GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Abbin ne yarigasu isowa gida Kuma yasan Babu kowa a gidan sai Inayah Dan haka daya dawo direct ta palonsu ya biyo tareda nufar bedroom dinta.

Yana isowa zubbi na fitowa daga dakin daukeda tray din abinci da Inayah din bataci ba.

Zubbi na ganinsa tayi saurin Dan yi gefe Tana cewa”

Welcome Sir.

Tray din hannunta ya kalla ganin Babu abinda aka taba daga abincin.

Dan rintse Ido yayi ya bude tareda cewa a natse,

“Kiyi warming abincin ki dawo Mata dashi.

Ok Sir” tafada tareda barin gurin.

Dayake kofar abude take Koda suke maganar Dan haka Inayah taji Qamshin turensa tasan abbi na kusa sai gashi taji muryarsa a hankali.

Da sallama Mara sauti sosai yashigo dakin Yana kallon yanda take zaune kan gado daga fuskarta har idanuwanta sunyi mugun kumbura gabaki dayama kusan kamanninta sun sauya sbd kuka da tsananin tashin hankali.

Sofa dake dakin ya nufa ya zauna ahankali tareda Dan takaita kallonsa akanta sbd ganin fuskarta ahakan damunsa zaiyi sbd baitaba barinta tun yarintaba tashiga damuwa irin haka.

Yana zaunawa ta miqe tsaye ta nufosa.

Wani kallo yayiwa qafafuwanta dasukai haske sosai ga sai zanen maroon lallen da akai Mata na aure yafito da Babu safa ko bedroom feetwear a qafafun tana kallon ta dakata tareda komawa baya ta dauki feetwear dake gefen gadon masu taushi na bargo ta saka kafin ta nufosa Dan yawo ba feetwear ko safa wani abune da abbinta koyar da ita tun qanqanuwarta
Duk tsafta da kyan gidansu basa da yanda tsarin gidansu yake na komai fes Bata tafiya ba takarmin ko safa a qafarta sbd wasu qananun qwayoyin cuta ta qafa suke saurin shigar mutum.

Gefensa ta qaraso jiki a sanyaye ta zauna tana kokarin yimasa wani kukan Dan dama tun jiya takeson ganinsa tayi Masa kukan dake cinta Amma taqi barin kowa ya gansa ya shigewarsa.

Fara hawaye tayi tana kallonsa tace”

Abbi Dan Allah kada kacemun bakaine mahaifinaba,
Ni Kai nasani Kuma Kai zanci gaba da sani a wannan matsayin
Bazan taba karban kowaba amatsayin uwa ko uba
Dan Allah Abbi kabarni da matsayina na ‘yarka ta Jini nafison.

Umma yaganah ce ta bude kofar dakin tashigo Kai tsaye sbd dawowarsu kenan.

INAYAH Bata tsaya da abinda take fadaba tacigaba da cewa”

Abbi Dan Allah kada karka bari a sauya mini wani sunan bayan Wanda ka sanyamin,
Ni banason kowa amatsayin jinina sai Kai,
Abbi Ni Kai kadai ne jinina,
Danasan yanda zanyi na hada Jinina da naka ya gauraya daya da naka Abbi wlh danayi ayau dinnan…….

Umma yaganah dake kokarin juyawa tabasu guri Batasan lokacinda ta tsaya cak ba tareda dawowa da wuri tana buge bakin Inayah din cikin kunyar zancenta.

Shi kansa MAJEED din Dan muskutawa yayi tareda fuskewa sbd Inayah dai idan zatai zance ba ruwanta yanko abarta kawai takeyi.

Lokuta da dama Dan umma yaganah na kwabarta ne Amma zantukan datake yankowa gaban Abbin mamaki suke basa matuqa Dan shi wasu abubuwan na halayen Mata dabai taba saniba sbd Bai mu’amalantu dasuba sosai a gurin Inayah yake ji da saninsu.

Ahankali ya kalleta Bayan ya kalli umma yaganah da bakin Inayah yake Bata takaici wasu lokutan.

A natse cikin yace”

Inayah wannan wata Gaskia ce da Dole zamu hakura na dauka sbd nafiki Jin dacin rashin Zama Wanda ya haifeki Amma hakan Allah ya qaddara.

Wannan kukan kidaina Babu Wanda zai tafi dake koina,
Dr Abdul Kuma idan kin daina kuka kin nutsu zan Bari kije ki dubasa.

Gangaro Mata hawaye sukai tace”

Abbi maganar auren fa?
Da gaske an daura mun aure da……

Sake buge bakinta umma yaganah tayi cikin wani sabon takaicin tace”

Waiki bakinki baya shiru idan bakisan me Zaki fada bane?

