INAYAH 31-40

Innalillahi wainna ilayhirrajiun” yafara maimaitawa dukkanin jikinsa na saki.
Mai mashin ya fadawa Inda zai kaishi
Wata qaramar police station yaje da babyn suka qi karba sukace yace babban station kawai.
Wata station din yakuma zuwa sukuma sukaqi karban ‘yar suna zargin kodai yarda Yar kawai yakeson Yi.
Wata sabuwar masifar yakuma Shiga lokacinda yagama yawo da babyn Babu wata mafita ko daya.
Yanayin babyn kawai ya tabbatar masa da babyn sosai tayi nisa batada lafiya Dan haka ya tattara a nufi wani private asibiti yakaita su duba.
Suna karbanta take sukai dakin jarirai da ita.
Fada suka fara yimasa sosai ganin yanayin datake ciki.
Duk abubuwan zasuyi Mata sunyi suka sakata a kwalba sbd ma sai allah Kam idan Zata rayu.
Tashin hankali sabo yakuma Shiga lokacinda suka zayyano Masa cututtukan dasuke cin babyn.
Biyan komai yayi kafin ya samu ya wuce gida yabar babyn anan sbd akwai masu kula da babies a dakinsu.
Koda ya Isa gidansu mahaifiyarsa na ganinsa cikin tashin hankalin rashin daukan wayarsa da rashin ganinsa da driver yayi har kusan qarfe daya da rabi na daren yayi.
ABDULMAJEED..Ina ka shiga daga isowarka?
Lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali idanuwansa na qanqancewa da tashin hankali da damuwa yace”
Hajiya umma kaina kaman zai fashe
Zanshiga nayi sallah tukuna.
Cikeda kulawa tace”
Jeka kayi wanka da sallar ka huta da safe mayi magana.
Juyawa yayi Yana hada hanya ya nufi hanyar dakinsa Yana jin kansa na sake tsananta ciwo.
Zubewa yayi qasa tsakiyar dakin Yana dafe kansa,
Daqyar ya tashi ya qarasa isa ya tube kayansa ya shafa toilet.
Wanka yayi ko zai samu kansa ya Dan sake tareda alwala yafito.
Jallabiya da gajeran wando kawai yasake yayi sallah ya miqe a daddafa ya Isa kan gadonsa ya hau ya kwanta tareda rufe fararen idanuwansa dasuka qanqance sbd tashin hankali da damuwa.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/4, 11:05 AM] +234 813 979 4675: 40
Arewabooks@Mamuhgee
Babban tashin hankalinsa shine a yanayinda babyn Nan take ciki bazai iya bada ita ga Yan sandaba kokuma gidan marayu sbd tana cikin mawuyacin hali,
Haka Kuma mahaifiyarsa a yanda ya santa mace ce Mai tsananin kishin ‘yayanta Musamman shi ta tsani wani ya rabesa Dan haka yasan bazata taba yarda da abar babynba hannunsu harta danyi wayo tukuna akaita gidan marayun
Idanma baa ga uwar babynba kenan Dan zuciyarsa takasa yarda da uwa Zata iya jefar da ‘danta ta gudu duk tsananun rayuwa kuwa..
Washe gari tun kafin kowa ya tashi daga masallaci sallar asuba ya fice zuwa asibiti da mota Yana Jin rashin nutsuwa matuqar ba zuwa yayi yasan halinda babyn ke cikiba.
Banyi baccin nutsuwaba sbd Jin yake babyn mutuwa zatayi a halinda dai yabarta.
Tunaninsa gabaki daya ya karkata akan uwarta ta gudu ne tabar ‘yar sbd rashin lafiyar babyn da bazata iya daukaba wannda hakan zallar rashin imani da tausayine.
Koda ya Isa asibitin babyn ba laifi tarta fara daidaituwa sbd Madara da aka kwana ana bata duk Bayan mintuna sbd yunwace da tsananin wahala da sanyi suka Kama babyn sosai.
Fes aka shiryata cikin kayan sanyi masu tsananin taushi farare tas daya siya tun jiya a asibitin aka shiryata.
Har Inda babyn take aka Isa dashi tareda kallonsa likita yace”
Ina uwar babyn take ne?
Tayi sakaci da ganganci sosai akan wannan babyn gskia.
Wani irin sanyi yaji zuciyarsa tayi batareda ya dauke idonsa daga kan babynba dake bacci idanuwanta a rufe murya a sanyaye yace”
Batada uwa.
Dakatawa daga rubutu a file Dr yayi yana dagowa dukkaninsa ya kalli ABDULMAJEED din da mamaki yace”
Ka kuwa gane abinda na tambaya?
