GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Tunda umma Hadiza tashigo take rarraba idon Neman ganin Inayah cikin gidan.

Inayah tunda taji su umma Hadiza sunzo gidan taqi fitowa ko Alhaji babbah tanason fitowa ta gaidar Amma batajin Zata iya barin umma Hadiza ta ganta matuqar bada izinin Abbinta ba sbd shine kawai yakeda iko akanta na yanda zaiyi da alaqarta da Hadizan.

Umma yaganah ma Gaisawa kawai tayi dasu Alhaji babban ta miqe Zata komawarta ciki sbd yanzu da mahaifiyar MAJEED take Nan ba buqatan zamanta agurin dama can Dan tana matsayin uwa ne.

Cikin nutsuwa Alhaji babbah yace”

Yaganah dawo ki zauna ai komai dake zaayi kece MAJEED yanzu tunda Baya Nan.

Dan murmushin yaqe tayi tareda dawowa ta zauna tana dan kallon Inda hajiyar MAJEED take zaune fuskarta ba walwala ko kadan.

Kusan kowa ya zauna ya nutsu,

Alhaji babbah ne da CM a gefe daya
Sai umma Hadiza da Haj balaraba a dayan gefen
Alhaji buhari dasu malam Umar ma dasuka matsu dason ganin Inayah duk suna zaune sai Dr Abdul daya rakube cikin yanayi na tausayi da ciwon dake damunsa.

Hajiyar MAJEED ma da Anty juwairiyyah da umma yaganah sai Anty Hafsat gefensu daya.

Cikin nutsuwa Alhaji babbah yafara magana da cewa”

To dukkaninmu dai kusan bamusan junaba anan MAJEED da INAYAH ne ya hadamu anan,

MAJEED yayi tafiya wadda Nima ban hanasa duk da nasan zaayi wannan zaman sbd Yana cikin yamutsin Kai Dana zuciya
Yaron Yana buqatan nutsuwa sbd abubuwan duk sun taru sun ratayane akansa Dan haka gwara abarsa ya samu nutsuwa kada pressure da damuwa din mahaifiyarsa gatanan data matarsa data hajiya Hadiza dama Tamu duka ta sanyasa cikin wani hali.

Hajiya Asma’u wannan itace hajiya Hadiza da ‘yan uwanta gasunan mahaifiyar Inayah ‘yar MAJEED da kuka sani a baya matarsa Kuma a yanzu.

Hajiya Hadiza wannan Kuma itace mahaifiyar ABDULMAJEED data haifesa.

Ayanzu wannan taron dai na fahimatar junane dakuma warware duk wata damuwa da qaddarar data Riga ta wuce.

Inayah dai ba ‘yar MAJEED bace hajiya kaman yanda kike tunani
Amma dai yanda tazo hannunsa ne Babu Wanda yasani sai Allah saikuma MAJEED din da Hadiza gatanan zaune.

Hadiza ki warwarewa hajiya komai sbd kawarda zargi da Kuma damuwar qaddarorin dasuka gifta abaya data rabu da ‘danta akan hakan.

Dagowa Hadiza tayi jiki a sanyaye ta kalli hajiyar cikeda kunyar Zama mugun sanadin daya kawo abubuwa da dama.

Kan su Yaya Umar da Yaya kabiru ta maida kallonta sbd kusan suma sune sanadin komai.

Inayah data tsaya bakin kofar dakin umma yaganah sbd tanason taji yanda tazo hannun Abbinta da kunnenta batareda wani ya fada Mata ya rage Mata wani abun….

SHEKARUN BAYA….

MAMUH

LOVE/ROMANCE/LOADING

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[11/3, 10:19 AM] It’s Queen Meenali????: 38
Arewabooks@Mamuhgee
Tana fitowa gidansu rungume da jaririyar tata dake lafe kirjinta tana bacci taji qafafuwanta na Neman sanyi Amma sukasa riqeta sbd wani irin nauyi da kirjinta kemata tareda radadi a maqoshi..

Sake rungume jaririyarta tayi da kyau ahankali kafin ta dago ta kalli hanya da idanuwanta dasuka qafe sukai jajir sbd kuka tuni ya qafe daga Idanuwanta.

Ahankali ta daga qafafunta tafara tafiya tareda kauke kanta qasa sbd Yan anguwa wainda suka lura da ita suke kallonta da ma’anoni da maganganun zunde da zagi.

Bakowane yasan tadwo daga Lagos dinba da ciki saidai sukaji haihuwar tareda rasuwar mahaifiyarta shiyasa kusan duk Wanda ya bude Baki tir da Allah wadai yake furtawa gareta da jaririyar ‘yarta.

