INAYAH 31-40

Cikin damuwa da takaici umma yaganah tace”
Babban damuwata akan Inayah
Ga abinda yakamata ta fuskanta wato Wanda aurensa ya rataya akanta Amma Sam ita ko yarda da zancen taqiyi bare bawa zancen mahimmanci hauka kawai ta dauka munayi tunda abokan wasantane mu,
Idan Ni ta rainani ai Alhaji babbah da Abbin nata bazasuyi Mata wasaba ko shirme irin nata datake tunani.
Neesah ajiyar zuciya ta sauke tana ajiye spoon din hannunta tareda Shiga tunani tana kwatanta irin rayuwar da Aminiyarta Zata zuba a cikin gidansu Kuma gidan aurenta da Wanda Koda qazantar mafarki Bata taba mafarkin aurensaba,
To Amma yanxu da hakan ta kasance tayaya zata karba auren harsu samu cika burikan dasuka dauka zasuyi da mazajensu idan dukkaninsu sukai aure.,
Babban qarin abin shiga tunanin shine abbin da kusan baiwani San mataba,
bama kusan ba
Baisaniba kwata kwata tunda bashine ya Haifa Inayah ba to tabbas kenan
“he’s virgin” tafada a bayyane tana zare Ido cikin Murna Mai tsanani sbd burin Inayah kenan auren wanda Bai taba sanin kowace maceba sai akanta,,,
“”ohh my God, Abbi is still a virgin????
Tafada da Dan farin ciki tana kokarin miqewa zuwa gurin qawarta suka hada Ido da umma yaganah dake sake Baki duka tana kallonta cikeda tsoro da mamakin yanda yaran Nan suka Gama lalacewa basuda masaniya akai.
Wata irin kunya ce takama Neesah tana ganin irin kallon da umma ke Mata tasan itama ta sake layi Dan daga ita har Inayah din bakin nasu wani lokacin ba burki bare ribas.
Dan fuskewa take kokarin Yi ta hanyar komawa ta zauna Dan qarasa cin abincin da Zata Bari sbd zumudi
Umma a kasalance da mamaki tace”
Aa karki koma ki zauna jeki Inda kikai niyar zuwa Dan yanzu Kam na Gama tabbatarda kunfi qarfina yaran Nan Musamman Inayah,.
Yanzu ko kunyar Allah bakwaji zakije kuyi maganar MAJEED Bai taba sanin ma….
Kasa qarasawa tayi tana girgiza Kai cikeda kunya da takaicin fada da bakinta.
Kallon yanda Neesah tayi tsamo tsamo tayi tace”
Jeki kuyi abinda zakuyi din,
Nagamo da ita tana maganar gauraya Jini kekuma gakinan yanzu kema kina Taki maganar banzar,
Allah ya shiryaku ya sakamu kunya irin ta ‘yaya Mata Dan kuwa Naga sai mun dage da adduar kunyi nisa,
Ita ansamu tun batai tsamari ba an aurar Saura ke
Kema Kuma hankali na kwantawa zanfadawa Fatima suyi Miki aure.
Kaman munafukar Neesah tabar gurin a ranta tana cewa”
Allah yasa umma yaganah kinawa momy magana ko wata kada na qara Amin auren ai inaso.
Da mamaki umma tasake bin Neesah da kallo jin ta amsa adduarta ta qarshe da cewa”
Amin” a bayyane.
Neesah Kai tsaye dakin Neesah ta Isa tana murmushi da dauke gira daya ta qarasa kan gadon da Inayah din ke kwance tana waya da Abdulsamad wadda sai alokacin suka samu Jin juna tunda wannan abun yafaru.
Tunda ya Kira wayar ta dauka take rero Masa wani irin kuka ahankali tanajin kaman ta bude Masa zuciyarta yaga matsayin sonsa aciki.
Kukanta kawai yake saurara Yana zubda hawaye shima sbd bazai iya magana ba shima,
Daga zuciyarsa har kirjinsa da kansa zafi suke Masa,
Yakasa yarda ko karban Inayah amatsayin ‘yar uwa,
Bazai iyaba,
Bazai iya daukaba,
Hakama zuciyarsa bazata iya daukaba bare kwakwalwarsa data gama yamutsewa akan son Inayah tuni.
Ganin halinda suke cikine yasa jikin Neesah sanyi ta kalli Inayah dake kuka sosai har hancinta Saida yayi jajir Bayan idanuwanta da fuskar gabaki daya.