Mahaifiyarta nake nufi,
Wadda ta haifeta.
Wani daci yaji yakuma cika ransa ambatar sunan uwar babyn…
Yana kallonta tana kallonsa da ‘yarta a hannu tahau mashin ta gudu tabarsa da ‘ya jaririya Yana yawo tsakar dare nemanta.
Mezaice gameda wannan uwar?
Mezai fadawa kowa gameda uwa irin wannan aduk Inda ze Kai babyn yasan bazaa taba kaunarta ko kulawa da itaba Kamar uwarta Koda kuwa a halin talauci da qunci ne.
Numfashi ya sauke a boye tareda dagowa ya kalli likitan Kai tsaye yace”
Mahaifiyarta ta rasu.
Numfashi Dr ya sauke tareda tausayawa babyn
Saikuma ya dago ya kalli ABDULMAJEED din dakyau
Dan haihuwa Kam ya Isa ya Haihu tunda matashine Amma Kuma yanayin wayewa da hutun daya gani tattareda dashi yasan zaiyi wuya ace yayi saurin aure bare harda haihuwa
A qiyasa bazai wuce 300level hakaba zuwa 400 a karatun jami’a.
Duk tunanin dr iya lissafinsane kawai Dan haka kai tsaye yace”
But you are the Father right??
Yes” kawai yace Masa Dan bayason tambayar.
Sauran abubuwan da baayi bane jiyan aka qarasa yi qarshe dai bai baro asibitin ba sai qarfe goma Sha daya sbd babyn Kam Saida aka hada da Oxygen.
Daga asibiti report yaje yasaka na Neman uwar babyn Wanda yasan zaiyi wuya a sameta tunda tana sane ta gudu ba wai batane babyn tayiba.
Koda ya dawo gida hankalin hajiya umma yagama tashi hakama duk Inda ranta yake yagama Kai qololuwa gurin baci.
Musamman su Anty juwairiyyah dasuka Gama qara hawar da ita akan zancen ABDULMAJEED yafi daukan mutanen waje da mahimmanci akanta.
Hajiya umma wadda asalin sunanta yake AYSHATOUH mahaifiyace ga ABDULMAJEED da yayunsa Mata guda biyu.
Anty juwairiyyah itace Babba sai Anty safiyyah saikuma shi ABDULMAJEED daya kasance qarami Kuma auta.
Son da mahaifinsu da hajiya umma kewa ABDULMAJEED sosai ya zarta abinda Yan uwansa zasu iya dauka sbd bambamci ne afili.
Mahaifinsu justice Abdullahi Isah babban former justice ne a high Court dake Abuja,
Yayi retire tareda barin qasar yakoma South Africa tsawon shekaru kafin yadawo Nigeria sbd ABDULMAJEED dake shaawar karatu da rayuwarsa a Nigeria.
Dagowarsu da qanqanin lokaci akai auren juwairiyyah da wani babban barrister anan Abuja haihuwarta daya auren ya mutu tadawo gida itakuma anty safiyyah dama Bata samu mijinba aikinta kawai takeyi Dan itama aikin mahaifinsu tabi lawyer ce.
Anty juwairiyyah da Anty safiyyah tun ABDULMAJEED dasu suna qanana Allah ya sanya musu kishinsa Mai tsanani Wanda ta wani fannin yake surkuwa da baqin ciki sbd fifici da banbancin da iyayensu suke nuna musu sosai akansa Musamman hajiya umma.
Abbansu Yana iya kokarinsa gurin yimusu adalci da Basu iya tasu kulawa da kaunar Amma Kuma ko yayane baya iya boye fificin kaunar ABDULMAJEED.
Ita hajiya umma nata shine yafi tabasu sosai sbd Babu tunanin illar hakan take nuna nata fificin.
Sunkoma tamkar wasu ‘yayan riqo a hannun iyayensu sbd ABDULMAJEED Wanda hakan ya Gina rashin kauna tsakaninsu da ‘dan uwansu.
Bayan rasuwar abbansu Haj umma sosai ta sake qwallafa ranta akan majeed Bataji Bata ganin kowa sai shi,
Su Anty juwairiyyah dasuka fara nuna rashin Jin dadinsu a fili sai kawai ta tsana zamansu a gida kullum cikin musu fadan rashin fidda mijin aure takeyi sun fara tsufa a gida.
Wannan kalaman nata ya tsananta duk wata tsanar dasukaiwa Dan uwansu sunajin kamar shine duk wata matsakarsu da baqin cikinsu na rayuwa.
Haj umma tsananin kaunar datakewa ‘danta yasa ta kasance cikin irin iyayen dake tsananin kishin ‘yayansu
Kishi Mai tsanani,