GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Ko kunyar ‘danki dake gidan Nan bakijiba kika kwaso jiki da jaririn shege kizomun anan?

To Kinga Hadiza tun kafin Raina ya baci Kuma tum kafin wani yaji tashi ki fice,

Mune mukafi kowa hauka a duniya ne dazamu Baki gurin zaman renon barna……

Rawa hannuwan Hadiza suka fara hankalinta yasake mummunan tashi tana kallon hajiya da idanuwanta jajir tace”

Dan Allah hajiya ki yarda Dani ki fahimceni
Kima kaini a dubani idan ana dubawa wallahi tallahi banyi kowace irin barnaba nasamu cikin Nan,
Wallahi cikin salisu ne……

Wata irin mummunan zabura hajiyar tayi tana kallon Hadiza a gigice sbd mamaki da baqin cikin zancenta Dan ta Gama raina Mata hankali kokuwa dai mahaukaciya ta dauketa?
Amma dai Bari ta tabbatar…kallonta tayi a Rikice tace wane salisun Hadiza?

Muryarta Bata fita sosai sbd shaqewar maqoshi tace”

Salisu baban Abdul….

Kasa magana hajiyar tayi ta rufe idonta daya fara sauyawa sbd tsananin bacin Rai da masifar Rainin da Hadiza tazo dashi Dan haka Bata buqatan ma Jin komai ta nuna Mata hanya tace”

Fice Hadiza kibar gabana Dan Allah.

Dagowa Hadiza tayi ta kalli hajiyar sai alokacin hawaye suka ciko jajayen idanuwanta suka fara gangarowa.

Magana takeson yi Amma zuciyarta tayi nauyi bazata iyaba sai wani irin quntataccen kuka Mai ciwo daya zuwar Mata.

Ganin ba tashi zataiba kada wani yashigo yagantama kokuma yaji haukar datake fada yasa hajiyar Kama hannayenta ta miqar tsaye tareda janta takaita har waje ta Kuma gargadeta akan sake zuwa da wata jaririyar gidan da sunan salisu abakinta.

Kuka sosai Hadiza keyi tanajin wani irin azababben ciwo a zuciyarta,
Jin takeyi kaman zuciyarta zata mutu,

Ganin mutanen dake wucewa sunfara Mata kallon mahaukaciya yasata Jan jiki tabar kofar gidan.

Tafiya kawai takeyi sbd Batasan Inda zataba,

Jin jaririyar tayi baccin wuya itama yasata tsayawa ta goyata taci gaba da tafiya.

Tafiya Mai nisa tayi wadda batamasan tayiba har Saida yamma tayi sosai ta nema bakin wani gidan abinci ta zauna tareda sauke jaririyarta ta saka cikin hijabinta tafara Bata nono.

Kasa Shan nono ‘yar tayi sbd tuni ciwon zazzabin wahala ya rufeta sbd ba qaramar Rana sukashaba.

Fara jijjigata tayi tana sake cusa Mata nonon Amma Bata amsaba Dan haka ta maidata ta goya.

Shagon dake gefen gidan abincin ta qarasa ta siyo ruwan roba na sauran canjinta dasuka rage Takoma Inda ta baro ta zauna tasake saukoda ‘yar ta bude ruwan ta ringa zubawa a murfin robar tana Bata.

Ruwan ma batasha saidai wasu sun shiga cikinta kadan…

Kuka jaririyar keyi sosai Wanda ya qarasa gigita Hadiza..
Batasan ya zataiba sbd kanta zazzabi da ciwone Mai qarfi a jikinta.

Gabanta radadi yake Mata sbd qarin haihuwa da rashin ruwan zafin gasa gurin ga doguwar tafiya cikin azabar Rana Dan haka itama take a gigice.

Kukan ‘yar yasa Dole tabar gurin ganin hankalin jama’a yafara yawa kanta.

Cikin wasu mabarata dake gaba kadan bakin wasu super market taje ta zauna tana sake fama da Yar dake kuka har lokacin.

Nanma bata tsiraba sbd anfara Mata kallon zargi da ‘yar
Silalewa tayi tabar gurin kafin ayi Mata dukan Satan ‘ya takama hanya taci gaba da tafiya gashi duhun dare yafara Dan har anfito sallar magriba.

Tafiya Mai Dan tsayi takuma Yi taji bazata iyaba sbd radadi da azabar da tsakiyar cinyiyinta ke Mata,

Azabar datakeji tafi Mata naqudar haihuwar datayi sbd gurin ya goge sosai sbd tafiya Dan haka tasamu wasu shaguna da Yan gudun hijira suke ta zauna daga can gefe itama.