Ahankali take takawar sbd rashin qarfin jiki dakuma qarin data samu agun haihuwa gakuma rashin abinci ko abinsha Dan haka batada wani babban kuzarin takawa da sauri harta fice daga layin batareda ta waiwayo ba Dan tanajin idanuwan mutane akanta Wanda tasan mummunan fatar rashin ganin me kyau suke Mata a duniyar da Zata shiga.

Kasa hawa titi tayi sbd Batasan Inda ta dosaba,
Batasan gurin waye Zata ba a wannan mummunan halin datake ciki,

Batada uwa Bata uba batada miji waye gareta Mai tsaya mata?

Samun kanta tayi da zaunawa bakin wata bishiya sbd kwakwalwarta datake neman Dena aiki.

Jaririyarta tafara kuka Wanda na tsananin zafin ranar dake dukansu ne

Yaye zanin datake dunqule aciki tayi ta Dan kalli fuskarta taga yanda fuskar tayi jajir take sbd azabar Rana
Sai alokacin taji zuciyarta data daskare tana narkewa da tausayin kanta dana jaririyar Dan haka batada zabi daya wuce ta tunkari gidansu salisu ko ummansa Zata karbesu tunda jikartace su taimaketa ta zauna gurinsu ta Rena Ayshatouh idan ko shekara tayi saita barta takoma gidansu idanma sbd itane su Yaya Umar suka koreta daga gida.

‘yar qaramar jakar kayanta ta bude tafara duba kudin datake dasu.,

Dari uku da ashirin tagani take jikinta yakuma mutuwa saidai halinda zuciyarta take ciki Batajin akwai abinda zai fisa daci.,

Miqewa tayi ta qarasa bakin titi Anata kallonta sbd Jin yanda jaririya ke kuka sosai a jikinta Dan haka Bata tsaya juran napep ba ta tsayarda Mai mashin ta hau suka tafi.

Gabanta tsananta faduwa da shiga qunci yakeyi sbd hajiyar salisu ma batasan yaya zata karbesuba…

Mai mashin na ajiyeta kofar gidan ta Ciro dari da hamsin ta miqa Masa ta juya ta shige qaramar kofar gidan tana sake qamqame yarta jikinta.

Tun kafin ta qaraso ciki Yara suka fara Isa gurin hajiyar suka sanar Mata Hadiza tazo.

Dan shiru hajiyar tayi kafin ta kalli yaran ta korasu waje ta dawo da hankalinta kansu balaraba dake gidan ta sallamesu suka wuce inda zasu ta kofar baya batareda sun tsaya Gaisawa da Hadizan ba Dan dama a sama sama suke da ita tun salisu nada Rai bare yanzu da basuda alaqa da ita.

Da wata irin dasasshiyar sallama ta shigo hankali sbd muryarta ko fita batayi.

Da mamaki hajiya ta kalleta idanuwanta na sauka kan jaririyar dake hannun Hadizan.

Idanuwan Hadizan zuwa fuskarta ta kalla dakyau take tagane jegone tareda Hadizan Dan haka ta tattaro hankalinta da mamaki a bayyane kan fuskarta tace”

Hadiza¿
Kece nake gani?
Lafiya da Rana tsaka haka?
Ba zaman karban gaisuwar Aishatu akeba.

Kasa magana Hadiza tayi sbd jirin dake dibanta Dan haka a sukwane ta qaraso ta durqusa gaban hajiyar tareda sunkuyar dakai idanuwanta na sake rinewa.

Sake Shiga firgici hajiya tayi tana qin nuna taga jariri atareda hadizanba tasake cewa”

Hadiza nace lfy kuwa?
Kiyi mgana kikai shiru kina bani tsoro…

Dagowa Hadizan tayi tana kallon hajiyar sbd tasan bazatace bataga abinda ke hannuntaba
Idanma Bata ganiba bazatace batajin kukan da Ayshatouh ke tsalawaba.

Sunkuyar dakai tayi tareda bude jaririyar dakyau agaban hajiyar muryarta na a disashe da tsananin damuwa da qunci Mai daci tace”

Hajiya haihuwa nayi su Yaya Umar sukace nabar gida,
Bansan Inda zaniba sbd ko Abokai banda shine nataho Nan….

Dauke wuta hajiyar tayi daga zaune tana kallon Hadizan Baki sake ko fuskar jaririyar taqi kalla.

Qofa tafara kalla ta leqa tsakar gida taga ba kowa tadawo da sauri ta kalli Hadizan cikin tsananin mamaki, firgici da takaici Kai tsaye tace”

Me Zan Miki anan hadiza?
Haihuwafa kikace kinyi?
Haihuwa ba aure fa?
Wace qaddarace wannan takaiki ga wannan mummunan sakamakon? Shine Kuma Zaki zomun Nan?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button