Karbe wayar Neesah tayi tareda dorawa akan kunnenta cikin tausasa murya dakuma damuwa tace”
Dr wannan kaman kuna neman butulcewa qaddarar da Allah yake jarabtarku da itane,
Inayah matar wanice yanzu daga ita har Kai kunsan me ake nufi da hakan
Badan kana matsayin muharramintaba dasai nace wanna haramun ne kuke aikatawa mezaisa bazaku danganaba ku dauki hakan wani babban rabo daga ubangiji ku gode Masa da kuka kasancema Jini daya qarshen kauna,
Shi Abbi Yana baqin ciki da takaicin rashin zamtowarta jininsa kaikuma data zamo jininka kuna Neman batawa kowa da komai Dan wannan lalata komai zaku qarasa yi.
Kashe wayar tayi ta dungurar Mata gefe tareda kallonta cikin fara Dan siqewa da yawan kukanta akan soyayyar Dr Abdul tace”
Inayah can you stop all this stupidity,
Yanzu ke kunya bakyaji ki zabi wani kinata kuka akan wani duk kin kasa tsayawama ki duba babban abinda ya rataya akanki.
Tsoki tayi tareda juyawa tabar gurin ta fada toilet Dan yin wanka sbd ita duk sun fara Bata haushi.
Rayuwa saukine da ita,
Ansan ba abune Mai saukin karbaba wannan yanayin dayazo Amma Kuma ba abinda zaka daga hankalinka bane sbd abbin dai dayafi Mata komai da kowa yasake zamowa nata dukkaninsa ba maganar kukan rabuwa dashi Amma haukan soyayyar wani na Neman rufe Mata Ido waninma ‘dan uwanta da aka tabbatar Mata da Babu aure tsakaninsu.
Inayah dake hawaye komawa tayi ta kwanta kawai batareda ta iya magana ba sbd bazata iya cire soyayyar Dr Abdul arantaba lokaci dayaba,
Tafi tausayinta sosai akan kanta na wannan yanayin dasuka samu kansu sbd sanin yanda yagama zurfafa da haukacewa a Sonta.
Aurenta Kuma da Abbi Bata Gama yarda dashi bane sbd tasan abbin ma bazai taba karban aurenba sbd Babu yanda zaayi suyi rayuwa ko zaman aure Dan tamkar haramunce garesu.
Ita maganar uwarta da akeyi Kuma batajin Zata taba iya daukanta a wani matsayin Bayan na mahaifiyar Abdulsamad kawai
Sbd aduk matsayinda Abbi zai dauketa hakan itama Zata dauketa Mai kyau ko sabaninsa sbd har abada Abbinta shine komai nata Kuma maganarsa zataci gaba Dabi har qarshen rayuwarta.
Koda Neesah tafito har lokacin Inayah din takasa daina hawaye sbd yanzu kukan rashin sanin kanta takeyi.
Shin marainiyace ita kokuwa ‘yar gaba da fatihan dagaske¿
Yarasa tayaya uwarta Zata jefar da ita kokuma guduwa tabarta kokuma kaita gidan marayu tun jarinta,
Tayaya ta fada hannun Abbinta,
Wace irin tsana uwarta Tai Mata da Zata jefar da ita tana jaririya
ta dauki Abdul daya girmeta Amma ita ta jefar da ita.
Ganin kukan datakeyi yayi yawa Kuma akwai tsananin damuwar abin da quncinsa a bayyane da Inayahn yasa Neesah tahowa ta zauna gefen Inayah din tareda Dan rungumota batareda tace komaiba Dan kada ta katse Mata damuwar datakeson ragewa ta hanyar kukan da tunanin.
Sun jima a hakan kafin Inayah ta janye jikinta tareda zamewa ta kwanta kan gadon tana rufe idanuwanta.
Shiryawa Neesah tayi itama cikin kayan bacci masu gajeran wando tazo ta kwanta gefen Inayah sbd tana period bare tayi sallar ishai.
Tanajin yanda jikin Inayah yayi zafi sosai alaman yauma da zazzabin atareda ita Dan haka ta miqe tadauko Mata magani tabata Tasha suka kwanta tanajin jikinta duk yakuma sanyi.
Washe gari ma Bata fito breakfast shima Abbin Bai fitoba su kadai sukayi daga umma yaganah sai Neesah.
Bayan sun Gama umma yaganah da kanta takai breakfast din abbin palonsa ta jiye ta fito.
Neesah Kuma tayi Shirin na Inayah takai Mata daki itama.
Zazzabinta ya tsananta Dan haka hankalinsu ya tashi Amma dai duk da hakan umma Bata sanarwa Abbin ba sbd kada damuwar suyi yawa Dan haka suka samu suka Dan lallabata Neesah Tai Mata allura bayan awa biyu jikin nata ya Dan saki tasamu qwarinsa tasamu tayi wanka tayi sallar azahar.
Tana idarwa ta zare kayan sallar ta miqe ahankali ta zura slippers ta fito dakin sbd tasan Abbinta baisan batada lafiyaba tunda Bai nemetaba Dan haka Kai tsaye tana fitowa Bata nufi koinaba sai hanyar palonsa jikinta ba qwari tafiyarma ahankali takeyi.