Qarya zamu Miki baa shine mijinki ba?

Baice komaiba ya miqe ya fice Yana cewa”

Wannan kukan idan Baki dainaba ko gate bazaki sake fitaba bare zuwa duba Dr Abdul.

Yana fita anty Hafsat da Zata wuce tashigo dakin tana kallonsu,
umma ta zauna gefen Inayah cikin takaici tace”

Ke bakinki baya haila ko?
Kullum Ina kwabar bakin Amma kin kasa iya kamesa ko?
Da kike maganar dakinsan yanda Zaki hada Jini dashi da kin hada ayau
Saurin uban me kikeyi idan a gauraya Jini kikeso ai zaa zo gurin saikiyi bayani da kanki,
Kullum kwabarki nakeyi bakyaji
Yanzu dai mijinki ne idan zakiyi hankali kiyi Dan kuwa bakin Nan naki kaiki zaiyi yabaro tun baayi nisaba ki gane barno gabas take.

Murmushi Anty Hafsat tayi sbd ko baa fadaba tagano kan zancen ta kalli Inayah datai tsit idonta yake hawayen fadan ummsn cikin kulawa tace,

“Yi shiru Inayah
Amma ki koya fadan magana bako wace iriba agaban Abbi yanzu sbd yanzu mijinki ne wata maganar idan kinyi kina tadowa kanki aikine tunda wuri wuri Wanda bazaki iya daukaba.

Kinga shikansa yanzu bai Gama karban yanayin ba Dan haka ki ringa Kama bakinki kisan me zakina fada.

Karma ta Kama taci gaba ita Zata bada labari Ina zaune Ina kallo
Badai gaurayan Jini kikesoba
Zaa gauraya Inda rai kuwa.

Umma Dan Allah ayi Mata hakuri da kyakkyawar manufa ta fada sbd yanayin data samu kanta da Wanda ta dauka mahaifinta ne,
Ita kanta Batasan wata manufar abinda tafada tabadaba.

Duk da hakan Inayah nada buqatan sanin abubuwa da dama na sanin Kai tunda yanzu aure yahau kanta Dan haka Hafsat ke wannan aikin ya sama saiki bada himma gurin ganar da ita.

Da farin ciki anty Hafsat tace”

Umma ai wannan aikin Dole ma kuwa
Musamman angon na Inayah shakkarsa duka muke muma dake yanne Kuma iyaye
Amma ahakan zakisha kallon hudubar da zanwa mutuniyar tawa.

Allah yasa ta dauka idan ba zuwa zatai tana fada Masa abubuwan da kike koya mataba
Wlh databarki da kunyar duniya”

Umma yaganah ta fada tana dariyar abinda zai biyo baya kuwa idan hakan ta kasance.

Dariya anty Hafsat tayi tana cewa”

Dakuwa mun Bata da ita idan tamun wannan gangancin
Yanzu mijine bakomai Zata fada masaba sabanin adah dayake matsayin uba.

Ganin Zata shiririce yasata miqewa Tai musu Saida safe ta wuce sbd anzo daukanta.

Bayan fitar anty Hafsat umma ma miqewa Tay ta wuce dakinta
INAYAH tabi kofar dasuka fice da kallo tanajin sun datse Mata maganarta da Abbi batareda sun gamaba.

Miqawa tayi ta nufi toilet tashige sbd alwalar sallar magrib da ake Kira.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/2, 10:00 AM] It’s Queen Meenali????: 35
Arewabooks@Mamuhgee

‘YAR ZURU Maman ZEE ZEE Best kayan mata

Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta shahara wurin hada kaya kamar haka ❤️kamar su
Kaza
Zabo
Zakara
Ciccibi
Zuciya
Tsimin kankana d rake
Tsimin tabaje
Zumar dabino d kwakwa
Zumar gorun tula syrup
Garuka masu kama jiki kamar su ❤️
Bita zai zai
Dan wata bakwai
Madarar mata
Bata????????????
Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki
Matsin kinfi budurwa
Kalolin gumba dsauransu
Address maberar jariri bayan FGC sokoto
Phone 08068526455
Instagram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata.
Karku Bari kuwuce Baku gwada kayan Maman zee zee best kayan Mata ba..

35
Arewabooks@Mamuhgee
Da daddare tun 7:30 sukaci abincin dare Amma banda Inayah dataqi fitowa shima Kuma abbin tambaya daya yayi umma tace Inayan ba yanzu tace zataciba
Baikuma maganaba yagama cin abincinsa ya fice yabar umma da Neesah a table suna sake jinjina taurin Kai irin na Inayah sbd son zuwa ganin Abdul Zata dagawa kowa hankali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button