INAYAH 31-40

Har yamma lis suna asibitin Inayah Bata farkaba sai magriba.
Tana farkawa takasa kallon kowa a dakin sbd yanda duk sukai jigum jigum yabata tabbacin abinda yafaru kafin zuwanta asibitin Gaskia ne haqiqanin Gaskia Kuma Dan haka Batasan ta Ina Zata fara bayyanarda babban abinda takeji tokare da zuciyarta da maqoshinta.
Cikin kulawa da sanyin jikin yanayin da Inayah din ta nuna umma yaganah da Anty Hafsat suka fara kokarin magana saiga shigowar Abbi Wanda Yana shigowa qamshinsa ya gauraya dakin suka tsit suna jiran abinda zai faru Kuma ga Inayah din ga Abbi a amatsayin ma’aurata.
Yanayinsu yasashi basarwa tareda Dan kamewa ya kalli Inayah data dago ta zuba Masa Ido tana Neman fashewa da kuka yace”
Kina farkawa Kuma Zaki fara wani kuka agurin.
Neesah dake gefenta ya Dan kalla yace”
Ku shirya gida zaa koma da ita yanzu.
To” Neesah tace tana kallon Inayah din dake kokarin fashewa da kuka Amma takasa sbd abun datakeji ya girma qwaqwalwarta.
Juyawa yayi ya fice suka biyo bayansa.
Anty Hafsat motar CM zatabi itada Mimi da Safnah
Su Kuma su Inayah din motar Abbi zasubi Dan haka suka nufa motar Kai tsaye umma yaganah na riqe da hannun Inayah dake kokarin zubewa sbd tangadin datake na Bata cikin cikakkiyar nutsuwarta.
Kaman yanda suka Saba fitarsu da Abbin idan takama Inayah ce a gaba Dan haka yau dinma itace agaba sai umma da Neesah a baya.
Bayan sanyin Ac na motar da qamshinsa daya cika motar Yana zagayawa Babu Mai ko motsi acikinsu kaman ba kowa a motar kowa da tunanin daya shiga Banda Inayah da har lokacin qwaqwalwarta Bata fara aiki daidai ba dif take Bata ji Bata gane komai yanzu.
Suna Isa gida Dole Neesah ce ta kamota suka nufi ciki tana kokarin kaita bedroom dinta ta qwace Takoma Palo tana kokarin bin bayan Abbi cikin dimauta tana cewa”
Abbi ne kawai zaifadamun Gaskia na yarda da abinda duk ake fada,
Abbina ne kawai zan yarda da maganarsa.
Da sauri umma yaganah ta riqota tana cewa”
Ki nutsu Mana Inayah,
Me zakije kice Masa yanzu?
Bakiji anfada Miki yanzu mijinki bane,
Qarya zamu taru mu Miki ne?
Alhaji babbah zai Miki qaryane?
MAJEED din dakikeson saiya fada Miki komai Yana cikin damuwa sosai bakya gani?
Zaki sake daga Masa hankali da kukan Nan nakine idan kikace rikicewa zakiyi.
Rikitaccen Kuka ta fashe dashi Mai tsananin qunci tana cewa”
Ni bazan yardaba wlh abbin ne mahaifina,
Banason kowa a mahaifi sai Abbi,
Har umman Abdul din banaso amatsayin uwa Ni Abbi ne kawai uwa Kuma ubana…
Da sauri umma ta rufe Mata Baki jikinta na rawa sbd jikinta daya fara sanyi itama da irin kukan da Inayah din fasawa Wanda tunda take Bata taba yin irinsaba sai yau.
Rirriqeta sukai ta zube qasa tana sake tsananta kukanta zuciyarta na Mata wani irin zafi da radadi…
Idan ba abbine mahaifinta ba ai ita asaran duniya da baqin cikin duniya tana cikin cikinsa da wannan mummunan labarin da gwara ayita fasa aurenta har abada akan wannan labari…
Bazata taba yarda da maganar kowaba sai taji daga Abbinta cewa gaske bashine ya haifetaba.
Dukkanin sautin kukan datake yanajinsu Amma Bai iya zuwa Inda suke dinba Dan kusan yafita baqin ciki da wannan bankadar,
Dan yaso ya tsaya a ubanta na har abada saidai qaddara Bata bar hakan ba Dan kuwa Koda warware auren Nan akayi har abada ita zaa Kira da matarsa ta farko wadda tafara daukan igiyoyin aurensa haka itama har abada shi zaa Kira da mijinta na farko daya fara riqe martabar aurenta.
