GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Zama kowa yayi jiki a sanyaye Musamman Inayah da kusan komai Bata ganewa Takoma kaman wata mutum mutumi.

Ita Alhaji babbah yafara kalla cikeda tausayawa da kulawa kafin ya maida kallonsa kan umma yaganah datake Babba zatafin fahimtar komai Kuma idan ta fahimta komai zaifi tafiya daidai Dan itace Zata ringa dorata a hanya akan auren da haqqoqinsa tunda tare suke rayuwa gida daya.

Gaisawa suka fara Yi kafin ya Dora da fadar”

Haj yaganah ya fama da hidima da jama’a?
Allah yasa angama lafiya yakuma sanya Alkhairi.
To wani babban Al’amari yafaru tsakanin shekaran jiya zuwa jiya da Kuma yau din kafin daurin aure Wanda yasa aka samu sauyi cikin qurarren lokaci.,

Shi aure nufine na Allah Dan haka kada kuyi Wani mamaki da Al’amarin ubangiji,
Inayah dai kaman yanda a da MAJEED shine jigonta yanzuma shine jigonta Kuma ma’ishinta Dan kuwa shine mijinta haryanzu yafi kowa iko akanta.

Basai an tsaya tone toneba anan ko dogon bayani Wanda Zata samu daga baya idan ansamu komai ya lafa
MAJEED dai bashine mahaifinta ba Kuma yada alaqar Jini tako Ina da ita bamu kadaiba duniyama Bata taba sanin da hakanba sbd riqon Amana da Gaskia da yayi Mata da zuciya daya Kuma a wannan duniyar abune Mai wuya samun irinsa Dan kuwa ko ‘dan jininka baka riqewa ba Amana irin hakan Amma shi ya riqeta ya reneta da Amana da kauna bai taba barin tasan bashine mahaifinta ba idanba yanzu da hakan ta bullo ba Rana tsaka shima Kuma hakan da yayi yayine duk akanta sbd har gobe itace kulawarsa.

Shi Dr Abdul dai anfasa aurensane sbd uwarsa daya ubansa daya da Inayah Wanda shi wannan bayanin ba hurumin shigata bane
Dan hakan Ina fatan Kun fahimci yanayin da aka shiga dakuma wandama zaa Shiga Nan gaba sbd Koda Wasa karnaji anyi wata fitina kokuma tashin hankali akan wannan auren,
Shima MAJEED din danasan yafi kowa shiga mugun yanayi akan wannan auren nai Masa nasiha Kuma Inshallah Ina fatan ya dauka.

Dan hakan Haj yaganah sai anyi kokari gurin fahimtar dasu wasu abubuwan aure ya wuce mutum yayi Masa daukan dayaga dama,
Allah ya sanyawa auren albarka,

Suma can Allah yabasu ikon warware komai lafiya.

Waiwayowa yayi zaiwa Inayah nasiha akan itama saita dauki qaddara sbd da tashin hankali samun kanka irin wannan yanayin sai ganin sukai tana Jan numfashi alamar attack Zata samu
Kafin suyi wani yunqurin tasamu attack take Dan haka a rikice suka dauketa zuwa cikin gida.

Allah yasa akwai likita taredasu Neesah taredasu Amma bada ita akaje palon Alhaji babbah ba
itace tayi gaggawar fara taimakawa Inayah din wadda takejin kaman zata rasa ranta sbd yanda numfashinta ke Neman yankewa Neesah na taimaka Mata gurin janyosa da karfi.

Ganin kaman Al’amarin zaiyi girma sosai Dole suka Kira Dr farhat wadda kafin ta iso suka dunguma da Inayah din zuwa asibiti sbd tuni umma yaganah takira Abbi ya sanar Masa yace su wuce asibiti gashinan zuwa asibitin.

MAMUH

LOVE/ROMANCE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[10/31, 9:43 PM] +234 703 926 9802: 32
Arewabooks@Mamuhgee
Private hospital din dake anguwarsu Alhaji babbah aka kaita sbd kafin suce sunje AA specialist wato private hospital dinsu akwai nisa daganan da hakan suka tsaya tanan kusa.

Cikin gagawa suka karba Inayah din
Neesah ma bata barmusu aikinba su kadai da ita sukayi Dan sunada fahimta tana sanar dasu itama likitace suka barta ta taimaka musu tunda dama itace kusan tasaba taimakawa Inayah idan irin hakan ta taso.

