GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Yau kam komai yasake yimata tsananin da takejin mutuwa take buqata Ido rufe.

Uwarta da ubanta da salisu takeson bi Ido rufe sbd ta huta da qunci da baqin cikin duniyar datake ciki.

Kuka aranar tayisa har idanuwanta basa gani sosai sbd kumbura.

Tahau titi rungume da ‘yarta wadda take tsoron dubawa ko ta mutu ko tanada sauran Rai.

Mutuwa take Kira take Kuma fata sbd Babu Inda takejin sassauci a wannan rayuwar.

Wani azababben ciwon gaba take fama dashi da ciwo ciki Mai tsanani,
Ta bangare daya qwaqwalwarta tafara kasa daukan tashin hankalin da masifar datake ciki Dan haka wunin ranar attempting kashe kanta kawai takeyi Amma tsananin qaunar datakewa yarta Yana hanata idan ta kalleta.

Tamkar mahaukaciya tafara komawa sbd taba qwaqwalwarta da abin yafara Musamman mummunan infection din daya shigeta sosai sbd rashin kulawa da gurinda ta Haihu.

Tun tana iya controlling kanta akan yanayinta dayake son juyar da qwaqwalwarta haryazo tafara tsoraran yanayinda jaririyarta da itama kusan Rai ne kawai ya rage Mata Zata shiga idan wani Abu ya sameta.

wani masallaci takai ‘yar ta ajiye Zata gudu tabarta ko zaa samu Wanda zai tallafeta Amma saita kasa barinta agurin tadauketa tana hawaye tana jujjuyar dakai tabi hanya tana surautai ita kadai.

Batasan ya akaiba sai gata kwatsam takai kanta hanyar Tasha tana tafiya.

Kaduna ne?

Ina zuwa ne?

Kano ne?
Katsina ne?

A kunnuwanta kalmomin ke sauka suna sake yamutsa qwaqwalwarta…

Jikinta rawa yakeyi sosai kanta na sake juyawa sosai.

Ahankali sama sama takejin cikin nutsuwa wani yayi magana a bayanta.

Assalam alaikum,
Malama Zan wuce ko
Zaki Dan matsa.

Waiwayowa tayi da sauri a firgice  tareda kallon Mai maganar.

Saurayine matashi Wanda zatai qani dashi bamai tazaraba sosai.

Sanye yake cikin qananun Kaya Riga ash da wandon jeans black.

Cikin sauri Dan tashar masu mota ya qaraso Yana daka Mata tsawa da cewa”

Dalla matsa ki wuce daga Nan
Kinzo kintare hanya
Idan bara zakiyi ki matsa can.

Yallabai Kace gombe Abuja ne ko?

Kallonsa matashin yayi kafin ya kalli Hadiza data Matsa gefe ta rabe rungume da abinda yake sakaran ‘da ne sbd yanda ta rungume zanin cikeda so da shauqi.

Hannu ya saka aljihunsa ya Ciro Dubu daya ya miqa Mata cikeda kulawa batareda yace komaiba.

Hannu ta miqa a hankali ta karba tareda kafesa da Ido tana zuba godiya Kuma takasa tafiya.

Cikin qaguwa ya kalli masu lodin motar yace”

Saura mutum nawane motar tacika hanyar kunsanfa bawani kyaune da itaba.

Yallabai Saura mutum uku motar tacika.

Muje zan biya kudin sauran gurin.

Angama ranka yallabai.

Hadiza dake rakube tanajin haka sai kawai tasamu kanta da biyo bayansa tafara kokarin Shiga motar sbd Jin zaa biya koba komai gwara tashiga duniyar tunda hakane qaddararta.

Kokarin hanata shiga motar direba yafara yana cewa”

Ke tsaya, tsaya
Ina zaki?
Wane gari Zaki?

Abuja” ta furta Kai tsaye muryarta na ‘dan rawa.

Ina kudinki na mota?

Waiwayowa tayi ta kalli gefenda matashin yake zaune cikin nutsuwa Yana duba wayar hannunsa.

Ganin tana kallonsa ya fahimci batada kudin motar Dan haka yacewa drivern tahau gurin mutum daya cikin kudin mutum biyu daya biya.

Kasa kallonsa tayi bare tasake Masa godia saima sauke kanta datayi qasa tana sake rungume jaririyarta.

Hanya aka dauka aka fara tafiya Mai nisa kowa yayi tsit a motar Yana aikin gabansa masu bacci Kuma nayi.

Ahankali ahankali idanuwan Hadiza suke cikowa da hawaye tanajin wani irin masifaffen ciwon Kai da zabar ciwon ciki.

‘yarta take ji,
Ita take tausayi ba kantaba,
Jin kanta na neman juyewa yasa tafara jin kaman tace a tsaya ta sauka.