Kuka Inayah da tashin hankali sosai tashiga lokaci daya Wanda ya gigita umma yaganah da Neesah harma dasu zubbi da Salimat sun Shiga tashin hankali da damuwa sosai ganin halinda Inayah din ke ciki
Ta bangare daya shi kansa Mai gidan babu Wanda yakuma ganinsa har washe gari,
Abincin gidan ranar haka aka daukesa aka fitarwa Bosco ya rarrabawa securities din anguwar abokanansa sbd Babu Mai nutsuwar cin wani abinci.
Da zazzabi Mai zafi Inayah ta kwana Dan kaman yarinya qarama Takoma musu daqyar baccin wahala ya daukeda jikinta da mugun zazzabi.
MAMUH#
LOVE/ROMANCE
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
0913484810733
Arewabook@Mamuhgee
Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta kwanta sbd tsananin ciwon Kai Dana kirji,
Ana Gama breakfast umma yaganah ta sallami baqinta aka kaisu aka sanya mota tareda Dan abin arziki gidan yasake daukan tsit.
Su zubbi tuni suka shirya komai a dining na breakfast kaman yanda suka Saba.
Umma dai a dakinta tayi breakfast din Neesah ma bata fito dining ba Dan a daki Tasha tea Danma sunyi sunyi Inayah ko tea din Tasha taqi.
Har lokacin bata daina tsiyayar hawayeba,
Takasa yarda da wannan qaddarar lokaci daya wai ace Abbinta shine mijinta,
Tayaya Zata fara fuskantar wannan maganar,
Har abada bazata taba iya karban Abbi amatsayin mijintaba sbd haramun nema agunta kallon Abbi a matsayin Miji ba uba ba.
Daga Neesah har umma sunyi rarrashi da nasihun harsun gaji Amma Babu sassauci a lamarin,
Gabaki daya fuskarta ta sauya sbd kuka.
Anty Hafsat ma tazo tayi nata rarrashin Amma Dole haka zasu hakura sbd dama bazai yiyu ka karbi irin wannan ba lokaci daya.
Gabaki daya wunin basuga Abbi ba sbd yafita tun safe gurin sallamar baqinsu na nesa dazasu wuce Kuma akwai wainda zaiyi meeting dasu kafin su wuce din.
Da farko mantawa yayi da auren daya rataya akansa jiyan sai daga baya bayanma ya daga waya zai Kira Inayah.
Dan rinte Ido yayi tareda maida wayar ya ajiye Yana fitarda Dan numfashi Mai zafi.
Miqewa yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan Yana gogawa fatarsa sabulun mountain water soap na Creed.
Sai bayan wasu Yan mintuna yafito daureda blue towel a qugu yafara shiryawa.
Cikin dark blue kaftans yafito da blue hular kube Bai wani shiga can palonsu ya fice daga gidan sbd jiransa da ake.
Sai Bayan azahar Inayah ta iya tashi da daqyar takai kanta toilet tayi wanka.
Sallah tayi tazauna tareda janyo wayarta tana sake saka kiran Heart dinta Wanda yanzu Kuma hankalinta ya karkatane akan taji yanda yake sbd tasan Yana cikin matsanancin halin shima.
Wayarsa har lokacin bata Shiga Dan haka tasake daga hankalinta da wata qarin damuwar.
Dole anty Hafsat da Neesah da umma yaganah sukai Shirin tafiya dubosa asibiti Dan dama suma duk sun damu dason sanin halinda yake ciki din tun iya basuda labarin komai akansa da mahaifiyarsa Kuma mahaifiyar Inayah.
Abbi umma yaganah takira ta sanar Masa zasu tafi dubo Abdul din Bai hanasuba yace suje.
Har Zata kashe Kai tsaye a nutse cikin kamewa yace”
Kar kuje da Inayah ta zauna gida.
Ok shikenan.
Inayah taji lokacinda Abbi yace kada aje da ita Dan haka hankalinta yaqara tashi da sauri tadauki wayarta tareda saka kiransa.
Ringing wayar tafara
Lokacin Yana tareda dasu CM da wasu school mates Dinsu da duk sunzo daurin auren sbd kowa nata kokarin hulda dasu shida CM yanzu sbd ganin sun Zama abokan manya sbd kudi.
Dan waiwayawa yayi gefensa da wayar ke ajiye ya kalli wayar a natse yaga Inayah ce me Kiran yakuma San Sarai roqonsa zatai akan binsu shikuma bazai taba barin ta hadu da Hadiza ba ayanzu Dan haka ya dauki wayar a kame yace”