Ruwan robar data siyawa yarta itama taciro daqyar ta iya karban kadan ta shimfida zaninta agurin ta kwanta tana fidda numfashi daqyar jikinta na rawar sanyi.

Babu Wanda ya lura da ita sbd suma kowa ta kansa yakeyi Bata wani ba dan kowa agurin abin tausayine.

Yarta na dungule cikin jikinta itama tayi bacci.

Hadiza Batasan inda kanta yakeba sbd kusan suma tayi saida sanyin asuba da kukan yarta ya dawo da ita
Ta bude idanuwanta daqyar tana Neman tashi Amma takasa.

Daga kwancen ta sake rungume jaririyarta ta Ciro nono tasaka Mata a Baki.

Ana Gama sallar asuba duka mabarata da Yan gudun hijira dake gurin suka fara watsewa sbd baa barin Zama gurin da daddare kawai suke zuwa su kwanta da gari ya waye kowa yatafi gurin bara.

Daqyar ta iya daddafawa ta tashi tabar gurin
Tafiya kadan tayi tasamu guri ta zauna sbd bazata iyaba.

Anan gurin ta Rana ta fito ta sameta
Mutanen dake wucewa suka fara Bata sadaka sbd sun dauka Bata takeyi

Dayake tana buqatan taimakon ana bata haka ta ringa karba har Allah yasa ta hada 400 ta tashi daqyar ta siya ruwan zafi gurin me shayi ta Sha na hamsin ta siya wasu na hamsin din ta wankewa ‘yarta jiki ta gogeta ta maida Mata kayanta da daudarsu da komai.

Har yamma tana garari a hanya Dan haka tasake komawa gidansu salisu
Hajiyarsa Bata tausayawa mataba tayi Mata korar wulaqanci harda munanan kalamai akan ‘yarta Dan haka ta sake komawa Inda ta kwana jiya anan ta Kuma kwanciya.

Washe gari ma haka ta sake zuwa gidansu salisu a karon karshe hajiyarsa tayi Mata mummunan gargadin sake zuwa tareda tabbatar Mata da har abada bazasu karbi shegiyar data haifaba amatsayin ‘yar salisu.

Ranar tayi kukan data jima batasamu tayiba sbd maganganun hajiyar dakuma ciwo Mai tsanani daya sakota gaba da ‘yarta.

A ranar ko bacci Bata samu tayiba a zaune ta kwana tana kallon yarta wadda da alama sanyi ne yayi mummunan shigarta tana numfashi daqyar.

Gabaki daya duniyar tayi mata zafi,
Qunci da nauyi takeji a zuciyarta Mai tsananin gaske..

Washe gari da safe data samu qarfin jikinta ta tallaba takai jaririyarta wani qaramin asibiti datagani a hanya.

Karon farko ana dubata akace Mata ‘yar batada lfy sosai,
Zuciyarta Bata bugawa yanda yakamata hakama sanyi na Neman shigarta.

Gado aka Bata Amma sbd batada ko kudi suka korota ta fito tana bin hanya Ahankali idanuwanta na tsiyayar hawaye.

Yau Bata samu gurin kwanciyaba sbd yan hijirar dasuka qara yawa Dan haka Nesa dasu sosai tasamu ta kwanta.

Hankalinta a tashe yake da Inda ta kwanta din sbd itace a nesa qarshe sosai
Wasu irin sauro da cinnaku suka ringa cizonta tanaji Amma Bata ko iya motsawa sbd zuciyarta data Gama mutuwa.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/3, 7:34 PM] +234 808 746 2576: 39
Arewabooks@Mamuhgee
Koda garin ya waye daga ita har ‘yarta  gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun bayyana ajikinsu ita hardana cinnaku dasukai Mata kaman Mai wani ciwon take fuskarta ta kumbura.

Tashi tayi ta nufi Inda suke gyara jikinsu ta gyara ta fito ta miqa hanya goye da ‘yar tata.

Kwananta hudu agurin aka rarraba musu kudin sadaka a gurin akan kowa yabar gurin
tana karban nata ta tattara tsumman kayanta ta nufi asibiti takai ‘yarta data fara nisa.

Kwantar dasu akai tareda sakasawa ‘yar oxygen Wanda ya cinye kudin nata batareda ansamu na siyan sauran maganiba.

Daqyar takai safe cikin tashin hankali Mai tsanani da qaqa nikayi sbd jikin ‘yar jaririyarta daya sake gabaki daya.

Rashin Imani da rashin tausayin asibitin haka suka sallameta sbd rashin magani da rashin kudin siyansa ta rungumo ‘yarta ta fito tana hada hanya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button