barin Hadiza gida daga bakin jama’a Amma tayi shiru ta lafe sbd tunanin ko cikin banzane Hadizan tasamo daga Lagos sbd kada a dangantasu da cikin Tai shiru taqi Kuma barin ‘yayanta ko daya yasani dan kada suce zasu karba tunda ba tabbas hakama Hadiza ta sameta takanas da jaririyar Amma shedan yaqi Bari ta amsa.

Tsufa ya kamata sosai yanzu Amma itama haka ta ringa kukan danasani da farin cikin da aka samu Ayshatouh take zancen yafara fita a dangi saidai halinda Abdul ke ciki yafi daga hankalinsu akan murnar bayyanar wadda basuma San da itaba a zuriar.

Dr Abdul mummunan shock din daya shiga ya daki zuciyarsa zuwa qwaqwalwarsa sosai Dan haka ya jima Bai farfado ba Kuma ya a farfadowa ummansa yafara zubawa indanuwansa dasukai mummunan ja yana kallonta cikin karaya da mutuwar dukkanin jiki yace”

Umma since Inayah ‘yarki ce itama kece kika haife shiyasa bazan auretaba Abbi ya aureta
Ni nakasa gane komai
So kawai naji daga bakinki idan kece mahaifiyar Inayah tayaya AA MAJEED zai Zama ubanta?

Umma Dan Allah kicemun ba kece kika haifetaba,
Kicemun bakida alaqar komai da ita sai wadda zamu qulla yanzu ta auratayya,
Umma Dan allah kice bakece uwar Inayah ba bakida alaqan komai da ita…umma bazan iya rayuwa Babu Inayah ba kinsani akanta zan iya rasa hankalina da nutsuwata,

INAYAH ce farin cikina,rayuwata da nutsuwata…..umma kice wani abun Dan Allah Amma ki janye maganar kece mahaifiyar INAYAH.

Kakkarwa jikinsa keyi idanuwansa na sake fitowa da tashin hankali.

Saikowa yayi gadon Yana Neman faduwa sbd jiri sukai saurin riqesa umman cikin kuka ta riqosa tana kallon yanda yake kokarin haukace musu tace”

Abdul hakuri zakayi da wannan kaddarar ka runguma sbd bazan iya goge alaqar jinin dake tsakaninka da Ayshatouh Inayah ba,

Kai Dan uwantane na Jini,
Nice na haifeta kaman yanda na haifeka,
Uwar daya ubanku daya Babu Mai iya goge wannan sbd rubutacciyar kaddara ce,

Abdulsamad ma dauki danganar rasa Inayah sbd har abada Babu aure tsakaninku
bazaka taba aurentaba Koda ku biyu zaku rage a duniya.

Dan Allah Abdul ka karbi wannan kaddarar da hannu babbiyu sbd zuciyata bazata iya daukan wannan tashin hankalin dakake saka kanka acikiba Dan Allah Abdul.

MAMUH

KUYI HAKURI AMIN UZURI NASAN CHAPTER DIN IS TOO SHORT.????

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810734
Arewabooks@Mamuhgee
Umma Hadiza hankalinta yagama rabuwa daban daban,
Tana buqatan fuskantar MAJEED akan abinda yayi na auren Inayah badan komaiba sai Dan nuna Mata iko akan Ayshatouh..

Ta Bangare Daya tasan Inayah ma na can cikin matsanancin halin itama,

Babbar damuwar Kuma ganin Abdulsamad na Neman zauce musu sbd yaqi sauraren kowa bayan zantukan tashin hankali da qin yarda da uwarsa daya da Inayah kaman yanda itama Inayah batama yarda da tanada wata uwarba Dan ko acikin tarin damuwarta umma Hadizan Bata shigob ita tashin hankalinta Abbi daya zamana ba mahaifinta ba ko auren daurawa kawai akayi batajinsa ajikinta kwata kwata.

Zuwansu umma yaganah yasa hankalinsu Haj balaraba tashi sbd mummunan halinda Abdul yakuma shiga Dan kuka ya ringa yiwa su umman da Anty Hafsat Yana maimaita sunan Inayah cikin karyewar zuciya.

Umma yaganah dayake tanada saurin kuka take itama tafara hawayen tausayin Abdul tana cewa”

Abdulsamad sai hakuri
Jarabawar ubangiji ce duk zaa cinye idan anyi hakuri da tawakkali
Inayah tariga ta Zama ta waninka dole dangana zaa dauka abarwa Allah…

Kalaman umma yaganah suka qara Karya zuciyarsa yaci gaba da zubda hawaye Yana sunkuyar dakai zuciyarsa na Masa wani irin ciwo.

Anty Hafsat ma jikinta mugun sanyi yayi da tausayin Abdulsamad Mai tsanani Dan kuwa Basu dauka abin yayi tsanani hakanba.,

Abdulsamad din dasuka sani Dan gayu da kwalisa shine ya garare cikin kwana daya sbd masifar ciwon rashin Inayah.

Neesah kuwa itama jitayi tausayinsa da Inayah harma Dana Abbi yasa hawaye ciko idonta sbd kowannensu yana cikin matsanancin halin da Babu mafita sai dauka da dungumar abinda ya samesa.

Irin naci da daga hankalinda Abdulsamad yayi nason zuwa ganin Inayah yasa umma yaganah miqewa su tafi sbd ko hauka bazata sakata tafiyada abdul dinba ko basa damar zuwa ganin Inayah ayanzu sbd bayan haqqin mariqi da MAJEED yake dashi akan Inayah yanzu shine Mai gabaki dayanta Dan haka bazatai wannan wuce gurinba ko gangancin zuwa dashi Dan haka suka miqe suka fito jiki a sanyaye Koda,
Inayah ma Babu Wanda yayi musu maganarta sbd kowannensu baimasan me zaiceba akanta Dan haka sukai shiru kafin suga sun fara samun daidaituwar Abdul tukuna ayi zaman wannan maganar dake buqatan iyaye da manya aciki sbd tsanar da MAJEED yayiwa Hadiza Saida manya a zancen zai yiyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button