Umma yaganah gabaki daya kanta neman sake cakewa yakeyi da wannan Al’amuran daketa faruwa daga wannan sai wannan,

Har cikin ranta takejin kauna Mai tsafta da tsanani akan MAJEED da Inayah sbd sune danginta itace danginsu Dan lokuta da dama sukan mantama basuda alaqar jini da juna.

Badan a yanda yanayin komai ya fallasa kansa ba lokaci daya ba zato ba tsammani da Babu Wanda zai kaita murnar Auren MAJEED datake addua da fatar gani tsawon shekaru.

Hakama auren Inayah wani babban burinta ne shima datake fatan Allah ya nuna Mata ya cika a yau din
sai gashi Allah yacika Mata burin Auren dukansu a yanayinda Babu wanda yataba tsammata,

Ku kansu basuma San farin ciki zasuyiba ko damuwar sanin ba Abbi ne ya haifi Inayah ba.

Anty Hafsat ma zuciyarta kusan Kashi Kashi take kasuwa tana rarraba Mata tunani sbd ayanzu Bayan Jin bayanin yanda Al’amarin yake daga bakin Alhaji babbah taji zuciyarta na farin ciki da auren Dan kuwa Inayah Allah yayimata kyakkyawan sauyin dayafi duka tarin mazan data rasa abaya sbd Abbinta yakai kowanne level da ake kwadayin namiji yakai badan tashin hankalin halinda Inayah tashigaba da a fili Zata fara bayyanarda farin cikinta akan wannan tsintar damu akala da Inayarsu tayi Dan kuwa Abbi kam Masha Allah.

Sbd wadda tasaba ji da matsalarta na kusa yasa ma’aikatan asibitin Basu Sha wuyar taro yanayinta ba tadawo hayyacinta saidai take bacci ya dauketa sbd kusan wannan attack din yafi wainda tasaba samu abaya.

Kwantawa hankalinsu yayi ganin tadawo daidai tasamu bacci Amma kallo daya zakawa fuskarta ka gano baccin na tattareda yanayin firgici data shiga.

Suna zaune a dakin datake anty Hafsat na kokarin daidaita ACn dakin da yayi yawa umma yaganah Kuma na zaune tana kokarin amsa wayarta da Mimi ke Kira saigashi ya iso yashiga dakin cikin nutsuwa sanyeda Lululemon wears har lokacin da alama Bai tsaya sauyawaba zuwa wasu manyan kayan.

Fresh skin dinsa daya bayyana sosai cikin kayan anty Hafsat da Neesah suka kalla suna sake tabbatarda kyau da tsarin da Allah yayiwa Abbin
Take suka sake Jin tabbas ta wannan fannin Inayah Dinsu tagama dacen miji illa kawai baqin cikin dazata Shiga sanin Abbinta datafi so fiyeda komai baida alaqan Jini da ita
Tsintar yayi,kyautarta akai Masa kokuma tayaya ya sameta Allah ne kawai yasani saishi da umman Abdul din.

Cikin girmamawa anty Hafsat da Neesah sukai Masa sannu da isowa

Da qaramin sauti ya amsa Yana dan kallon Inayar kafin ya kalli anty Hafsat sbd umma yaganah na waya yace”

Doctors din sungama dubata ne?

Neesah ya nisan yanayin nata?

Firgici ne kawai data shiga ya daketa sosai Amma Inshallah lafiyanta kalau yanzu anmata allura ne sbd tayi baccinda kanta zai Dan warware ya rage Mata tashin hankalin.

Gyada Kai yayi ahankali tareda sake kallon Inayah datai wani iri cikin lokaci qanqani.

Dan gajeran numfashi ya sauke tareda juyawa yafita zuwa ganin likita Dan bayason ta kwana a asibitin gida zasu koma tunda suna tareda qwararrun likitoci a gidan.

Fitarsa da mintuna biyar sai gasu Mimi sun iso asibitin a gigice sbd tashin hankali biyu,
Na farko Jin auren MAJEED da Inayah dakuma Jin uwarsu daya ubansu daya itada Dr Abdul ga qarin halinda Inayar tashiga.

Jigum jigum sukai a dakin wasunsu na sake Dan jajanta wannan alamari da masu godewa Allah da baa Riga an daura aurenta da Dr Abdul dinba dan da abin yafi lalacewa.

Umma dai bayan taga Inayah ta tashi babu abinda take fata Dan ita kanta yanzu tanajin dacin da Inayah Zata Shiga,.

A sanin dataiwa Inayah kuka da baqin cikin dazata Shiga na zaman Abbi ba mahaifintaba zaifi Mata ciwo da radadi fiyeda auren Dan kuwa tafi buqatan ace alaqar jini suka hada Bata auratayyaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button