Yanayin yanda take sake qanqame babynta yasashi Dan dagowa ya kalleta dakyau yaga tarin tashin hankalin dayake ciki kafin ya maida kallonsa kan babyn cikeda kulawa yace”

Ki Dan sassauta riqon
Kina matse babyn sosai Inaga.

Da sauri kaman qaramar yarinya tayi saurin sassauta riqon tareda bube jaririyar gabaki daya Dan Tasha iska.

Wani irin mamaki da firgici ne ya kamasa ganin babyn wadda alamun rashin lafiya sosai da yin nisa ya bayyana atareda da ita,

Gabaki daya babyn yunwa tagama kamata tako ina.

Dauke kansa yayi daga kallon jaririyar sbd zuciyarsa bazata iya jurewa kallontaba.

Tafiya suka cigaba dayi mai nisa da gudu..
Guri biyu aka tsaya siyan abinci Kuma ya siya Mata yabata sbd lurada akwai yunwa tareda ita.

Duk abinda ya siya Mata ya bata bataciba suna jikinta dunqule sbd bazata iya ciba ita kadai tasan tsananin halin azabar datake ciki.

Daga Nan Basu sake tsayawaba a hanya suka cigaba da zuba gudu a hanya.

Qarfe Tara da mintuna arbain da takwas suka isa birnin tarayya.

Kowa fitowa yayi daga motar yana haramar daukan kayansa ya wuce.

Daga shi sai jakarsa dake rataye a kafadarsa ya fito Yana sake saka Kiran Wanda aka aiko daukansa daga gida.

Ahankali Hadiza ta tako gefensa ta kallesa qafafuwanta na ‘dan yin rawa.

Tsalle zuciyarta keyi ga abinda zuciyar tata ke ingizata ga aikatawa.

Jin takeyi zuciyarta ta kwanta data barmasa ‘yarta ta gudu sbd yanada tausayi da Jin qai Dan kuwa ita batada tabbacin zatakai labari ayanda takejin azaba da radadi cikin jikinta.

Bazataso wani Abu ya sametaba ‘yarta ta gararanta…

Jin mutum kusa dashi yashi juyowa da Dan sauri sbd ya Dan firgita.

Kallonta yakeyi da mamaki sosai batareda yace Mata komaiba.

Ganin kallon dayake Mata yasata kallon ‘yarta cikin kokarin daidaita kanta tace”

Nagode sosai Allah yasaka maka da Alkhairi.

Amin” kawai ya iya furtawa Kai tsaye Yana cigaba da wayarsa.

Yana aje wayar drivern ya tura aljihun jeans dinsa drivern gidansu yace Saura kadan ya iso.

Jakarsa ya juyo zai dauka daga qasa gefensa idanuwansa suka sauka kan zani kan jakar tasa.

Da sauri ya waiwaya Babu kowa gefensa da bayansa.

Sake jujjuyawa yayi Yana Raba idon matar data bar Masa zanin.

Jakar ya riqe zai dauka ya watsar da zanin agurin sai zuciyarsa ta kasa Dan haka yakai hannu kawai zai janye zanin yaji alamun Abu aciki

Batareda ya taba tunanin ganin komaiba bare ‘dan mutum ya bude zanin aikuwa yayi Ido biyu da babyn.

Zaro Ido yayi da sauri tareda mayarda zanin ya rufe babyn zuciyarsa na rawa.

Da sauri tafara waigawa koina Yana zazzare idon Neman Hadiza.

Daukan babyn yayi dan Dole ya rungume Yana sake jujjuyawa Neman Hadiza.

Fara tashi hankalinsa yayi dayaga dagaske yakasa ganin uwar babyn.

Kokarin komawa yakeyi gurin motar dasuka iso sai kawai ya hangota tana sauri zatabar tashar tana zazzare idon kada ya ganta.

Da sauri ya bita
tana ganinsa ta sake sauri ba Shiri ta tare Mai mashin ta haye suka bar gurin da sauri.

Tashin hankali da tsananin mamakine da firgici yasashi Neman wani mashin din ya hau Amma tuni Hadiza da me mashin dinta suka bace Masa.

Me wannan matar tayi ne?
Me take nufi?
Da gangan tana sane ta bar Masa babyn ta gudu fa.

Innalillahi wainna ilaihrrjiun..

Meyasa zatayi haka?

Dama mahaukaciyace Basu luraba?

Meyesa Zata gudu tabar Masa baby ?
Ina zai Kai babyn to?

Yawo ya ringa Yi dame mashin hankaki tashe Amma sun kasa ganin hadiza ko Mai Kama da ita.

Dukkanin qwaqwalwarsa tsayawa tayi cak shima
Ya tsaya rungume da baby ajikinsa Yana Jin jiri na Neman zubar dashi,

Ya zaiyi da wannan babyn?

Bazai iya komawa tashaba sbd baisan wazai bawa babynba,
Baimasan wazai fara tunkaraba a tasha da babyn sbd Babu ruwan kowa babuma Kuma Wanda zai karba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button